RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (07)
FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (02) .
Kamar yadda bayani ya gabata a rubutu na shida a kan fikirar 'yan Sururiyyah don karfafar ginshikin hakimiyyah ta kafirtawa a mas'alar hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar, a nan bayani zai ginu ne a kan fikira ta biyu wacce ita ce:
(¡¡) Wuce iyaka a kan mu'amala da kafirai, ta yadda suke daukar duk wanda ya jibinci kafirai ta kowace fuska ya zama kafiri, wannan kuma a bayyane yake a Aqeedar Sururiyyun kuma kudurin nasu ya bayyana a fili lokacin yakin Khaleej da kasar Saudiyyah ta nemi taimakon sojin Amurka a kan tunkude ta'addancin Saddam, daga cikin wa'yanda suka fito suka bayyana wannan kudurin akwai Abdulazeez Al- Turaifee (wanda dan gidan Dr. Sani R/Lemu mai suna Abdurrahman Muhd Sani Umar yake yawan yada rubuce-rubucen sa ta kafar Facebook, wanda hakan a bayyane yake) Al- Turaifee ya bayyana hakan da bakin sa a cikin wani video nasa dake kan youtube (https://youtu.be/B6BzLeOLdHc) .
Ba za'a yi tuya a mance albasa ba! Ai wannan fikira sun gaje ta ne daga ainihin shugaban na Sururiyyah Muhammad Surur bin Nayef Zainu Al- 'Ābideen, yake bayyana bakaken maganganun sa da kuma kiyayyar sa ga gwamnatin Saudiyyah da jagororin da'awar Sunnah na wannan zamanin yake cewa a majallar Al- Sunnah (wacce Malamai suke kiran ta da majallar Bid'ah) adadi na ashirin da uku, dhul Hijjah shekara ta (1412H.) yake cewa:
وصنف آخر يأخذون ولا يخجلون ويربطون مواقفهم بمواقف ساداتهم... فإذا استعان السادات بالأمريكان انبرى العبيد إلى حشد الأدلة التي تجيز هذا العمل".
Da kuma wani kaso na daban, wa'yanda suke karbe (yana nufin tallafi daga gwamnati) kuma basa jin kunya suna kulla matsayar su zuwa ga matsayar sarakunan su... Idan sarakunan suka nemi taimakon Amurka sai bayin su tafi kacokan don tattara dalilan da suke halasta wannan aikin".
A lura da kyau, Malaman Saudiyyah irin su Shaikh Bin Bāz da Ibnu 'Uthaymeen sune wa'yanda fa Muhammad Surur yake suka da cewa su bayi ne, ma'ana: bayin dagutan shuwagabanni, kamar yadda Sayyid Qutb dai yake kiran musulman duk duniya da cewa su bayin kafirai ne, to shima irin tafarkin nasa yake bi, wannan yake kara fahintar da kai cewa har cikin masu da'awa da harshen mu na Hausa zakaji suna ambaton Sarakunan su da cewa Sarakuna ne na gargajiya da nau'ukan aibatawa mabanbanta wanda hakan yake nuni ga cewa sun tasirantu da tafarkin wannan talikin, lallai ya bace kuma ya batar!
Dangane da kuma maganganun Malamai wa'yanda suka fadi halascin neman taimakon kafirai a halin yaki idan da bukatuwa zuwa ga hakan kuwa akwai:
- Shaikh Bin Baz, yana cewa: neman taimakon kafirai a lokacin yaki idan da bukatuwar haka ya halasta (https://youtu.be/SgnpA6ltyeE)
- Shaikh Bin 'Uthaymeen yana cewa: neman taimakon kafirai a lokacin yaki idan bukatuwar haka ta taso ya halasta da sharadin idan an aminta daga sharrin su (https://youtu.be/Ps00XarzgHo) bal shi yana kore kasantuwar hakan a matsayin jibintar kafirai, wannan ma martani ne ga 'yan Sururiyyah!
- Shaikh Sāleh Al- Fauzān yana cewa: halascin neman taimakon kafirai a yayin bukata shine yafi rinjaye! (https://youtu.be/awTYeMEqLRg)
Fadakarwa mai mahimmanci:
Wata kafa ce da zamu toshe ta wacce Sururiyyun zasu iya sadadowa da bakin su na tsaka don su jefa shubuha a kwakwalen mutane, ita ce lallai Shaikh Muhammad Nāsiru Al- Deen Al- Albaniy (Allah ya jikan shi) yana da matsaya wacce ta saba ma Malaman Saudiyyah a kan neman taimakon Amurka a yakin Khaleej, kuma yana da maganganu masu kaushi a kan haka, wanda yake nuna rashin yardar sa.
To idan 'yan Sururiyyah suka kawo wannan a matsayin barrantar da Malaman su ko barrantar da matsayar Malaman su a kan wannan sai muce dasu:
1- Shaikh Muhammad Nasir Al- Albāniy Mujtahidi ne, yana tsakanin samun lada biyu idan yayi dai-dai ko samun lada daya idan bai dace ba. Shi kuma Muhammad Surur ba mujtahidi bane bal ba Malamin Sunnah bane, jagora ne dai na wata tafiya wacce ta saba wa Manhajin Annabta, saboda haka ba'a fatan Muhammad Surur yayi magana bare ma har a kirga maganganun sa cikin jerin wa'yanda suka dace da Malamai ko suka saba musu, abin da ya dace gare shi shine ya koma wajen Malamai amintattu yayi tambaya a kan ababen da suka daure masa kai ba ya koma gefe yana jifan su da cewa su bayin sarakuna ne ba.
2 - Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albāniy bai kafirta a wannan mas'alar ba, kuma bai halasta ma 'yan gwagwarmaya bore ga gwamnatin Saudiyyah ba, haka bai kaskantar da Malaman Saudiyyah ba, bal har Allah ya karbi ran sa yana ganin cewa kasar Saudiyyah daula ce ta Musulunci, kamar yadda 'yan uwan sa Malaman Sunnah suka kasance suna kallon ta har zuwa yanzu, kuma yana mai girmama Malaman Saudiyyah, sabanin 'yan Sururiyyah da dukkan 'yan Ikhwan da shauran 'yan uwan su 'yan Bid'ah na daga Khawarijawa wa'yanda suke ganin gwamnatin kafirci ce da makamanta maganganu na zalunci da jahilci .
Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albāniy -Allah ya jikan sa yana cewa kamar yadda yazo a cikin risalar Shaikh Ahmad bin Umar Bazmool -Allah ya kiyaye shi- mai suna "مراقي السعود في ثناء العلماء على حكام آل سعود" a cikin shafi na (21) :
منهجنا قائم على اتباع الكتاب والسنة، وعلى ما كان عليه سلفنا الصالح، وأعتقد أن البلاد السعودية إلى الآن لا يزال الكثير من أهل العلم فيهم على هذا المنهج".
Yake cewa:
Manhajin mu a tsaye yake kan biyayya ga Al- Qur'ani da Sunnah, kuma a kan abin da magabatan mu na kwarai suka kasance a kai, kuma ina kudurta cewa lallai kasar Saudiyyah har zuwa yanzu bai gushe ba da yawa cikin ma'abota ilimi daga cikin su suna kan wannan Manhajin".
Sabanin tafarkin Sayyid Qutb da yake ganin cewa babu daula musulma kuma yake ganin malamai da ladanai kaf din su sun koma bayi ga dagutan shuwagabanni, kuma sabanin yadda Sururiyyun suke kallon ita Saudiyyah din karan kanta da ma manyan Malaman ta, wanda a fili 'yan Sururiyyah masu tawaye ne ga shuwagabanni musulmai, kuma masu munanan kalamai ne ga Malaman Sunnah na gaskiya.
A takaice; Mun fahimci banbance-banbance dake tsakanin matsayar Shaikh Albāniy a kan neman taimakon Amurka da Saudiyyah tayi, da kuma rashin hankalin da 'yan Sururiyyah suka yi, kuma mun fahimci cewa lallai neman taimakon kafirai a irin wannan mataki baya daga cikin soyayya ko jibintar kafirai, sabanin abin da 'yan Sururiyyah suke fahimta kuma suke tabbatarwa! .
Raba ni da bonono rufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
14 / 08 / 1441
08 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق