RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (08)




FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (03)

Fikira ta gaba ita ce:

(¡¡¡) Yin sakaki da raini ga abin da ya shafi tawaye ga shuwagabanni musulmai da daukar mas'alar a matsayin mas'ala ce ta sabani, kuma sabani yana da mashiga a cikin ta, manufa idan wani yana ganin halascin tawaye ga shuwagabanni wani kuma yana ganin haramcin hakan to babu wanda za'a zarga a cikin su, wanda kuma hakan sabani ne ga Manhajin Annabta, baudewa ce ga tafarkin magabata na kwarai, kuma wannan tunanin tunani ne na Bid'ah, saboda Malaman Sunnah sun yi ijma'i a kan haramcin tawaye ga shuwagabanni musulmai, bal jagororin Sunnah sun rubuta a Aqeedar ma'abota Sunnah cewa haramun ne yin tawaye ga shugaba musulmi, kuma suna kirga tawayen a matsayin tafarki ne na 'yan Bid'ah, kuma a wajen ma'abota Sunnah wannan ba mas'ala ce wacce sabani yake da mashiga a cikin ta ba.

Hadisan da suka zo da umurni da biyayya ga shuwagabanni da hani daga yi musu tawaye, da hadisan da suka zo da umurnin yakar Khawarijawa (masu tawaye ga shuwagabanni), da hadisan da suka zo suna aibata Khawarijawa da siffanta yadda suke, da maganganun Malamai amintattu, duk 'yan Sururiyyah suka rufe ido daga gare su, kuma suke fadin cewa mas'ala ce wacce sabani yake da mashiga a cikin ta, kasancewar suna da ra'ayin tawaye wanda suke boye shi, dukda suna bayyana shi idan lokacin fitina yazo, kuma wanda ma bai san su ba suna bayyana gare shi a fili.

A takaice; an tambayi Shaikh Sāleh Al- Fauzān a kan irin wannan shubuhar ta 'yan Sururiyyah, mai tambaya yake cewa:

يتردد قول عند بعض طلبة العلم أن مسألة الخروج على ولي الأمر مسألة خلافية فما رأيكم جزاكم الله؟

Wata magana tana kai-komo a tsakanin wani sashe na daliban ilimi, suna cewa lallai mas'alar tawaye ga shugaba mas'ala ce wacce take ta sabani, menene ra'ayin ku , Allah ya biya ku?

الجواب:
هذا ما هو بطالب علم اللي يقول هذا طالب فتنة اللي يقول ها الكلام طالب فتنة ليس طالب علم ما هي بخلافية هذا بالإجماع تجب طاعة ولاة الأمور ما فيها خلاف قال تعالى: "يا أيها الذين آمنوا أطيعوا الله وأطيعوا الرسول وأولي الأمر منكم" وقال عليه الصلاة والسلام: "أوصيكم بتقوى الله والسمع والطاعة وإن تأمر عليكم عبد" فأين هذا اللي يقول أنها مسألة خلافية  نعم هذا إما أنه جاهل وإلا مضلل".

Sai ya bada amsa da cewa:
Wannan ba dalibin ilimi bane, wanda yake fadin wannan maganar dalibin fitina ne ba dalibin ilimi ba, wannan mas'ala ba mas'ala ce ta sabani ba, wannan anyi ijma'i ne, wajibi ne ayi biyayya ga shuwagabanni babu sabani, Allah madaukaki yana cewa: "ya ku wa'yanda kuka yi imani kuyi biyayya ga Allah kuyi biyayya ga Manzo da ma'abota al'amari daga cikin ku" , kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "ina muku wasici da tsoron Allah da ji da biyayya ko da bawa ne ya karbi shugabancin ku" . to ina wanda yake cewa mas'ala ce ta sabani? Na'am, wannan imma dai jahili ne ko kuma mai batarwa ne!
Kana iya sauraron fatawar ta wannan link din:
(https://youtu.be/BmoTKNvuzBE)


Lallai 'yan Sururiyyah suna yada wannan shubuha ne domin suyi kariya ga aikin da suke yi dare da rana na tawaye ga shuwagabanni da daukar hakan a matsayin gwarzantaka da umurni da kyakyawa da hani daga mummuna, kuma don su tabbatar da tawaye din, domin su kai zuwa ga kifar da gwamnatin da suka sanya a gaba.

Kai raba ni da bonono rufin kofa da barawo!

أمين ثالث يعقوب
15 / 08 / 1441
09 / 04 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!