RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (09)



FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (04)

(iv) Suna kore ingancin jagoranci na yanki-yanki, da daukar jagoranci ya takaita ne ga shugabanci mafi kololuwa kawai, kuma basa ganin wajabcin biyayya ga shuwagabanni musulmai da suke da shugabanci na yankuna .

Alhalin Annabi Sallallāhu 'alayhi wasallam yana cewa "koda bawa ne ya karbi jagorancin ku" . ma'ana ku saurare shi kuma kuyi masa biyayya, kuma ya kasance ya aika wasu daga cikin Sahabban sa zuwa wasu wurare kamar yadda ya aiki Mu'adh Bin Jabal zuwa Yemen kuma yace dashi ya kiraye su zuwa ga kadaita Allah da bauta zuwa shauran ababen da ya aike shi wanda a ciki ya kunshi ya karbi zakka a hannayen mawadatan su kuma ya bayar da ita zuwa talakawa daga cikin su, haka ya nada wasu jagoranci ga tawagogin yaki wanda ya wajabta biyayya a kan su ga wa'yannan jagorori matukar ba akan sabon Allah bane, haka kuma ya aiki Abu Musa Al- Ash'ariy, haka kuma ya aiki Aliyu Bin Abi Tāleb - Allah ya kara yarda a gare su- .

Haka ma Khalifofin sa sun nada gwamnoni wa'yanda suna wakiltar su a wajajen da suka nada su din, kuma wa'yanda aka nadawa suna musu biyayya da ganin wajabcin ta.

Amma a wajen 'yan Sururiyyah basa ganin wajabcin biyayya ga shugaba sai idan ya kasance mai jagorancin duk Musulmai, ba ya kasance mai jagorancin wani yanki ayyananne ba. wanda hakan ya saba ma Manhajin Annabta, daga cikin wa'yanda suka tabbatar da wannan kwamacala a cikin 'yan Sururiyyah akwai Dr. Shāfiy Al- 'Ajamiy kamar yadda zaku ji sautin sa a cikin wannan link din: (https://youtu.be/0kk2iyR8hp4) .

Kai raba ni da bonono rufin kofa da barawo!

أمين ثالث يعقوب
16 / 08 / 1441
10 / 04 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!