RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (04)
- Lokaci ya ja, wasu suna ta maye gurbin na baya dasu, sai wa'yanda basu san mafarin waccan Salafiyyar ta munafinci ba (ma'ana: sururiyyah) suka gan ta, sai suka rudu da ita, kuma suka riki jagororin ta, har suka tasirantu dasu, lallai akwai banbanci kwarai tsakanin Salafawan gaskiya da kuma 'yan Sururiyyah, akwai banbanci tsakanin mutanen da suka tarbiyyantu a kan Sunnah da kwadayin kasancewa tare da gaskiya, da kuma mutanen da suka tarbiyyantu a kan ta'assubanci ga kungiya da karfafar kungiyanci .
- Akwai banbanci sosai tsakanin wa'yanda suka tarbiyyantu karkashin ilimin Al- Qur'ani da Akidar Sunnah, da kuma mutanen da suka tarbiyyantu a karkashin kissoshi da fina-finai da ababen da suke tayar da tausayi na daga wakoki (Anasheed) da suke cakude da gurnani .
- Akwai banbanci tsakanin wa'yanda suka tarbiyyantu a kan son sahabbai da koyi dasu da tafiya a kan gwadaben su, da gwadaben tabi'ai da jagorori wa'yanda suka bisu da kyautatawa, da kuma mutanen da suka tarbiyyantu a kan soyayya ga Hassan Al- Banna, da Sayyid Qutb, da Muhammad Qutb, da Al- Maududiy, da Salāhu Al- Sāwiy, da wasun su daga cikin 'yan kungiyar Ikhwan .
- Salafiyyar gaskiya tana wata nahiyar, ita ma Sururiyyah tana wata nahiyar daban, domin Salafiyyar gaskiya wani abu ne daban daga wa'yancan da'awoyin ga baki dayan su, babu wa'yanda suka san Salafiyyar gaskiya sai mutane 'yan kadan, ita Salafiyyar gaskiya ta ginu ne a kan Al- Qur'ani da Sunnah da kuma fahimtar mafi alheri acikin zamunna, a Aqeedah ne, a ilimamce ne, a aikace ne, a dabi'ance ne, ita Salafiyyar gaskiya sanin gaskiya ne da kuma tausaya ma halittu, ita Salafiyyar gaskiya zaman lafiya ce kuma tafarkin Annabi da Sahabbai ce.
- Saboda karfin da'awar Ikhwan da kuma bayyanar ta cikin kyale-kyalen yaudara da sunan Salafiyyanci da Sunniyanci, da kuma fakewa a bayan manyan Malaman Sunnah, sai wani sashe na wa'yanda suke jinginuwa zuwa ga ilimi suka tasirantu da ita, ina ga kuma gama-garin mutane, haka kuma da abin da suke bayyanawa na taken kungiyanci wanda suka cakuda shi da Ikhwaniyyanci da Sururiyyanci wanda aka sanya mata rigar Salaf da Sunnah, sai ya kasance mutane sun karkata zuwa gare su cikin adadi mai yawa, kuma bamu da dabara bamu da karfi sai ga Allah .
- Sai aka kafe ginshikan Ikwaniyanci, da maganganun Qutbiyyanci, da tsare-tsaren Banna'iyyanci ta hanyar tashar boyayyar Sururiyyah wacce ta kafu a kan wasu ginshikai, da wasu fikirori da uslubai da wani sashe na Sunnah ya boyu ta dalilan su, kuma Al- Ummah ta rarraba ta dalilan su, haka kuma abokan gaba suka yi dare-dare a kan Musulmai .
- Saboda haka ne babu makawa sai an yaye tsiraicin wannan gwagwarmaya ta da'awar Salafiyyanci wanda yake boye da Ikwaniyanci, domin Sururiyyah tana cikin mafi hadari da mafi boyuwar matafiyoyi na fikirori Ikhwaniyyah, kuma hakan zai kasance ne ta hanyar takaitattun fadakarwa da wayar da kai game da ababen da 'yan Sururiyyah suke kafa da'awar su a kan su, domin tabbatar da Aqeedu da ginshikai wa'yanda suka gina Mahajin su a kai, da kuma fikirorin su, kuma suka boye cikin su da uslubai wa'yanda a hakikani suna daga cikin mabubbugar kungiyanci na Ikwaniyyah, ta hanyar sake-saken layi da zasu biyo baya .
Kai raba ni da bonono rufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
11 / 08 / 1441
05 / 04 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق