RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (10)



FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (05)

(vi) fikira ta biyar ita ce: tabbatar da mas'alar Al- Muwazanāt (ma'ana: yin gwaji tsakanin kyawawan ayyuka da munana) a yayin yin martani ga dan Bid'ah, ta yadda za'a ambaci kyawawan ayyukan sa da munanan a yayin yi masa raddi, wanda hakan yana kaiwa zuwa ga yin sakaki da ko in kula a kan martani ga 'yan Bid'ah da son zuciya .

Shaikh Bin Baz yana martani ga wannan Manhaji na Al- Muwazanāt wanda yake lazimta yin awo tsakanin ayyukan 'yan Bid'ah yake cewa:

"من أظهر المنكر أو البدعة، يحذر منه، ولا ينظر إلى حسناته، حسناته بينه وبين ربه.."

Ma'ana: duk wanda ya bayyana abin ki ko Bid'ah za'a tsoratar ne daga gare shi, kuma ba za'a yi dubi zuwa kyawawan ayyukan sa ba, domin kyawawan ayyukan sa tsakanin sa ne da Ubangijin sa!

Kana iya sauraren wannan magana tare da maganar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen -Allah ya jikan su- a kan maganar da ta shafi wannan, kai tsaye kabi wannan link din: (https://daralmahajjatalbaydhaa.blogspot.com/2019/09/magana-akan-yan-bidah-da-masu.html?m=1)

Haka ma a cikin martani ga wannan Bid'ah ta 'yan Sururiyyah wacce take lazimta ambaton kyawawan ayyukan 'yan Bid'ah yayin raddi gare su ko tsoratarwa da nisantarwa daga gare su, Shaikh Sāleh Al- Fauzān -Allah ya kiyaye shi- yana cewa da aka yi masa wata tambaya kamar haka:

A cikin littafin "Al- Ajwibatu Al- Mufeedah" an tambayi Shaikh Sālih Al- Fauzan -Allah ya kiyaye shi- , ga tambayar kamar haka:

س١٠: هل يلزمنا ذكر محاسن من نحذر منهم؟

Tambaya ta goma: shin ya zama dole mu ambaci kyawawan ayyukan wanda muke tsoratarwa daga garesu?

جـ/ إذا ذكرت محاسنهم فمعناه أنت دعوت لاتّباعهم، لا، لا تذكر محاسنهم . اذكر الخطأ الذي هم عليه فقط؛ لأنه ليس موكولا إليك أن تزكي وضعهم،

Amsa: idan ka ambaci kyawawan ayyukan su to ma'anar hakan shine kira kayi a bisu, a'a, karka ambaci kyawawan ayyukan su, ka ambaci kuskuren da suke akan sa kawai; domin kai ba'a wakilta gareka ba tsarkake kuren su,

أنت موكول إليك بيان الخطأ الذي عندهم من أجل أن يتوبوا منه، ومن أجل أن يحذره غيرهم،

Yace: abin da aka wakilta gare ka shine ka ambaci kuskuren da yake tare dasu domin su tuba daga gare shi, sannan kuma domin wa'yanda basu ba ma su kiyayi wannan kuskuren,

والخطأ الذي هم عليه ربما يذهب بحسناتهم كلها إن كان كفرا أو شركا،
Yace: sannan kuma kuskuren da suke a kansa ta yiwu ma ya rushe ayyukan alkhairan nasu ga baki daya in ya kasance kafirci ne ko kuma shirka,

وربما يرجح على حسناتهم، وربما تكون حسنات في نظرك، وليست حسنات عند الله.

Yace: sannan yana ma iya yuwuwa kuskuren ya rinjayi kyawawan ayyukan, kuma yana ma iya yiwuwa kai a wajen ka ne ma kake ganin ayyukan nasu masu kyau ne, amma kuma a wajen Allah ba masu kyau din bane!».
(Al-Ajwibatul Mufeedah page 32 - 33)

Shaikh Jamāl a karkashin wannan fatawa yayi ta'aliki mai fa'idah yake cewa:

(٣٣) في ذكر محاسن المبتدع تغرير بالناس وإن ذكرتَ مساوئه؛ لأنهم لن ينظروا إلى المساوئ ما دمت أنك أثنيت عليه خيرا،
Yake cewa :
(33) a cikin ambaton kyawawan ayyukan dan Bid'ah akwai rudar da mutane ko ma ka ambaci kura-kuran nasan; domin su (mutane) ba zasu duba kusa-kuran ba, matukar ka riga ka yabi wannan dan Bid'ah ka ambaci alherin akan sa,

ولم يكن من منهج السلف الثناء على أهل البدع في النقد.
Yace: kuma baya daga cikin Manhaji (tafarkin) magabatan mu (Salaf) ambaton kyawawan ayyukan dan Bid'ah a yayin martani .

فهذا الإمام أحمد رحمه الله تعالى لم يثن على حسين الكرابيسي عندما بين حاله، وقال عنه «مبتدع» .

Yace: to ga Al- Imāmu Ahmad nan bai yabi Husain Al- Karābīsiy ba a yayin da ya bayyana halin sa yace «Dan Bid'ah ne» .
بل حذر منه ومن مجالسته، وكذا حذّر تحذيرا شديدا من مجالسة المحاسبي . وسيأتي نقله في حاشية رقم (٤٩) .
Yace: hasali ma tsoratarwa ce kawai yayi daga garesa kuma daga zama tare dashi, kuma haka nan (Al- Imāmu Ahmad) din yayi tsoratarwa mai tsanani daga zama tare da Al- Muhāsibiy. Kuma nakalin maganarsa zata zo a hashiyah mai lamba ta (49) .

Shaikh Jamāl yaci gaba da ta'alikin sa yace:

وهذا أبو زرعة رحمه الله سئل عن الحارث المحاسبي وكتبه فقال للسائل: «إياك وهذه الكتب، هذه كتب بدعة وضلالات، عليك بالأثر» .
Yace: kuma ga Abu Zur'ata Allah ya jikan sa an tambayeshi game da Al- Hārith Al-Muhāsibiy da kuma littafan sa, sai yace: «ka kiyayi wa'yannan littafan, wa'yannan littafan Bid'ah ne da bata, ka rike athar».

Yaci gaba da cewa:
ولا يخفى عليك -أخي القارئ- أن الكرابيسي والمحاسبي من بحور العلم، ولهم ردود على أهل البدع، ولكن الأول سقط في القول باللفظ في القرآن، والآخر سقط في شيء من الكلام، ورد على أهل الكلام بالكلام ولم يردّ بالسنة . . .

Yace: kuma baya boyuwa gare ka -ya kai mai karatu- cewa Al- Karabīsiy da Al- Muhāsibiy kowannen su kogi ne na ilimi, sannan kuma suna da raddoji a kan ma'abota Bid'ah , sai dai na farko ya auka cikin fadin lafazin bayi ga Al-Qur'ani halittacce ne, dayan kuma ya fada ne cikin falsafanci ta yadda yayi martani ga falsafawa da falsafanci, baiyi musu martani da Sunnah ba. . .

هذه أهم نقطة أنكرها عليه الإمام أحمد، راجع : التهذيب (١١٧/٢) ، تاريخ بغداد (٨/ ٢١٥-٢١٦) ، السير للذهبي (١١٠/١٣) (٧٩/١٢).

Yace: wannan shine mafi mahimmancin gaba da Al- Imam Ahmad ya kyamata a kan sa, ka (duba Al-Tahdheeb 2/117) , Tāreekhu Baghdād 8/215-216), Siyar ta Al-Imām Al-Dhahabiy 13/110) , (12/79) .

Shaikh Jamāl har wa yau a karkashin wannan fatawa yake cewa:

(٢٤) هذه كتب شيخ الإسلام ابن تيمية أكبر برهان في عدم ذكر محاسن المبتدعة حين ذكرهم ببدعتهم؛ فهي مليئة بالردود والنقد: فقد رد على أهل المنطق والكلام، وردّ على الجهمية والمعتزلة والأشاعرة، ولم نجده ذكر شيئا من محاسنهم،
Yace:
(24) ga kuma littafan Shaikhul Islami Ibnu Taimiyah nan, babban dalili ne akan rashin ambaton kyawawan ayyukan 'yan Bid'ah a yayin ambaton su da Bid'arsu; domin (littafan nasa) cike suke da raddoji da martani: domin yayi raddi ga 'yan Mantiki da Ahlu Al- kalam, kuma yayi raddi ga Jahamawa da mu'tazilawa da asha'irah, kuma sannan bamu taras ya ambaci wani abu na kyawawan ayyukansu ba,

وانتقد أشخاصا بعينهم: كالرد على الأخنائي والبكري وغيرهم، ولم يثن عليهم،
Yace: kuma ya kama sunayen ayyanannun mutane yayi martani gare su: kamar raddin da yayi mai suna Martani ga Al- Akhnā'iy, da kuma Martani ga Al- Bakariy, da ma wasun su, kuma bai yabe su ba,

ولا يشكّ أحد أن هؤلاء لا يخلون من محاسن ، ولكن لا يلزم ذكر المحاسن في النقد. فتأمل .
Yace: kuma babu wanda zai yi shakka cewa wa'yannan mutane suna da wasu ayyuka na alheri, sai dai (abinda ake so kowa ya gane anan shine: baya zama lazimi ambaton kyawawan ayyuka a yayin martani. Don haka ka lura!.

Yaci gaba da cewa:

قال رافع بن أشرس رحمه الله: «من عقوبة الفاسق المبتدع ألا تذكر محاسنه». شرح علل الترمذي (٣٥٣/١)
Yace: Rafi'u Bin Ashras yace: «yana daga cikin ukuba ga dan Bid'ah shine rashin ambaton kyawawan ayyukan sa».

Wannan ya isa zama hujjah akan lalacewar wannan sabuwar Bid'ah da masu kariya ga 'yan Bid'ah suka assasa ta, dukda cewa ta fantsama a kasashen Musulmi , ta hanyar wa'yanda suka tsotsa daga mashayar Al- Ikhwan Al- Muflisoon, na daga Sururiyyun Qutbiyyun, sune suke yada wannan Bid'ah babu kunya babu tsoron Allah kaji mutum yana danganta kansa ga Salafiyyah ko tafarkin ma'abota Sunnah amma yana zuzuta 'yan Bid'ah da sunan adalci, (daga cikin wa'yannan karkatattun akwai wanda al- ummah ta fitinu dashi musamman a kafar sadarwa ta Facebook, cikin wa'yanda suke rubutu da harshen Hausa suna yaudarar mutane suna jefa su cikin fikirorin Sururiyyah akwai wanda ake kira "Dr. Aliyu Muh'd Sani" dan garin Misau, wannan yana halakarwa ya zama wajibi wanda yake son tsira da kasancewa a kan turba ta magabata na kwarai ya nisance shi da ire-iren sa, domin babu fa'idar kasancewa tare dasu domin 'yan Bid'ah ne) alhalin baiyi wa manhajin magabata adalci ba da ya nuna manhajin nasu na gaskiya zalunci ne da kuma jahilci a cikin sa, shi yasa ake fama da mutane kwarai kasancewar an riga an fesa musu wannan guba cikin muhadarori da lakcoci na wa'yanda suka amintar wa addinin su garesu, sai kaji mai magana yana ikirarin Sunnah Salafiyyah kuma wai yana kambama su Sayyid Qutb ko yana basu kariya ko yana kambama lamarin su Dahiru Bauchi ko Ishaka Rabi'u, ko kaji ana ikirarin Sunnah ko Salafiyyanci kuma ana zuzuta sha'anin Bakhawarije Usama Bin Ladin ana gwarzantar dashi, ko kaga yana cewa a koma wajen malaman Bid'ah a dauki karatu a sorayen su, (kamar yadda Mal. Auwal Adam Albani Zariya -Allah ya jikan sa- yake cewa daliban Ahlu Al- Sunnah su sanya ma zukatan su ruwa su koma wajen 'yan darika su koyi fikihu) ko kaga jagororin kungiya masu ikirarin Sunnah suna kai ziyara gidajen jagororin Darika domin neman hadin kai ba don gabatar da nasiha garesu ba ko nuna rashin yarda da batan da suke akan sa ba, ko kuma lalacewa dan Bid'ah yayi lecture dan kungiya yayi ta'aliki to dama duk abu daya ne dan jumma ne ya hadu da dan jummai!! ko kuma suyi wa mutane surkulle suce a dauki alkhairi a ajiye sharri, yo ba ga irin barnar nan ba an samu mu'utazilawa acikin ma'abota wannan kungiya mai ikirarin sunnah (Izala komai kin hada amma banda Sunnah) wai kuma da rushe Bid'ah!, ita kanta kungiyar rusashiya ce saboda har za'a samu 'yan Bid'ah a cikinta masu matsayin malaman kungiyar, to meyasa magabata basu fadi irin wannan maganar tasu ba kuma basu yi irin wannan ziyara tasu ba ta rushe Sunnah da nesanta mutane daga manhajin magabata na kwarai a wajen mu'amalantar 'yan Bid'ah? Ko a wajen mai irin wannan maganar su magabatan azzalumai ne ko suma 'yan zafin kai ne da dumin kirji irin su Al-Imām Ahmad?!, ko kuma yana zargin magabatan da jahilci ne sai yanzu shi yana da ilimi ya fisu gane tafarkin nasu?! Ko kuma gidadawa ne su basu iya tafiya da zamani ba?! Duk babu ko daya kuma wa'yannan tambayoyi ne da basu da amsa, sai dai mutum yayi turjiya ya doge akan Bid'ar sa yaki komawa ga gaskiya sannan kuma yayi jafa'i ga wa'yanda suka tsaya inda magabatan suka tsaya kuma tafarkin na magabata ya wadacesu daga duk wani sabon tafarki ko wata fikirah ko hayaniya da hauragiya da sauran su, wannan manhajin na Muwazanat abin tir ne kuma abu ne na ayiwa mutum takaici akan sa ba a rinka yadawa mutane suna ji ba, abinda yake wajibi shine a kone wa'yannan kasusuwa da suke rawwaja fikirori na Bid'ah, ba alfahari za'ayi dasu ba, domin wargaje Sunnah ne da kuma daurewa Bid'ah da ma'abotan ta gindi ne.

Allah ya kiyaye mu daga aukawa cikin Bid'ah ta boye da ta sarari.

Kai raba ni da bonono rufin kofa da barawo!

أمين ثالث يعقوب
17 / 08 / 1441
11 / 04 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!