Wani yayi tambaya yace: "menene ma'anar Sururiyyah?"
Sai nace dashi:
Kungiya ce wacce ake nasabta ta ga Muhammad Surur Zainul Abideen, wanda asalin sa dan Syria ne, yayi zama a Saudiyyah shekaru 8, yayi karatu a Kwalejin ilimi a Buraidah, daga nan ya koma Brtaniya, ya koma Qatar wanda a nan ya mutu a shekarar 2016, wannan kungiya ta Sururiyyah an san ta ne da gauraye tsakanin Sunnah da Ikhwaniyan ci, sune suka kawo rudanin cewa Aqeedar Mutum Salafiyyah amma Manhajin sa Ikhwaniyyah, an san su da tawaye ga shuwagabanni Musulmai, tawaye na kalma da kuma karfafar Khawarijawa masu yakar gwamnatocin su, da yaba musu, da kuma tunzura matasa a kan zanga-zanga ma gwamnatocin su, da da'awar neman 'yanci ko kuma inkari ga azzalumai, sannan suna kambama Sayyid Qutb da tawagar sa 'yan ta'adda, basa kuma ganin cewa akwai gwamnatin Musulunci a wannan zamanin, suna kiran shuwagabanni Musulmai da الطواغيط (ma'ana: dagutai) sannan suna jifan Malaman Sunnah wa'yanda suke hani daga tawaye ma shuwagabanni da cewa su علماء السلاطين (ma'ana: malaman sarakuna) ne, kuma suna jifan Manyan Malaman Sunnah irin su Shaikh Bin Baz, Muqbil, Albani cewa su basu fahimci zamanin su ba, kuma su علماء الحيض والنفاس (ma'ana: Malaman haila da biki) ne, idan kana neman fatawa a kan Aqeedah ko ibadah ko mu'amala ka tafi wajen Malaman, amma in kana neman fatawa akan zamani kaje wajen 'yan gwagwarmaya, domin sune suka san فقه الواقع (fahimtar zamani) Malamai kuma basu sani ba, suna goyon bayan juyin mulki da kunar bakin wake
Kuma suna zurfafawa akan مسألة الحكم بغير ما أنزل الله (ma'ana: mas'alar yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar) suna kafirtawa akan ta مطلقا (a sake babu ka'ida) , sannan suna kafirta المصر على المعصية (wanda yaci gaba da yin sabo, kamar yadda Abu Ishaq Al- Huwainiy yake tabbatar da wannan Aqidar), kuma suna kira zuwa ga Jihadi ba a karkashin ولي الأمر (shugaba) ba, suna ingiza matasa suje su shiga kungiyoyin ta'adda da ake kira kungiyoyin jahadi, sannan kuma suna yabon kungiyoyin ta'addan suna jinjinawa jagororin su .
Kari a kan ababen da na ambata masa:
- Suna lazimta yin Al- Muwāzanah (ma'ana: auna dai-dai da laifi) a yayin martani ga 'yan Bid'ah, suna nufin a rinka ambaton alheri tare da sharri, suna da'awar cewa wai haka shine adalci, amma kuma ba haka abin yake ba, domin wannan ka'ida tasu ta saba wa Manhajin Annabta, kuma Malaman Sunnah sunyi musu raddoji akan wannan ka'idoji nasu, daga cikin wa'yanda suka yi martanin wannan ka'ida akwai Shaikh Bin Baz yake cewa:
من أظهر المنكر أو البدعة يحذر منه ولا ينظر إلى حسناته، حسناته بينه وبين ربه.
Ma'ana: duk wanda ya bayyana abin ki ko Bid'ah to za'a tsoratar daga gare shi, kuma ba za'a duba kyawawan ayyukan sa ba, (domin) kyawawan ayyukan sa tsakanin sa ne da Ubangijin sa.
Kana iya sauraren sama da haka a cikin wannan murya da zan dora, bal ma Shaikh yace za'a yada tsoratarwar da bayani akan sharrorin su a littafai da gidajen radio da jaridu! .
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=918683938310613&id=100005070461845
Haka ma Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albaniy -Allah ya jikan sa- yayi musu martani, da Shaikh Sāleh Al- Fauzān, da Shaikh Rabee' Al- Madkhaliy a wallafar sa .
Ga maganar ta Shaikh Muhammad Nāsiruddeen Al- Albāniy (Allah ya jikan sa) a sauti :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=811718032340538&id=100005070461845
Ga kuma wata magana ta Shaikh Muhammad Amān Al- Jāmiy (Allah ya jikan sa)
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=943856245793382&id=100005070461845
A kan su ne Shaikh Muhammad Nasirudden Al- Albāniy -Allah ya jikan sa- yake cewa:
"الجمع بين السلفية والإخوانية كالجمع بين الصواب والخطأ إن لم أقل بين الهدى والضلال"
(سلسلة الهدى والنور - 699).
Ma'ana: hada tsakanin Salafiyyah da Ikhwaniyyah kamar hada tsakanin dai-dai da kuskure ne in ma ban ce tsakanin shiriya da bata ba!. (Silsilatu Al- Hudā wa Al- Nur 699).
أمين ثالث يعقوب
29 / 01 / 1441
29 / 09 / 2019
تعليقات
إرسال تعليق