RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (02)
(BQS) =
(I) Banna'iyyah
(II) Qutbiyyah
(III) Sururiyyah
Yana da kyau muyi bayani a kan wa'yannan sunaye domin idan mai karatu yaci karo dasu ko daya daga cikin su ya san me karatun yake nufi, kuma ina aka dosa, domin idan yazo rufe kofar gidan sa ya haska da kyau kada ayi tsautsayi ya rufe kofa da barawo! In ma da can ya rufe to ba aibi bane idan ya gane shi ya karya mai lago domin ya samu sauki wurin fidda tsohon maciji daga garkar gidan sa!!
A cikin littafi mai suna "المورد العذب الزلال" shafin sa na dari da tamanin da takwas (188) Shaikh Ahmad Bin Yahya Al- Najmiy (ya rasu ranar laraba ashirin ga watan Rajab shekara ta alif da dari hudu da ashirin da tara hijriyyah 20 / 07 / 1429, shekarar sa goma sha biyu kenan da rasuwa ) -Allah ya jikan sa- yana cewa:
ومن ولائد الإخوانية: السرورية والقطبيون، وهما فرقتان أو حزبان انفصلتا من الإخوانيين، فالسرورية تنسب إلى محمد سرور بن نايف زين العابدين الذي هو الآن مقيم في مدينة لندن...
Yace: kuma daga cikin kyankyasar Ikhwaniyyah akwai: Sururiyyah da Qutbiyyun, kuma rassa ne ko kungiyoyi ne wa'yanda suka cirata daga Ikhwaniyawa, ita Sururiyyah ana jingina ta ne zuwa ga Muhammad Surur bin Nayef Zainu Al- 'Ābidēēn wanda a yanzu haka yana zaune a birnin Landan..
Haka kuma yana cewa a shafi na dari da tis'in da takwas (198) :
أما القطبيون فهم قوم درسوا كتب سيد قطب، وتابعوه في كل ما قاله واعتقده، بل وعظموه كل التعظيم مما جعلهم يتخذون كل ما قاله في كتبه حقا وصوابا وإن خالف الأدلة وباين مذهب السلف...
Amma kaga Qutbiyyun sune mutanen da suka karanci littafan Sayyid Qutb, kuma suka bishi a cikin dukkan abin da yace kuma ya kudurta shi, bal ma sun girmama shi matukar girmamawa ta yadda hakan ya sanya su suna karben dukkan abin da ya fada cikin littafan sa a matsayin gaskiya da dai-dai, ko da ya saba ma dalilai, ya rabe daga tafarkin magabata (na kwarai)...
Shaikh 'Abdulsalām Bin Sālim Al- Suhaimiy -Allah ya kiyaye shi yana cewa a cikin littafin sa mai suna "فكر التكفير قديما وحديثا وتبرئة أتباع مذهب السلف من الغلو والفكر المنحرف" a shafin sa na tis'in da daya (91) :
البنائية: نسبة لمؤسس الجماعة حسن البنا
Banna'iyyah jinginuwa ce zuwa ga wanda ya assasa kungiyar (sunan shi) Hassan Al- Banna.
Binciken mu zai kasance ne a kan Sururiyyah wacce Muhammad Surur ya fitar da samfurin ta, in sha Allahu a kan ta zamu tattauna ba wai saboda magana a kan shauran rassan guda biyu baya da mahimmanci bane, a'a saboda ma'abotan Sururiyyah sune suka fi addabar 'yan uwan mu musulmai masu iya karanta rubutu da harshen Hausa, da masu sauraren harshen da fahimtar sa, musamman ma masu jingina kawunan su ga Salafiyyah, kasancewar sune hadafi na farko ga 'yan Sururiyyah domin suyi musu kwanton bauna su sanya su a shekar su kafin su farga bakar macijiya ta kyankyashe su alhalin basu da masaniya.
- Muhammad Surur Bin Nayef Zainu Al- 'Ābidēēn haifaffen dan kasar Syria ne, kuma ya shiga kasar Saudiyyah ya zauna a cikin ta na tsawon shekaru takwas (8) a Hā'il sai Al- Ah‘sā' , yayi karatu a kwalejin ilimi dake Buraidah, kuma ya zauna a Birtaniya daga nan sai ya koma Qatar yayi zaman sa, a nan Allah ya karbi rayuwar sa a sha daya ga watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da goma sha shida miladiyyah (11 / 11 / 2016).
Wannan talikin shine wanda yazo wa kungiyar Ikhwan da wani sauyi, ta yadda yayi makil da cikin sa da fikirorin 'yan Ikhwan da wani uslubi daban wanda yafi uslubin Ikhwan hadari kuma masifar sa ta dara ta Ikhwan din asali, ta yadda shi yake boye Manhajin Ikhwan tare da bayyana riga ta ma'abota Sunnah, ya zama mai fuska biyu, Ma'abocin Sunnah a fili kuma a lokaci daya Ba'Ikhwaniye a boye!
- Idan ka fahimci haka; to wannan Manhajin da ake kira "Sururiyyah" shine Manhajin da Muhammad Surur ya kyankyashe, ma'ana nasa sanfarin ne sabo dal na Ikhwaniyyah, ya sanya 'yar ciki ta Ikhwan ya lullube ta da malun-malun ta Sunnah .
- Sai yaci gaba da fesa Manhajin Ikhwan a karkashin wannan malun-malun din, har sai da ya tarbiyyantar da wani adadi na dalibai, wa'yanda a farkon lamari basu kai ko ina ba, musamman ma a wannan lokaci akwai manyan Malaman Sunnah kuma jagorori hudu na da'awar Sunnah na wannan zamanin su Shaikh Abdulazeez Bin Baz, Muhammad Bin Sāleh Al- 'Uthaymeen, Muhammad Nāsir Al- Albāni, Muqbil Bin Hādiy Al- Wādi'iy -Allah ya jikan su . A kan haka; basu iya daga kawunan su ba a wannan lokacin kuma basu iya kira da taken su na musamman ba basu kuma iya kira zuwa ga fikirorin su da karfi kuma a bayyane ba, da ace wani yayi yunkurin hakan to da Malaman sunyi masa raddi, kuma da fikirar sa da maganar sa bata samu wani tasiri mai girma ba.
- Sai suka bi tafarkin makirci da ha'inci sai halin su yake cewa ga daliban su "ku dau ilimi daga Malamai amma jagorancin ku yana hannun wa'yanda suka tarbiyyantu ne a hannun kungiyar Ikhwan" , sai suka yi kokarin fesa shubuhohi a cikin zukatan daliban ilimi domin su gwada fifiko tsakanin su da malamai, sai suka zare yardar su ga Malamai: "Malaman ku masana ne a kan Fiqhu da Hadisi, mu kuma masana ne gogaggu a kan fahimtar siyasar zamani, su wa'yancan masana ne a kan haila da jinin biki, mu kuma mune muka fi kwarewa a kan halayen mutane" . Sai aka samu irin wannan nau'in na matasa wa'yanda sun samu tarbiyyah a karkashin malamai amma kuma an dora su ne ana basu fuskantarwa daga wasu boyayyun 'yan Ikhwan -Kuma malamai sun barranta daga gare su- sai kyankyasar 'yan Ikhwan suka tashi a haka, kuma sune 'yan Sururiyyah, sai suka tashi a wannan yanayin, sai suka girma a idanuwan mutane ana musu kallon masu da'awa ne zuwa ga Sunnah, sai aka rudi da yawa daga cikin gama-gari, sai suka karkace daga mikakken tafarki.
- Sai ya kasance abin da ake jira a wannan lokacin shine "Malamai zasu mutu kuma mune zamu gaje su" kuma ilai kuwa, bayan tafiyar wasu shekaru, sai abin da bama iya guje masa yazo, sai aka jarabce mu da mutuwar wasu Malamai, kuma mutuwar tasu sai ta kasance daya na bin daya, a cikin tagwayen shekaru, sai ma'abota wannan Manhajin mai lullube da guba suka daga kawunan su, kuma suka sanya guba a hankulan mabiyan su, suka samu karkatar zukatan gama-gari zuwa gare su.
- Sai masu da'awar Sururiyyah suka samu damar fesa da'awar su cikin masallatai da tarurruka, kuma muryar su ta shahara ta mabanbanta kafofin sadarwa, suna masu tabbatar da ginshikan Ikhwananci da sunaye da lakubba masu dauke da sunan Sunnah a kan tafarkin Qutbiyyah Banna'iyyah (kamar yadda Muhammad Al- 'Areefiy -Allah ya shirye shi- yayi tawilin Hadisin Annabi da yake cewa: "اسمع وأطع وإن جلد ظهرك وأخذ مالك" ma'ana: ka saurara (ma shugaba) kuma kayi masa biyayya ko da an daki bayan ka, ko an karbe dukiyar ka" sai yayi tawilin hadisin da cewa idan shugaba yayi dare-dare a kan hakkin wani ayyanannen mutum ne ba idan ya zalunci daukacin talakawan sa bane! Ga maganar tasa da kuma raddin Shaikh Sāleh Al- Fauzān ga mummunan tawilin nasa! : ( https://youtu.be/JvGiBGZ05UQ )
- Sa'annan suka yi amfani da jagororin addini kamar su Ibnu Taimiyyah da Ibnu Al- Qayyim, sai suka rinka gutsure maganganun su iya inda suke ganin zai yi hidima ga Manhajin su, haka kuma suka riki ambaton Malaman Sunnah kamar Ibnu Baz, Albani, Ibnu 'Uthaymeen -Allah ya jikan su- cikin darussan su da muhadarorin su da makalolin su, suka riki ambaton wa'yannan Malaman Sunnah din a matsayin wata hanya wacce zasu kimsa mutane i zuwa tafarkin su na Ikhwan, saboda cakuda lamurra ga daluban ilimi masu tasowa wanda hakan al'ada ce da suka gaje ta daga su ma wa'yanda suka yaudare su a farko, sannan kuma don samar da adadi mai yawa na magoya bayan su cikin gama-garin mutane, abu mafi mahimmanci a wajen su shine samun mabiya masu yawa don cimma burin su na hadin kai da suke raya wa da fatar bakin su! Sai suka zama kamar yadda ake cewa: "asalin takarda ta Sunnah ce amma hashiya Ikhwaniyyah" sai mutane suka rudu dasu, masu wawan tunani suka biye musu, masu raunin basira suka biye musu da gaugawa, suna masu zaton cewa Sururiyyah ita ce Salafiyya ta gaskiya !
Raba ni da bonono rufin kofa da barawo!!
أمين ثالث يعقوب
10 / 08 / 1441
04 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق