MAGANA AKAN 'YAN BID'AH DA MASU KARKATACCEN MANHAJI BA GIBA (GULMA) BACE
❁❁❁❁❁❁ ــــــ ❁❁❁❁❁❁ ـــــ ❁❁❁❁❁❁
Fatawar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen (Allah ya jikansa) :
❍ الشيخ محمد بن صالح العثيمين :
السّـؤال : الكلام في أهل البدع ، مثل أن يقال مثلاً: أنهم يؤولون الآيات والأحاديث، ويقولون: يفعلون كذا وكذا.. أيعتبر هذا غيبة إذا كان بين الطلبة ؟
Tambaya: Magana akan 'yan Bid'ah, kamar misali ace: sunayin tawilin ayoyi da hadisai, kuma suna aikata kaza da kaza, shin wannan ana daukarsa giba (gulma) ce in ya kasance a tsakanin dalubai ne?
»» الجواب: الكلام في أهل البدع ومن عندهم أفكار غير سليمة أو منهج غير مستقيم، هذا من النصيحة وليس من الغيبة ، بل هو من النصيحة لله ولكتابه ولرسوله وللمسلمين ، فإذا رأينا أحداً مبتدعاً ينشر بدعته ، فعلينا أن نبين أنه مبتدع حتى يسلم الناس من شره ، وإذا رأينا شخصاً عنده أفكار تخالف ما كان عليه السلف فعلينا أن نبين ذلك حتى لا يغتر الناس به ،
Amsa: Magana akan 'yan Bid'ah da masu tunani wanda ba lafiyayye ba, ko masu manhaji wanda ba mikakke ba, magana akansu yana cikin nasiha ne, bata cikin giba (gulma), bari ma dai, tana cikin nasiha ne ga Allah da littafinsa da Manzonsa da musulmai, to idan mukaga wani yana yada Bid'arsa to ya zama wajibi mu bayyana cewa wane dan Bid'ah ne saboda mutane su kubuta daga sharrinsa, haka in muka ga mutum dauke da wasu afkar(tunane-tunane) wa'yanda sun sabawa tafarkin da magabata suka tafi akai to ya zama wajibi muyi bayanin haka saboda kar mutane su rudu dashi,
وإذا رأينا إنساناً له منهج معين عواقبه سيئة فعلينا أن نبين ذلك حتى يسلم الناس من شره ، وهذا من باب النصيحة لله ولكتابه ورسوله ولأئمة والمسلمين وعامتهم.
Kuma idan muka ga mutum wanda yake akan wani Manhaji ayyananne wanda karshensa sharri ne, to ya wajaba akan mu da mu bayyana haka domin mutane su kubuta daga sharrinsa, kuma wannan yana cikin babin nasiha ne ga Allah da littafinsa da Manzonsa kuma ga jagororin Musulmi da gama-garin su.
وسواء كان الكلام في أهل البدع فيما بين الطلبة أو في المجالس الأخرى فليس بغيبة ، وما دمنا نخشى من انتشار هذه البدعة أو هذا الفكر أو هذا المنهج المخالف لمنهج السلف يجب علينا أن نبين حتى لا يغتر الناس بذلك.
Kuma sawa'un wannan magana akan 'yan Bid'ah ta kasance ne tsakanin dalibai ko a wasu majalisai na daban to wannan fa ba giba bace(haramtacciya), ma damar muna jin tsoron yaduwar wannan Bid'ah ko wannan tunani ko wannan Manhaji wanda ya sabawa Manhajin Salaf, lallai ya wajaba a garemu da mu bayyana kar mutane su rudu da wannan.
◣ *【فتاوى نور على الدرب (120) 】◢*
Kenan:
Shaikh Muhammad Bin Sālih Al- Uthaymeen (Allah ya jikan sa) yabi tafarkin magabata wajen tsoratarwa akan 'yan Bid'ah da masu wani Manhaji wanda ya saba wa na Magabatan, don gudun sharrin su kar ya yadu yayi tasiri a tsakanin al'ummah, ba tare da yace ayi dubi zuwa ga kyawawan ayyukan su ko a ambace kyawawan ayyukan a yayin tsoratarwa daga gare su ba, sabanin masu Manhajin Bid'ar Muwazanat, wanda asali manhaji ne Ikhwaniyawa fallasassu, wanda suka kirkireshi don baiwa mabarnata kariya.
Abin da zai kara tabbatar maka da cewa Shaikh Ibnu Al- Uthaymeen bai bi Manhajin Muwazanat ba shine: idan ka saurari tsoratarwar da yayi akan Ikhwaniyawan nan guda: biyu Dr. Salman Al- Audah da Dr. Safar Al- Hawāliy wa'yanda (Manhajin su na Ikhwan kuma dama karshen sa babu kyau) masu yada tunani da Aqidar khawarijawa a tsakanin matasa, da kuma halasta musu fito na fito ga shuwagabanni Musulmai, kamar shi Salmān Al- Audah ya taba fitowa anyi muzaharah dashi tare da matasan da suke zaburarwa, kuma wannan shine dalilin da Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen din yasa yayi tsoratarwa daga garesu din, kuma shaikh bai ambaci wani alheran su ba, saboda waje ne na tsoratarwa, kuma manhajin Ahlus- Sunnah bai ginu akan ambaton alherai wajen tsoratarwa ba.
A yanzu haka duk suna garkame a kurkuku su da ire-iren su, saboda irin Manhajin nasu na Ikhwan wanda yake yada Aqidar khawarijanci, da tada zaune tsaye, da halasta jinin shuwagabanni don tabbatar da muradun kungiyar su.
Allah ya kiyaye mana imanin mu, ya kare mu daga zamiya da komawa cikin bata bayan shiriya.
Dan uwan ku a Musulunci da Sunnah:
أمين ثالث يعقوب
24 / 12 / 1439
05 / 09 / 2018
تعليقات
إرسال تعليق