RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (05)
MANYA MANYAN GINSHIKAN DA MANHAJIN SURURIYYAH YA GINU A KAN SU
Manhajin Sururiyyah ya ginu ne a kan manyan ginshikai guda uku (3) wa'yanda shauran bala'o'in suke resantuwa daga wa'yannan ginshikan, kana suke hidimtawa don tabbatar dasu, ginshikan kuma sune:
♦ TAUHIDIN HAKIMIYYAH — (Ma'ana: Tauhidin da yake kunshe da tabbatar da hukunci ga Allah shi kadai)
- 'Yan Sururiyyah suna bayar da mahimmanci wajen tabbatar da wannan Tauhidin Hakimiyyar kuma suna sanya shi ya zama wani kaso ne mai zaman kan shi daga karkasuwar Tauheedi, ma'ana a wajen su Tauhidi ya kasu kashi hudu, kamar yadda akwai Tauhidin Ibādah da Tauhidin Rububiyyah (ayyukan Allah) da Tauhidin Sunayen Allah da siffofin sa, to sai suka kara wannan ya zama kashi na hudu, bal suna daukar shi a matsayin shine mafi mahimmanci a cikin karkasuwar Tauheedi din, wanda kuma Malaman Sunnah sunyi cin gyara a kan wannan aika-aikar tasu, kuma suka bayyanar da cewa ita Hakimiyyah tana cikin Tauhidin Ibādah ne bata fita daga gare shi ba, kuma ba wani kaso ne mai zaman kansa ba, balle har ya zama shine mafi mahimmanci a kan Tauheedin kadaita Allah da bauta . kamar yadda Abu Ishāq Al- Huwainiy daya daga cikin Manyan Malaman 'yan Sururiyyah kenan -Allah ya shiryar dashi- yake tabbatar da wannan kaso na Tauhidin Hakimiyyah din , zaka iya samun maganar sa a wannan link din: ( https://youtu.be/2eV3ngCoptE )....
kuma wannan ci gaba ne ga 'Aqeedar Sayyid Qutb, daga cikin maganganun sa a kan Hakimiyyah akwai:
والذين لا يفردون الله بالحاكمية في أي زمان وفي أي مكان هم مشركون، لا يخرجهم من هذا الشرك أن يكون اعتقادهم أن لا إله إلا الله مجرد اعتقاد .
(في ظلال القرآن ـ 2/1492- دار الشروق).
Kuma wa'yanda basa kadaita Allah da hakimiyyah (hukunci) a cikin kowanne zamani, a kowane wuri mushrikai ne, kudurtawar su cewa babu abin bauta da cancanta sai Allah bata fitar dasu daga wannan shirkar, zallar kudrtawa .
Wanda a wajen ma'abota Sunnah yin hukunci da abin da Allah bai saukar ba a karon farko ba kafirci bane wanda yake fitarwa daga Musulunci, sai idan wanda yayi wannan hukuncin yana mai kudurta cewa ya halasta yayi nasa hukuncin, ko kuma da hukuncin sa da na Allah dai-dai ne, ko kuma hukuncin sa yafi hukuncin Allah, sannan ma'abota Sunnah suna rarrabewa tsakanin hukuncin aiki da kuma wanda ya aikata aikin, ba kowane lokaci bane hukuncin aiki yake fadawa a kan wanda yayi aikin ba, idan Allah yaso zamuyi bayani a kan haka a gabar da ta dace.
Shaikh Rabee'u Bin Hādiy Al- Madkhaliy -Allah ya kiyaye shi- yana mai cin gyara ga wannan magana ta Sayyid Qutb yake cewa:
إن النجاشي كان إسلامه مجرد اعتقاد أن لا إله إلا الله؛ أي: لا معبود بحق إلا الله، فلم يطبق الحاكمية في المعاملات، ولا [الأعياد]، ولا التقاليد، ولا الأزياء، ولا النظام في دولته بالحبشة، ومع ذلك صلّى عليه النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه، أفرأيت لو أنه طبق الحاكمية [فيما ذكرنا]، ولم يؤمن بعقيدة التوحيد، أيعدّ مؤمناً؟ ). (أضواء على عقيدة سيد قطب وفكره ـ ص80- عام 1414).
Ma'ana:
Lallai Al- Najjāshi musuluncin sa zallan kudurtawa ne ga Aqeedar La ilaha illallāh; ma'ana: babu abin bauta da cancanta sai Allah, shi bai kamanta hakimiyyah ba a cikin mu'amaloli ne, ko a cikin bukukuwa, ko a cikin al'adu, ko a cikin tufafi, ko a cikin tsarin daular sa a Habasha, amma tare da haka Annabi Sallallāhu 'alayhi wasallama yayi masa salla shi da Sahabban sa a lokacin da ya mutu, shin kana ganin da ace ya kamanta hakimiyyah a cikin abin da muka ambata amma kuma sai bai yi imani da Aqeedar kadaita Allah da bauta ba, shin a hakan za'a lissafa shi cikin masu imani?
Amsa ita ce: a'a! Allah ya saka ma Shaikh Rabee' da alkhairi.
Haka ma Shaikh Sāleh Al- Fauzān -Allah ya kiyaye shi- a cikin "سلسلة شرح الرسائل" shafi na dari da talatin da biyu (132) cikin Sharhin risalar "تفسير كلمة التوحيد" wallafar Shaikh Muhammad Bin 'Abdilwahhāb -Allah ya jikan sa- yana bayanin karkasuwar mutane a kan ma'anar kalmar "La ilaha illallāh" da martani gare su yake cewa:
٤ - تفسير الحزبيين والإخوانيين اليوم:
يقولون: (لا إله إلا الله) أي: لا حاكمية إلا لله، والحاكمية كما يسمونها، جزء من معنى لا إله إلا الله؛ لأن معناها شامل لكل أنواع العبادات.
فنقول لهم: وأين بقية العبادات، أين الركوع والسجود والذبح والنذر، وبقية العبادات؟
Ma'ana:
4 - FASSARAR MASU KUNGIYANCI DA 'YAN IKHWAN A YAU:
Suna cewa: (La ilaha illallāh) ma'anar ta: babu hukunci sai ga Allah, kuma ita hakimiyyah kamar yadda suka sanya mata suna, ita wani yanki ne daga ma'anar babu abin bauta da cancanta sai Allah; domin ma'anar ta(ma'ana La ilaha illallāh) ta kewaye dukkan nau'ukan ibada.
Sai muce dasu: to ina shauran ibadojin? Ina ruku'u? Ina Sujada? Ina yanka? Ina bakance(alwashi)? da shauran nau'ukan ibadar?
هل العبادة هي الحاكمية فقط، إذا كان معناها عندكم الحاكمية فقط؟
Shin bautar Allah ita ce kadai hakimiyyah? Idan ya kasance ku a wajen ku ma'anar ta ita ce hakimiyyah kadai
وأين ما تنفيه من أنواع الشرك؟ يا سبحان الله! ينبغي التنبه لهذه الأمور؛ لأن هذه كلمة عظيمة، هي المنجية من النار لمن حققها، وكل الدين ينبني عليها من أوله إلى آخره، ودعوة الرسل والكتب المنزلة كلها مبنية على هذه الكلمة". اهـ
الشيخ صالح الفوزان -حفظه الله تعالى- (سلسلة شرح الرسائل ص ١٣٢).
To ina abin da (kalmar shahada) take korewa na nau'ukan shirkoki? Tsarki ya tabbata ga Allah! Ya kamata a fadaku ga wa'yannan lamurran; domin wannan kalmar mai girma ce, ita ce mai tseratarwa daga wuta ga wanda ya tabbatar da ita, kuma addini ga baki dayan sa yana ginuwa ne a kan ta, tun daga farkon sa har zuwa karshen sa, kuma da'awar Manzanni da littafan da Allah ya saukar dukkan su sun ginu ne a kan wannan kalmar!
A takaice wa'yannan raddojin guda biyu sun wadatar ga mai neman gaskiya in sha Allahu.
♦ CEWA MUTANE GA BAKI DAYA SUNA KAN JAHILIYYAH — (Ma'ana halin da duniya ta kasance kafin zuwan Musulunci) .
- A wajen 'yan Sururiyyah dukkan mutane sun koma 'yan jahiliyyah, bal wasu daga cikin su suna bayyana cewa mutane ga baki daya kaf din su sun koma riddaddu, kamar yadda bayani ya gabata cewa ita Sururiyyah gwamutsatsen tafarki ne wanda yake bayyanar da launin Sunnah amma a hakika Ikhwaniyyanci ne a lullube, kafirta jama'a da cewa duk duniya anyi ridda sun gaje shi ne daga Sayyid Qutb, wanda bayani ya gabata cewa 'yan Sururiyyah sun tarbiyyantu daga littafan Sayyid Qutb, yana cewa a cikin "في ظلال القرآن" :
البشرية عادت إلى الجاهلية، وارتدّت عن لا إله إلا الله" .
(في ظلال القرآن ـ 2/1057- دار الشروق)
Mutane ga baki daya sun koma jahiliyyah, kuma sun yi ridda daga La ilaha Illallāh!
Kuma yana cewa:
إنه ليس على وجه الأرض اليوم دولة مسلمة ولا مجتمع مسلم؛ قاعدة التعامل فيه هي شريعة الله والفقه الإسلامي). (في ظلال القرآن ـ 4/4122- دار الشروق).
Lallai babu wata daula musulma a ban kasa a yanzu, haka kuma babu wani mujtama' musulmi wacce ka'idar mu'amala a cikin ta ita ce sharee'ar Allah da fikihun musulunci.
Haba Sayyid Qutb! Baka tausaya ma kanka ba, yanzu ko Saudiyyah iya kokarin ta na kamanta Sharee'ar Allah da kiyaye dokokin sa da jagorancin mutane da littafin Allah da Sunnar Manzon Allah, da bayyana sha'irori na Musulunci, amma ka runtse ido kace babu daula ko kwaya daya musulma a doron kasa?!
Shi yasa a lokacin da Abubakar Shekau yace "Saudiyyatu Al- 'Arabiyyah ma ba Islamiyyah bace, 'yan Ālu Sa'ud ne" , banyi mamaki ba, saboda babu wani dan ta'adda bakhawarije a doron kasa cikin masu kungiyoyin bid'ah na jahadi face almajiran Sayyid Qutb ne, ana tarbiyyantar dasu a kan littafan Sayyid Qutb .
Haka nan Sayyid Qutb ya bayyana ta'addancin sa wanda 'yan ta'adda suna alfahari dashi yake cewa a cikin "في ظلال القرآن" :
"إن المسلمين اليوم لا يجاهدون، ذلك أن المسلمين اليوم لا يوجدون، إن قضية وجود الإسلام ووجود المسلمين هي التي تحتاج اليوم إلى علاج". (في ظلال القرآن 3/1634)
Yake cewa:
Lallai musulmai a yau basa jahadi, kuma hakan ya faru ne domin a yau babu musulmai, lallai kadiyyar samar da musulunci da musulmai ita ce yau take bukatar a magance ta .
To Sayyid Qutb fa bai taba yin jahadi ba har ya mutu, kuma yana cewa babu musulmai a bayan kasa, wannan batan basira da me yayi kama?! Kuma kunji abinda yasa yace ba musulmai a duniya shine rashin jahadi, shin yanzu masu karantar da littafan Sayyid Qutb sunga natijar samuwar kungiyoyin ta'addanci da sunan Jahadi yanzu sun samu natsuwa a kan cewa akwai musulmai tunda ga 'yan uwan su na cikin daji suna tada zaune tsaye ko?!
Kuma yana cewa a cikin "العدالة الإجتماعية" :
ونحن نعلم أن الحياة الإسلامية على هذا النحو قد توقّفت منذ فترة طويلة في جميع أنحاء الأرض، وأن وجود الإسلام ذاته ـ مِنْ ثَمّ ـ قد توقّف كذلك). (العدالة الاجتماعية ـ ص185- دار الشروق 1415).
Ma'ana:
Kuma mu muna sane da cewa lallai rayuwa ta musulunci a irin wannan yanayin ta riga ta dakata tun wani lokaci mai tsawo a cikin dukkan sassan duniya, kuma lallai samuwar musulunci a kankin kan sa tun daga wancan lokacin ita ma ta dakata .
Haka nan barnar sa ta kai ga yana cewa:
البشرية بجملتها بما فيها أولئك الذين يرددون على المآذن في مشارق الأرض ومغاربها كلمات لا إله إلا الله بلا مدلول ولا واقع، وهؤلاء أثقل إثماً وأشد عذاباً يوم القيامة، لأنهم ارتدّوا إلى عبادة العباد بعدما تبين لهم الهدي، ومن بعد أن كانوا في دين الله). (في ظلال القرآن ـ 2/1057- دار الشروق).
Yake cewa:
Mutane ga baki dayan su tare da wa'yanda suke cikin su na daga masu maimaita kiraye-kirayen Sallah (yana nufin ladanai) a gabashin duniya da yammacin ta, suna maimaita kalmar La ilaha illallāh, ba tare da abin da take nufi ba, ba tare da waki'i (yana gaskata su) ba, kuma wa'yannan (yana nufin ladanai) zunubin su yafi nauyi, kuma azabar su tafi tsanani a ranar Al- Qiyamah, domin sunyi ridda zuwa bautar bayi, bayan kuma gaskiya ta bayyana gare su, bayan kuma da can sun kasance a cikin addinin Allah!
A takaice; wannan ya nuna mana mafarin kafurta mutane ga baki daya ya samo asali ne daga Sayyid Qutb wanda 'yan Sururiyyah suka tsotsa daga mabubbugar sa.
♦ JIBINTAR 'YAN KUNGIYAR SU DA BARRANTA DAGA WA'YANDA BA SU BA
- Suna jibintar wanda yake tare dasu a kungiyar su, da wanda yake jinginuwa zuwa gare su, kuma suna barranta daga duk wanda yake musu tarar aradu da kara (yake musu martani yana bayyana tsiraicin su da ilimi) kamar yadda halin dukkanin kungiyoyin bata yake, wannan a fili yake baya bukatar wani misali, ko da wannan mutumin ya kasance cikin manya-manyan ma'abota ilimi ne!
Mu'amalar su ga Malamai wa'yanda basa kan tafarkin su ba boyayya bace, suna jifan su da cewa Malaman fada ne, dakikai ne basu fahimci siyasar zamanin su ba, ilimin su bai wuce bayanan jinin mata ba, da shauran maganganu na raini da rashin albarka kamar yadda bayani ya gabata .
Kai raba ni da bonono nufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
12 / 08 / 1441
06 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق