KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA
KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA
Allah madaukaki yana cewa:
وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ اجْعَلْ هَٰذَا الْبَلَدَ آمِنًا وَاجْنُبْنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعْبُدَ الْأَصْنَامَ [ابراهيم : 35]
Kuma ka tuna Ibrahim a lokacin da yake cewa : ya Ubangiji ka sanya wannan gari ya zama amintacce kuma ka nisantar dani da 'ya'ya na daga bautar gumaka (Ibrahim: 35).
Annabi Ibrahim -Alaihi al- Salām- yayi addu'a ya roki Allah a kan cewa ya amintar da haramin Makkah kuma sannan ya nisantar da shi da 'ya'yan sa daga bautar gumaka, lallai duk wanda yake neman zaman lafiya da aminci na rayuwar duniya harma da ta lahira to dole ya roki Allah shi kadai, kenan ana rokon ne ga Allah shi kadai, ba'a rokon wanin Allah abin da babu mai iya bayarwa sai Allah, yin haka shirka ne fada ne da Allah din, kuma babu wanda ya isa yayi fada da Allah bare yai nasara, sannan bayan an samu zaman lafiyar kuma to babu abin da zai wanzar da wannan zaman lafiyar ya samu dorewa a samu facakar tattalin arziki, a samu natsuwa birni da kauye tudu da teku, a daina shakkar 'yan fashi da barayi masu sace mutane, a daina shakkar duk wani azzalumi, to hakan bata samuwa sai in an tabbatar da bauta ga Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, idan ko aka kuskure aka yi shirka aka dogara ga wanin Allah to Allah zai dauke wannan ni'mah zai mayar da wahala a madadin ta, shi yasa Tauhidi shi ne silar samun zaman lafiya, shi ne mabudin ayyuka na kwarai, kamar yadda shirka kuma ita ce silar gushewar zaman lafiya da duk wani sharri a duniya da lahira.
Na rantse muku da Allah in dai har ana shirka ana cin riba ana neman yaki da Allah ba za'a taba gani da kyau ba.
In muna so duniyar mu da lahirar mu suyi kyau to mu koma ga Allah mu bauta masa shi kadai mu tsayar da dokokin sa a kan mu, mu tsayar da adalci a kan masoyin mu da makiyin mu, mu guji mafi munin zalunci shirka da shauran sabon Allah da zaluntar na kasa damu da na sama damu, mubi Sunnah mu jibinci ma'abotan ta, mu nisanci bid'ah da makirayan ta, mu saurari taimakon Allah.
Wallahi duk abin da bawa ya shuka shi zai girbe, in ka shuka alkhairi zaka girbi alkhairi, in ka shuka sharri sharri zaka girbe. Allah baya zalunci kuma ya haramta zalunci ga kan sa kuma ya haramta shi ga dukkan bayin sa.
Ku tsaida adalci mafi girma Tauhidi, kubi Sunnah kuyi ma kan ku adalci, tare da yin adalci a tsakanin ku. Ku saurari taimakon Allah, amma in har yanzu baku yarda ba, kuna sauraron taimakon wani shugaba ne da zai zo nan da shekara biyu ya fitar daku daga mawuyacin hali zuwa hali na jin dadi, wai ya fitar daku daga tarzoma zuwa zaman lafiya, wai ya fitar daku daga talauci zuwa arziki, wai ya fitar daku daga tashin farashin kaya zuwa arahar kaya, to har yanzu baku farka daga dogon suman ku ba, kuma har yanzu baku san menene zaman lafiya da hanyoyin samun sa ba, baku san fitintinu da hanyoyin fita daga gare su ba.
Madalla da bayin da suke gane kuskuren su su koma ga Allah rayayye tsayayye, tir da masu ta'llaka jin dadin su ga 'yan uwan su halittu masu rauni, masu zaluntar kawunan su.
أمين ثالث يعقوب
13 / 05 / 1443
18 / 12 / 2021
تعليقات
إرسال تعليق