RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (03)
- 'Yan Sururiyyah ('yan Ikhwan mabiya bangaren Muhammad Surur) sun fita daga mataki na rauni zuwa mataki na karfi, domin mabiyan su sunyi yawa, kuma gama garin mutane suna bayan su, haka kuma shantakakku daga cikin daliban ilimi suna karfafar su (kamar yadda bayani zai zo a kan shantakewar wasu cikin daliban Nigeria da suka bi tafarkin Sururiyyah din in sha Allahu), sai halin su yake cewa: "ku fada mu kuma muna tsaye da nusarwar ku, ku tafi mu kuma muna biye daku" .
- Sai 'yan Sururiyyah suka fara sukar Malaman Sunnah a bayyane, suna jifan su da cewa "ai Malaman fada ne, kuma ai fatawoyin su suna rusunawa gwamnatoci ne, tare da kuma basu da fahimtar siyasar zamani, kuma ai wa'yannan Malaman masu sukar mu ne, 'yan ghuluwwi (wuce iyaka) ne a Jarhi da ta'deeli, masu kokari ne wajen raba mutane, basa hada kan mutane, da kuma zallan tankade da rairaye, basa hada sahun mutane... Wa'yannan irin kirkire-kirkire ne da suka dinga yayatawa domin su zubar da kimar malamai don su samu wuri, su samu damar jagorancin mutane .
- Lokacin da suka fi samun karfi wajen bayyanuwar su kuwa da kuma lokaci mafi bayyanarwa ga halayen su shine lokutan fitina, don haka sun samu karfin bayyanar da kansu a lokacin yakin Khaleej (Gulf war) a shekarar turawa alif da dari tara da tis'in da daya (1991), haka kuma har wa yau an ga munin jagorancin su a cikin tabbatar da bore da juyin juya hali na kasashen larabawa, suna masu wage hakoran su, suna bayyanar da manhajin su, suna masu cin moriyar fitina suna cakuda lamurra ga mabiyan su kuma suna suka ga malaman su da shuwagabannin su .
- Kuma mai bada shaida daga cikin iyalan su ma yayi shaida a kan su, wato Yusuf Al- Qardhāwiy mai hudubar fitina, yake cewa game da 'yan Sururiyyah:
ومنهم السلفيون الجدد، الذين يسميهم بعض الناس (السروريين) وهم الذين اهتموا للجانب السياسي مع الجانب العقدي، ونقد الأوضاع العامة، المحلية والدولية، وكان لهم موقفهم من دخول الأمريكان إلى المنطقة في حرب الخليج، وفيهم علماء ودعاة لهم وزنهم مثل المشايخ فهد سلمان العودة، وسفر الحوالي، وعايض القرني". (أمتنا بين قرنين ٧٤).
Yake cewa:
"daga cikin su akwai sababbun salafawa, wa'yanda wasu mutane suke kiran su 'yan Sururiyyah, sune wa'yanda suka himmantu da bangaren siyasa, tare da bangaren Aqeedah, da kuma cin gyara ga halaye da suka shafi kowa, na cikin gida da na kasashe, kuma suma suna da matsayar su ta musamman a kan shigar (Sojoji) Amerikawa cikin kasar (yana nufin Saudiyyah) a lokacin yakin Khaleej, kuma a cikin su akwai malamai da masu da'awa wa'yanda suna da ma'aunin su na musamman irin malamai kamar Salman Al- 'Audah, da Safar Al- Hawāliy, da 'Ā'id Al- Qarniy" .
Kaga kenan Yusuf Al- Qardhāwiy uban tafiyar Ikhwan ya saukake mana wajen bayyana wasu daga cikin 'yan Sururiyyah wa'yanda suka kasance kuma basu gushe ba 'yan gwagwarmaya ne na Ikhwan amma tare da lullubewa da 'Aqeeda, da yaudarar mutane da sunan Salafiyyanci!, kuma ya saukake mana wajen banbancewa tsakanin Salafawan gaskiya daga su din saboda yace su "Sababbin Salafawa ne" wanda kuma wannan kalmar tana nufin su din sun zo da wata irin tafiya da suke kiran ta Salafiyyah amma kuma su suna himmantuwa da siyasa wanda shi kuma duk tsufan sa yaga Malaman Salafiyyah irin su Bin Baz, Bin 'Uthaymeen, Albani, Muqbil, basu kasance suna himmantuwa da siyasa ba, abin da suka himmantu dashi shine ilimantar da mutane da bayyana musu shari'o'in addinin su, wanda hakan ya janyo musu zagi da cewa wai su basu fahimci siyasar zamanin su ba!
- A cikin wa'yannan ababe da suka faru, da kuma wa'yannan farfagandoji, sai adadi mai yawa na daliban ilimi suka shiga cikin wannan da'awa 'yar hayaniya, mai take na zakin baki, suka yi ta shiga suna narkewa cikin ta kamar yadda katifa take narkewa cikin wuta, a cikin wa'yannan matasa akwai masu son Sunnah, sai ya kasance niyyar mai kyau ce amma kuma rafkana ta mamaye su, sai suka tasirantu da Sururiyyah, har ya kasance basu da wata ragowar shakka a kan cewa Sururiyyah fa ita ce tafarkin Sunnah kuma Salafiyyanci ne wanda sahabbai ma suka kasance a kan ta da su da wa'yanda suka biyo bayan su da kyautatawa .
- Daga cikin ababen da suka kara ma abin boyuwa da cakuduwa shine 'yan Sururiyyah sai suka sanya ma kansu suna wai su Salafawa ne kuma suka bayyana hakan, sai aka samu wasu irin kungiyoyi suna da'awar Salafiyyanci a fatar baki, Salafiyyah wacce aka kayyade ta da wata siffa ko wani wuri (kamar ace wannan Salafiyyah ce ta gari kaza, ko ta makaranta kaza, ko ta Markaz kaza, wacce ta sha banban da tafarkin Malaman Sunnah, bal wani lokacin ma ma'abota wa'yannan da'awoyi suna bayyana cewa su basa tare da fahimtar dattawan Malamai su sune Malaman kansu, har wani ma yana iya bude baki yace idan ka kammala karatu ka dawo gida daga kasar Saudiyyah kazo kauyen su ya koya maka yadda zakayi da'awa a Nigeria, saboda wai a wajen su Malaman basu yi boko ba, ko basu fahimci siyasar zamanin su ba), wa'yannan da'awoyi ne wa'yanda aka kayyade su da wasu kiraye-kiraye na karya da ma'anoni na bogi, duk suna jinginuwa ga Sunnah wacce take tsafatatacciya, suna ma kansu shedar zur wai suma ma'abotan ta ne, kamar yadda ake ce:
وكل يدعي وصلا بليلى *** وليلى لا تقر لهم بذاكا
Kuma kowannen su yana da'awar hadewa da laila *** ita kuma laila bata tabbatar musu da hakan .
Kai raba ni da bonono.. Rufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
11 / 08 / 1441
05 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق