SALAFAWAN GASKIYA

 SU WANENE SALAFAWAN GASKIYA? 


KO KA SAN MU WA'YANDA AKE CEMA SALAFAWA KUWA? 


To a takaice mu din:


Muna daukar akidar mu ne kai tsaye daga littafin Allah da ingantattun hadisan Manzon Allah sallallahu 'alayhi wasallam. 


Tafarkin mu kuma shi ne tafarkin magabata na kwarai in kaso ka fada da larabci tafarkin Salaf ko kace Salafiyyah. 


Muna gabatar da fahimtar Sahabban Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam- (wa'yanda sune jagororin Salaf a bayan Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam wa radhiyallahu 'anhum-. 

Muna gabatar da fahimtar su da maganganun su da maganganun mabiya tafarkin su da kyautatawa na daga jagororin musulunci, na jiya da na yau a kan fahimtocin wa'yanda ba su ba. 


Muna gane tafarkin mutum dai-dai ne idan ya dace da tafarkin Sahabbai da mabiya tafarkin su da kyautatawa, kuma muna gane tafarkin mutum ba dai-dai bane idan ya saba ma ijma'in magabata din. 


Muna martani ga dukkan wanda ya saba ma gaskiya na kusa damu ne ko na nesa damu, muna kwadaitar da musulmai komawa zuwa ga tafarkin magabata na kwarai domin hakan shi ne tsiran mu ga baki daya, kuma shi ne zai hada tsakanin zukatan mu ko da kuwa gangar jikin sashe yayi nesa da na sashe. 


Muna bada mahimmanci a kan bayyana Tauhidi (bauta ma Allah shi kadai) da tsoratarwa daga shirka (bautar wanin Allah tare da bautar Allah) 

Kuma muna yawaita magana a kan hakan, shi din ne ma muka fi baiwa mahimmanci. 

https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-9368537216501702

Muna tabbatar ma Allah da sunayen sa da siffofin sa waƴanda suka zo a littafin sa da Sunnar Annabin sa (Sallallahu alaihi Wasallam) bama ƙetare littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) wajen tabbatar da sunaye da siffofin Allah, kuma muna karɓen su yadda suka zo, bama kutsawa cikin fassarar su da tawilin ma'abota surutu, muna barin su a zahirin su, muna tabbatar wa da Allah cikakken sani; ya sani ya rubuta a littafi tun kafin abu ya auku da ikon sa, muna cewa Allah ya dai-daita a kan Al- Arshi dai-daituwar da ta dace dashi, muna sanin ma'anar hakan amma muna komar da sanin yanayin hakan ga Allah, muna cewa Allah yana ji, Allah yana gani, ji na haƙiƙa gani na haƙiƙa, amma bamu san yadda yake ba, saboda bai ga damar sanar damu yadda yake ba, Allah yana yarda, yana ƙin yarda, yana so, yana ƙi, yana ganin dama, yana ƙin ganin dama, yana da iko, yana fushi, yana farin ciki, yana kishi, yana da fuska, yana da hannaye, yana da yatsu, yana dariya, yana damƙa, kuma zai damƙe sammai da ƙassai da hanun daman sa a ranar Ƙiyama, zai damƙi bishiyoyi da ruwa da turɓaya da duwatsu da dukkan halittu sannan zai girgiza su sannan yace: "Ni ne Mamallaki, ni ne Allah", yana da dudduge, yana da ƙwauri, yana saukowa saman duniya ɗaya bisa ukun ƙarshe na kowane dare yana sauraron masu neman gafara da masu neman arziƙi don ya biya musu buƙatun su, dukkanin siffofin Allah maɗaukaki muna tabbatar dasu ba tare da kamanta shi da halittun sa ba, domin babu wani da yake tamka gare shi, kuma babu wani wanda ya kewaye Allah da sani, kuma babu wanda ya kai Allah sanin Allah, kuma babu wani wanda ya san Allah bayan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya san Allah.


Muna kira zuwa ga ruko da Sunnah ko da ta saba ma ra'ayin duk wani mai girma domin babu mai girma wanda girman sa yayi kusa da girman Manzon Allah (Sallallahu 'alayhi wasallam) 


Muna son Sahabbai ga baki dayan su, muna son Ahlu al- Baiti muna cewa Allah ya kara musu yarda ga baki dayan su. 

Muna kudurta cewa matan Annabi -Sallallahu 'alayhi wasallam wa radhiyallahu 'anhunna- dukkan su tsarkakakku ne, kuma dukkan su uwayen muminai ne. 

Muna kudurta cewa babu mai sukar su sai asararre mutumin banza kazantacce. 


Muna girmama Malaman Hadisi ma'abota Sunnah, muna lura da sharhohin su, kuma muna lura da hukuncin su kan malamai da maruwaita hadisi. 

Harda na wannan zamanin da muke ciki, kuma muna kallon mai sukar su a matsayin dan bid'ah. 


Muna mutunta dalili kuma muna karkata zuwa gare shi da ma'abotan sa a duk inda Malamai sukai sabani. 


Muna son Malaman fiqhu kuma muna mutunta zantukan su muna yin fara'a dasu inda basu ci karo da Sunnah ba, inda suka ci karo da Sunnah kuma muna ajiye su tare da roka musu gafarar Allah da karin daraja a wajen Allah. 


Muna ganin cewa dole ne a mayar da sabani zuwa ga Al- Qur'ani da Sunnah a bisa fahimtar magabata na kwarai. 


Muna ganin cewa jahilci ne a mayar da sabani zuwa abin da ba hakan ba. 


Muna bauta ma Allah da ji da biyayya ga shuwagabanni musulmai ba tare da duba hanyar da suka kai ga mulki ba, matukar ragamar mulki ta tabbata a hannun su to shuwaganannin mu ne muna mutunta su muna musu addu'ar dacewa, muna kudurta cewa tsayar da haddi a kan masu laifi sune zasu zartar sune zasu yanke hannun barawo, sune kadai zasu rufe gidajen giya, sune kadai zasu ma mazinata bulala sune kadai zasu kira jahadi kuma su jagorance shi kuma su bada tuta, muna ganin haramcin fito na fito gare su da kuduri ko da kalma ko da yatsa ko da makamai, kuma muna kudurta cewa tawaye ga shuwagabanni yana farawa ne daga zuciya sannan harshe sannan makami. Muna kudurta cewa dukkan su saba ma Sunnah ne, kuma bid'ah ce mummuna, ma'abocin ta baya da alaka da Salafiyyah ko ta kusa ko ta nesa. 


Muna ganin cewa zanga-zanga haramun ce ko wacce iri ce ko an kira ta da ta lumana, muna ganin cewa hakan ba shi ne mafita ba, mafita tana cikin biyayya ga tafarkin Annabta, muna umurni da hakuri a kan zaluncin shuwagananni kamar yadda hadisai suka bayyana. 


Muna umurni da kyakkyawa muna hani daga mummuna gwargwadon yadda sharee'ah ta tanadar. 


Muna kulla so da ki a kan addinin Allah, muna kyautata zato ga muminai bama cewa wane dan aljannah ne, muna jiye ma masu sabon Allah tsoro amma bama ayyana mutum muce shi dan wuta ne.


Muna kudurta cewa imani ya kunshi gaskatawar zuci da furucin harshe da aikin gabbai. 


Muna kudurta cewa Allah yana sama, muna kudurta cewa babu wanda ya san gaibu sai Allah. 


Muna hani daga rarrabuwar musulmai zuwa kungiyoyi da darikoki duk sun saba ma addinin da Annabi -Sallallahu 'alayhi wassalama- yazo mana dashi, na haduwa a kan Sunnah da shiriyar Sahabbai da ji da biyayya ga shuwagananni da rashin kekkecewa cikin tafarkoka da kungiyoyi mabanbanta masu saba ma tafarkin Annabta. 


Muna ganin shar'antuwar nasiha ga shuwagabanni a sirrance kamar yadda hakan yazo a Sunnah, kuma muna ganin cewa yin ta a minbari ko bainar jama'a wannan bid'ah ce, kuma bata ne, ba abin yabo bane, kuma ba gwarzantaka bane, gwarzo shi ne wanda yaje ya gana da shugaba yayi masa nasiha kuma bai zo yana yayata wa ba. 


Muna kin 'yan bid'ah muna tona asirin su, muna kaurace musu, saboda magabata na kwarai sun yi ijma'i a kan haka. 


A takaice; muna kudurta dukkan abin da magabata na kwarai suka kudurta suka karantar na addini, kuma dalilan haka suna nan birjik. 


A kan haka muke, a kan haka muke fatan Allah ya karbi rayukan mu. 

A kan haka duk wanda kaga yana fada damu yake fada damu. 


أمين ثالث يعقوب 

18 / 03 / 1443

25 / 10 / 2021

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!