RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO ! (01)



- Hassan Al- Banna shine ya assasa kungiyar Ikhwan wanda shi ya mutu tun shekarar turawa na alif da dari tara da arba'in da tara (1949) kawo yanzu yana da shekaru saba'in da daya (71) a kasa .

- Wannan kungiya ci gaba ne ga fikirorin khawarijawa (bayanai zasu fito in sha Allah) kuma tana da tarbiyya ne ta Sufaye tare da tsare-tsare na kungiyanci na siyasa, a karon farko ta bayyana ne ba tare da fitowa a rigar Sunnah ba, wanda hakan ya sa mutane da yawa basu karbe ta ba, bal sunyi inkarin ta musamman a yankunan Saudiyyah, Bahrain, Qatar, Kuwait, Imarat, Oman.. Musamman saboda rashin lazimtar su ga Sunnah!

- Sai dai ta samu karbuwa a tsakanin wayayyun 'yan Boko zalla haka kuma 'yan inna rududu daga cikin gama-garin mutane sun tasirantu da ita (ja ya fado ja ya dauka kenan!).

- Daga cikin ababen da suka yaudari mutane dashi shine bayyanar da yaki da Yahudawa abokan adawa (Zionist), tare da rufe kofar martani ga 'yan Bid'ah da hujjar cewa ana son a dayanta sahun musulmai, saboda haka lokaci ba zai bayar da damar taba 'yan Bid'ah ba kuma hadafin dake gaban mu yafi girma a kan martani ga 'yan Bid'ah!!! Nan da nan sai wannan fikirar ta yadu cikin wani sashe na mutane ta cafke zukatan gama-garin su, nan take suka karkata zuwa gare su daya bayan daya, tare da wanzuwar wasu mutanen kuma da basu yarda sun amince musu ba, tare da kuma ana samun wani nau'i na tausayin su a wani sashe na mutane .


Kafin in jaku da magana, bari mu bayar da fagen ga Al- Shaikh Sāleh Bin 'Abdillāh Al- Fauzān -Allah ya kiyaye shi- domin ya haskaka mana a kan masu cewa a daina shagaltuwa da tona asirin 'yan Bid'ah domin maslahar fada da abokan gaba na yahudu da nasara

سئل العلامة صالح الفوزان -حفظه الله تعالى- :
لماذا التحذير من أهل البدع والأمة تصارع العداوة مع اليهود والنصارى والعلمانيين؟

An tambayi Shaikh Sāleh Al- Fauzān -Allah ya kiyaye shi- aka ce: me yasa ake tsoratarwa daga 'yan Bid'ah alhali kuma al'ummah tana cikin fada da adawa tare da yahudawa da nasara da 'almaniyyun?

فأجاب: لا يمكن للمسلمين أن يقاوموا اليهود والنصارى إلا إذا قاوموا البدع التي بينهم، يعالجون أمراضهم أولاً؛ حتى
ينتصروا على اليهود والنصارى،

Sai ya bada amsa yace: ba yadda za'ayi musulmi suyi galaba a kan yahudawa da nasara sai idan sun fara galaba a kan bid'o'in da suke a tsakankanin su, sai sun fara maganin cututtukan su a karin farko, daga nan sa samu taimakon Allah a kan yahudawa da nasara,

أما ما دام المسلمون مضيعين لدينهم، ومرتكبين للبدع والمحرمات، ومقصرين في امتثال شرع الله فلن ينتصروا على اليهود ولا على النصارى،

Amma dai ma damar musulmai suna lalata addinin su, suna aikata bid'o'i da haramtattun abubuwa, kuma sun tauye a cikin aiwatar da abin da Allah ya shar'anta musu to ba zasu taba samun nasara a kan yahudawa ba haka ba zasu taba samun nasara a kan nasara ba,

 وإنما سُلطوا عليهم بسبب تقصيرهم في دينهم.
فيجب تطهير المجتمع مـن البدع، وتطهيره مـن المنكرات، ويجب امتثال أوامر الله وأوامر الرسول -صلى الله وعليه وسلم- قبل أن نحارب اليهود والنصارى، وإلا إذا حاربنا اليهود والنصارى ونحن على هذه الحالة فلن ننتصر علهيم أبداً وسينتصرون علينا بذنوبنا.
 [الإجابات المهمة في المشاكل الملمّة 1/ 150-151].

Abin sani ma ai sunyi musu dare-dare ne domin tauyewar su cikin addinin su.
Saboda haka ya zama wajibi a tsarkake mutane daga bid'o'i, da tsarkake su daga ababen ki, kuma wajibi ne ayi aiki da umurce-umurcen Allah da umurce-umurcen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kafin mu yaki yahudawa da nasara, amma in ba haka ba, idan muka yaki yahudawa da nasara alhali muna cikin wannan halin to ba zamu taba samun nasara a kan su ba har abada, sai dai zasu samu nasara a kan mu saboda zunuban mu".
[Al- Ijābāt Al- Muhimmah 1/150 - 151].

Kenan; ba za'a daina tona asirin 'yan bid'ah ba da hujjar cewa wai muna da wasu abokan gabar sama dasu, domin dole mu gyara cikin gida kafin mu shiga gyaran waje, sannan mai hankali idan aka shiga cikin jirgin ruwa ko da ba'a kai tsakiya ba idan yaga wani daga cikin kwale-kwalen yana sanya adda ko zarto yana fafuke kasan jirgin, kai ko da kusa ya sanya yana huje kasan jirgin, babu makawa mahaya wannan jirgi zasu bayar da muhimmancin su domin suga sun dakile aikin wannan mabarnaci fiye da kwadayin da suke yi na kama manyan kifaye da suke cikin ruwa ko da ma wa'yanda suke cikin calin su ne!

Kai raba ni da bonono rufe kofa da barawo!!

أمين ثالث يعقوب
10 / 08 / 1441
04 / 04 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!