RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (06)
FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (01) .
Fitinar Sururiyyah tana da fikirori da suke karfafar wa'yancan ginshikai da ambaton su ya gabata, wa'yannan fikirori kuma sun hada da:
(¡) Wuce iyaka a kan batun hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar, kamar dai yadda Khawarijawa suka kasance, dama idan mai karatu bai mance ba mun ambata a baya cewa 'yan Ikhwan khawarijawa ne, Lallai 'yan Ikhwan sune wa'yanda suka jaddada Mazhabar Khawarij a wannan zamanin, dari bisa dari, kuma a wajen su suna ganin cewa lallai hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar kafirci ne babba kai tsaye, babu rarrabewa a kan wanda yayi wannan hukunci, sabanin tafarkin ma'abota Sunnah wanda asali shine yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar babban zunubi ne ba kafirci kai tsaye ba, kamar yadda Ibnu 'Abdi Al- Barr ya hakaito ijma'i a kan haka, sannan kuma tafarkin Salafawan gaskiya (ma'abota Sunnah) tafarki ne wanda yake lura da ababen da suke hana kafirtawa da sharuddan kafirtawa din a hade, bal a wajen ma'abota Sunnah yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar a matakin farko suna daukar sa a matsayin babban laifi ne, kamar yadda Sahabi 'Abdullāhi bin 'Abbās -Allah ya kara yarda a gare sa- yake tabbatar da hakan .
Sahābi 'Abdullāhi bin 'Abbās -Allah ya kara yarda a gare shi- a ruwayar Tāwus a karkashin fadin Allah ta'āla:
((ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكـٰفرون)) [المائدة: ٤٤]
Ma'ana:
((Kuma wa'yanda basu yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba wa'yannan sune kafirai)) [Al- Ma'idah: 44].
Yake cewa a kan ma'anar kafirci a wannan ayar :
"ليس بالكفر الذي تذهبون إليه!".
"ba fa kafircin da kuke fahimta bane!.
A wata ruwayar kuma yake cewa:
"إنه ليس بالكفر الذي يذهبون إليه، إنه ليس كفرا ينقل عن الملة، كفر دون كفر".
"Lallai ba kafircin da suke fahimta bane, ba kafirci bane wanda yake fitarwa daga musulunci, kafirci ne wanda bai kai kafirci ba" ma'ana karamin kafirci ne.
Kuma 'Aliyu bin Abi Talhah ya ruwaito daga Ibnu 'Abbās har wa yau a karkashin tafsirin fadin Allah ta'āla:
((ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكـٰفرون)) [المائدة: ٤٤] .

Yana mai fayyacewa game da wannan kadiyyar yace :
" من جحد ما أنزل الله فقد كفر، ومن أقرّ به ولم يحكم به فهو ظالم فاسق" .
Ma'ana :
"Wanda yayi jayayya da abin da Allah ya saukar hakika ya kafirta, amma wanda ya yarda da abin da Allah ya saukar amma bai hukunci dashi ba shi azzalumi ne fasiki ne" .
Daga cikin Malamai 'yan mazan jiya wa'yanda suka bayyana cewa wannan fassara ta tabbata daga Ibnu 'Abbās -Allah ya kara yarda a gare shi su kuma Allah ya jikan su- akwai:
- Al- Hāfidh Ibnu Katheerin a cikin tafsirin sa (2/64) yake cewa: atharin ingantacce ne bisa sharadin Bukhāri da Muslim.
- Ibnu Jareer Al- Tabariy a cikin tafsirin sa (6/166)
- Ibnu Battah a cikin Al- Ibānah (2/723)
- Al- Imām Al- Baghawiy a tafsirin sa (3/61)
- Al- Imām Al- Qurtubiy a tafsirin sa (6/190)
- Shaikhul Islāmi ibnu Taimiyyah, kamar yadda yazo a cikin Majmu'atu Al- Fatāwa (7/312)
- Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albāniy daga bayan su a cikin Al- Saheehah (6/109)
- Al- Imām ibnu 'Uthaymeen -Allah ya jikan shi- yana cewa kamar yadda yake a cikin "التحذير من فتنة التكفير" shafi na sittin da takwas (68) :
"لكن لما كان هذا الأثر لا يرضي هؤلاء المفتونين بالتكفير؛ صاروا يقولون: هذا الأثر غير مقبول! ولا يصح عن ابن عباس!! فيقال لهم: كيف لا يصحّ، وقد تلقاه من هو أكبر منكم، وأفضل، وأعلم بالحديث؟! وتقولون لا نقبل.. فيكفينا أن علماء جهابذة؛ كشيخ الإسلام ابن تيمية، وابن القيم -وغيرهما- كلهم تلقوه بالقبول ويتكلمون به، وينقلونه؛ فالأثر صحيح".
Yake cewa:
Sai dai da ya kasance wannan atharin baya yardar da wa'yancan wa'yanda suka fitinu da kafirtawa; sai suka koma suna cewa: wannan atharin ba karbabbe bane! kuma bai inganta daga Ibnu 'Abbbas ba!! Sai ace dasu: kamar ya bai inganta ba, alhalin wa'yanda suka fiku girma suka fiku falala suka fiku sanin Hadisi sun karbe shi?! Kuma kuce ba zamu karba ba.. To mu ya ishe mu kasancewa kwararrun Malamai; kamar Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah, da Ibnu Al- Qayyim -da ma wasun su- dukkanin su sun karbi wannan atharin kuma suna fadin sa, kuma suna nakalto shi, tabbas atharin ingantacce ne" .
Ibnu 'Abdi Al- Barr ya rasu shekara ta dari hudu da sittin da uku (463) bayan hijira -Allah ya jikan sa- yana cewa a cikin "التمهيد" mujalladi na biyar shafi na saba'in da hudu (5/74) :
"وأجمع العلماء على أن الجور في الحكم من الكبائر لمن تعمد ذلك عالما به، رويت في ذلك آثار شديدة عن السلف، وقال عز وجل (ومن لم يحكم بما أنزل الله فأولئك هم الكــٰفرون) [المائدة: ٤٤]. ، (الظالمون)، (الفاسقون)، نزلت في أهل الكتاب، قال حذيفة وابن عباس: وهي عامة فينا؛ قالوا: ليس بكفر ينقل عن الملة إذا فعل ذلك رجل من أهل هذه الأمة حتى يكفر بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر، وروي هذا المعنى عن جماعة من العلماء بتأويل القرآن منهم ابن عباس وطاووس وعطاء".
Yace:
Kuma Malamai sunyi ijma'i a kan cewa rashin adalci a cikin hukunci yana cikin manyan zunubai, ga wanda ya aikata hakan da gangan kuma yana sane da hakan, an ruwaito maganganun magabata masu tsanani a kan haka, kuma Allah mai girma da buwaya yana cewa: (Kuma wa'yanda basu yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba wa'yannan sune kafirai) [Al- Ma'idah: 44], yana cewa a mai bin ta (wa'yannan sune azzalumai), a mai bin ta yana cewa: (wa'yannan sune fasikai), an saukar da ita ne a kan Ahlu Al- Kitabi, Huzaifah da Ibnu 'Abbas suka ce: kuma ta game damu; suka ce: ba kafirci bane da yake fitarwa daga musulunci idan wani mutum ya aikata hakan daga cikin ma'abota wannan al'umnar har sai ya kafirce wa Allah da mala'ikun sa da littafan sa da Manzannin sa da rana ta karshe, kuma an ruwaito wannan ma'anar daga taron jama'a na masana ma'anonin Al- Qur'ani, cikin su da akwai Ibnu 'Abbas da Tāwus da Ata' ".
TO SU WANENE SUKA SABA MA WANNAN TAFARKIN?
Abu Al- Mudhaffar Al- Sam'āniy ya rasu shekara ta dari hudu da tamanin da tara (489H.) bayan hijira -Allah ya jikan sa- yana cewa a tafsirin sa (2/42) :
"واعلم أن الخوارج يستدلون بهذه الآية ويقولون: من لم يحكم بما أنزل الله فهو كافر، وأهل السنة قالوا: لا يكفر بترك الحكم" .
Yace:
"Kuma ka sani lallai khawarijawa (kamar a nan Nigeria ne kace 'yan Boko Haram) suna kafa dalili da wannan ayar kuma suna cewa: dukkan wanda bai hukunci da abin da Allah ya saukar ba to shi kafiri ne, amma su Ahlu Al- Sunnah cewa sukayi: baya kafirta da barin yin hukuncin".
Haka ma Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah -Allah ya jikan sa- yana cewa a cikin "منهاج السنة" mujalladi na biyar shafi na dari da talatin (5/130) :
قال تعالى: (فلا وربك لا يؤمنون حتى يحكموك فيما شجر بينهم ثم لا يجدوا في أنفسهم حرجا مما قضيت ويسلموا تسليما) [النساء: ٦٥] ؛ فمن لم يلتزم تحكيم الله ورسوله فيما شجر بينهم؛ فقد قسم الله بنفسه أنه لا يؤمن، وأما من كان ملتزما لحكم الله باطنا وظاهرا، لكن عصى واتبع هواه؛ فهذا بمنزلة أمثاله من العصاة، وهذه الآية مما يحتجّ بها الخوارج على تكفير ولاة الأمر الذين لا يحكمون بما أنزل الله، ثمّ يزعمون أن اعتقادهم هو حكم الله، وقد تكلم الناس بما يطول ذكره هنا، وما ذكرته يدل عليه سياق الآية".
Yace: Allah madaukaki yana cewa: (To a'a ha! Ina rantsuwa da Ubangijin ka, ba suyi imani ba har sai in sun yarda da hukuncin ka ga abin da ya saba a tsakanin su, sa'annan kuma basu samu wani kunci a zukatan su ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamawa) [Al- Nisā': 65]; duk wanda bai lazimci karbar hukuncin Allah da Manzon sa ba a cikin abin da ya auku na sabani a tsakanin su; to hakika Allah yayi rantse da kansa cewa lallai wannan bai yi imani ba, amma wanda ya kance ya lazimci karbar hukuncin Allah a boye da sarari, sai dai ya saba kuma yabi son zuciya, to wannan yana nan a matakin 'yan uwan sa (musulmi) masu laifi, kuma wannan ayar tana daga cikin dalilan da Khawarijawa suke yin hujja dasu wurin kafirta shuwagabannin da basa hukunci da abin da Allah ya saukar, sa'annan kuma suna raya cewa Aqeedar su ita ce hukuncin Allah, kuma hakika mutane sunyi maganganu wa'yanda ambaton su zai tsawo a nan, kuma abin da na ambata siyakin ayar yana nuni zuwa gare shi ".
Kenan; wa'yannan nakalolin guda biyu sun bayyana mana tafarkin Khawarijawa a wannan mas'alar haka kuma sun bayyana mana tafarkin Salafawan gaskiya, sannan kuma babu shakka 'yan Sururiyyah da shauran 'yan Ikhwan sun dace da Khawarijawa kuma sun saba wa ma'abota Sunnah a wannan mas'alar!
Haka ma Al- Imām Ibnu Al- Qayyim -Allah ya jikan sa- yana cewa a cikin "مدارج السالكين" mujalladi na daya shafi na dari uku da talatin da shida (1/336) :
والصحيح: أن الحكم بغير ما أنزل الله يتناول الكفرين: الأصغر والأكبر بحسب حال الحاكم، فإنه إن اعتقد وجوب الحكم بما أنزل الله في هذه الواقعة، وعدل عنه عصيانا، مع اعترافه بأنه مستحق للعقوبة؛ فهذا كفر أصغر. وإن اعتقد أنه غير واجب، وأنه مخيّر فيه، مع تيقنه أنه حكم الله، فهذا كفر أكبر. وإن جهله وأخطأه، فهذا مخطئ له حكم المخطئين".
Yake cewa: Kuma magana mafi inganci: lallai hukunci da sabanin abib da Allah ya saukar yana daukar kafirci guda buyu: karamin kafirci da babban kafirci gwargwadon halin mai yin hukuncin, idan ya kudurta wajabcin yin hukunci da abin da Allah ya saukar a cikin wannan abin da ya auku, sai ya kauce masa yana mai sabawa, tare da cewa yana tabbatar ma kansa cewa shi fa ya cancanci ukuba; to wannan kafirci ne karami, idan kuma ya kudurta cewa ba tilas bane, kuma shi yana da zabi a cikin sa, tare da cewa yana da yakinin cewa hukuncin Allah ne, to wannan kafirci ne babba, in kuma ya jahilce shi ko ya kuskure masa, to wannan mai kuskure ne, yana da hukunci ne na masu kuskure" .
Haka idan zamu ci gaba da lissafo maganganun jagororin Sunnah haka zamu ci gaba da gani, babu wanda yake goyon bayan 'yan Sururiyyah a cikin bin tafarkin Khawarijawa a wannan mas'alar.
Babban misali da zamu buga shine mas'alar Tauhidin hakimiyyah da Sayyid Qutb ya kafirta dukkanin dauloli da dukkanin mutanen duniya a kan ta, manufa a wajen sa kuma a wajen 'yan Sururiyyah shine in ya kasance mutum yayi hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar shi kenan ya zama arne jinin sa ya halasta, ko da yana Sallah ko da yana da Tauhidin kadaita Allah da bauta, kuma baya yiwa Allah tarayya da kowa a cikin bauta.
Wanda wannan irin tafarki shine abin da Sulaimān Al- 'Alwan daga cikin 'yan sururiyyah yake tabbatarwa shine yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar kafirci ne wanda yake fidda mutum daga da'irar musulunci kai tsaye sabanin abin da mai karatu ya karanta na maganganun magabata na kwarai a kan mas'alar, domin sauraren maganar tasa kana iya bin wannan link din a youtube :
(https://youtu.be/O5ZYePErJPU) haka ma Ahmad Al- Hāzimiy daga cikin 'yan Sururiyyah shima yana tabbatar da hakan (https://youtu.be/jRVzlugkDL4) .
A takaice; 'yan Sururiyyah suna wuce iyaka ne a mas'alar yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar ba don komai ba sai don karfafar ginshike daga cikin ginshikan Sururiyyah kuma shine ginshiki na farko "Tauheedin Hakimiyyah" .
Sai suka dace da Khawarijawan da suka ce da Sayyiduna Aliyu Bin Abi Tāleb -Allah ya kara masa yarda-
لا حكم إلا لله!
Ma'ana: Khawarijawa suka ce dashi "babu hukunci sai na Allah"!
Sun fadi wannan kalmar ne don karfafar ginshiki daga cikin ginshikan Aqeedar su wacce take kafirta duk wanda yayi hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar, suka saba ma tafarkin Sahabbai da fahimtar su, sai suka bace suka batar!
Raba ni da bonono rufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
14 / 08 / 1441
08 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق