المشاركات

عرض المشاركات من 2020

HIRATA DA DR. KABIR LAWAL GARBA ASSALAFY KADUNA HAFIZAHULLAH AKAN DA'AWAR SALAFIYYAH (A-1) 📼

 HIRATA DA DR. KABIR LAWAL GARBA ASSALAFY KADUNA HAFIZAHULLAH AKAN DA'AWAR SALAFIYYAH  (A-1) 📼 MAI TAMBAYA ___ Adam Sanusi Adam (Abu Uthaymeen) Assalafy  Kano 🎙️ MAI BADA AMSA ___ Sheikh Dr. Kabir Lawan Garba ( Abu Muhaisin) Assalafy Kaduna 🎤 MAI RUBUTAWA ___ Tasiu Salisu Assalafy Kano 🖋️ -------------------------------------------------------------------------- ADAM SANUSI ASSALAFY :- -------------------------------------------- Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulillah,  Muhammadin wa'alihi wasahbihi waman wala. Bayan haka Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. DR. KABIR LAWAL  ASSALAFY :- -------------------------------------------------- Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu. ADAM SANUSI ASSALAFY :- -------------------------------------------- Muna godiya ga Allah madaukakin sarki wanda yakaddara haduwarmu adaidai wannan lokaci, safiyar yau 18 gawatan zulhijja shekara ta 1441 hijirar Manzo (S.A.W) wanda yayi daidai da 8 gawatan ogost ...

DAGA CIKIN YABON MALAMAI GA SHAIKH RABEE'U BNU HADIY AL- MADLHALIY

صورة
 DAGA CIKIN YABON MALAMAI GA SHAIKH RABEE'U BNU HADIY AL- MADKHALIY (ALLAH YA KIYAYE SHI)  Ina son Rabee'u da nahju Al- Rabee'i Duk mai kin Rabee'u kunna mai wake na yaji Thanā'in a'immah ga Shaikhu Rabee'u la'alla ya zauna yaji Rabee'u bnu Hādiy zakkāhu bnu Bāzin Dama Shaikhuna Al- Albani Fauzan na yabon sa kamar yadda kowa yasan shi a 'yan zamani Albani yace wanda yai masa suka  Wannan baida hujjah kuji Yace ai fa ilmu yana kan Rabee'u  zan sa muku sautin kuji Yace Rabbana shiryatar ko ka karya Bayan masu suka ga Shaikh Madkhaliy Thana'in Uthaymeenu kan Al- Rabee'u yace Ku saurari kasusuwan Shehi Rabee' Al- Madkhaliy Yace kar a saurari Salman da Saffar suna tada zaune tsaye Sururiyyatun nahjuhum malamai ne na Takfir kuji kai tsaye Ni bani da nawa yabon kan Rabee'u don anyi yabon tun tuni Ina ma ina ma nake saka kaina cikin masu kutse a harkar da manya sukai ittifaki a kai tun tuni Na bayar da hujjah nayi nawa wajje ina gaida...
صورة
RADDI GA MASU JINGINA MA WASU MALAMAI TAWAYE (01) (1) Duk wanda yace maka Al- Imamu Malik yayi khuruji ga shugaba musulmi yayi ma Al- Imamu Malik kirkira . yana daga cikin dabi'un munharifai jingina tafarkin su da magabata domin samar masa da gindin zama. (2) Abin da aka ruwaito daga Al- Imamu Ahmad kuma shi ne hani daga tawaye, bal Malaman Fiqhu na Baghdad sun yi gangami domin su labarta masa kuma su nemi shawarar sa a kan cewa zasu yi tawaye ga Al- Wathiq, wanda yake azzalumin shugaba ne kuma yana da kafirar akidar cewa Al- Qur'ani halittar Allah ne, amma sai Al- Imamu Ahmad yace suyi hakuri, daga cikin abin da aka ruwaito daga gare shi a kan hani daga tawaye ma Al- Wathiq akwai fadin sa: "عليكم بالنكرة بقلوبكم، ولا تخلعوا يدا من طاعة، ولا تشقوا عصا المسلمين، ولا تسفكوا دماءكم ودماء المسلمين معكم، انظروا في عاقبة أمركم، واصبروا حتى يستريح بر أو يستراح من فاجر". Yace: ku rinka inkari da zukatan ku, amma karku fita daga yi masa biyayya, kuma karku fita da...
صورة
💥💥💥 *BAYANAI NA ADALCI A KAN SU :  MALAM AUWAL ALBANI ZARIA DA MALAM JAFAR ADAM -ALLAH YA JIKAN SU- TARE DA DALILAI NA MURYOYIN SU* . 💥💥💥 _*[GABOBI GUDA GOMA (10) DA SUKE NUNA CEWA WA'YANNAN MALAMAI SUNE SUKA HAIFAR DA BOKO HARAM!]*_ *MAI GABATARWA: SHAIKH ADAM ZUBAYR AL- NIGERIY (MALAM BAFFA HOTORO) ASSALAFIY -ALLAH YA DATAR DASHI- .* _*Kashi na daya :*_ https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/112 _*Kashi na biyu :*_ https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/128 _*Kashi na uku :*_ https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/133 _*Kashi na hudu :*_ https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/135 *Ayi saurare lafiya !* _*Daralmahajjatalbaydhaa taku ce domin fayyace Salafiyyar gaskiya daga tafarkokin 'yan rudu da taratsi!!*_
صورة
AN KARA BUDE DAMAR SAMUN KARATU A JAMIAR MUSULUNCI TA MADINA SAUDI ARABIYA sharudan samun admision 1- Kada Dalibi ya gaza shekara 17 Kada ya wuce 25 2- Dalibin da zai karatu da turanci zai gabatar da takardar shedar kwarewa ta turanci (Tofel) Takardu da ake bukata (1) E-passport (2) High school certificate or equivalent (3) Statement of result. (4) 2 Recommendation letters (5) Certificate of fitness Takardun da ba na larabci ba ana bukata a fassara su zuwa larabci ga wanda zai karatu da larabci  Bangarorin da zaka Iya karanta -College of Sharia . -College of Dawa and the Fundamentals of Religion. -College of the Holy Quran and Islamic Studies. -College of Hadith and Islamic Studies. -Faculty of Arabic Language. -College of Engineering . -College of Computer. -College of Science .  Wannan dama ta kunshi dauke ma dalibi dukkan wahalhalu na karatu/ wajan zama / abinci da sauransu Hanyar yin rijista https://admission.iu.edu.sa/HowToApplay.as...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (12) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (07) da (08) (vii) Fikira ta bakwai ita ce tsare-tsare na sirri da boyo da takiyya, wannan wata fikira ce da suke dasa ta a zukatan masu sauraren su wacce manufar ita wannan fikira shine burun-burun ta yadda za'a koyar dasu boye abin da suke kudurtawa daga shauran mutane gama-gari, domin cimma manufofin su na kungiyanci (hizbiyyah) da binne barna a cikin kasa, shi yasa Abdullāh 'Alwān yake cewa a cikin "العقبات" mujalladi na biyu shafi na dari biyar da tis'in da shida (2/596) , yake cewa: "حين تبتلى الحركة الإسلامية بحاكم إرهابي لا ديني متسلط يعتقل الدعاة، تكون الخطة على الشكل الآتي: ١ - الاقتصار في تبليغ الدعوة على السر... ". A lokacin da gwagwarmayar Musulunci ta jarabtu da shugaba dan ta'adda ba mai addini ba mai karfin mulki wanda yake garkame masu da'awa, to take-taken zai kasance ne a cikin yanayi kamar haka: 1 - takaituwa wajen isar ...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (11) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (06) (v) Fikira ta shida ita ce: hada mutane a kan ka'ida mai suna "قاعده المعذرة والتعاون" ma'ana: "ka'idar bayar da uzuri da taimakekeniya", ma'ana: idan dan Ikhwan yayi kowace irin barna ce to ba za'ayi martani gare shi ba, kuma ba za'a kushe shi ba, wanda hakan yana bayar da babbar gudummawa wajen lalata addini daga tushen sa, ta hanyar rufe kofar umurni da kyakyawa da hani daga mummuna wanda ya kunshi ayi cin gyara ga duk wanda ya saba, kuma a soki wanda ya cancanci suka a shar'ance, wacce kuma ita wannan ka'ida a wajen 'yan Ikhwan ka'ida ce ta zinariya, suna cin moriyar wannan ka'ida ne wajen kame baki a kan barnar wa'yanda suke tarayya dasu domin cimma hadafofin su na siyasa da kungiyanci (hizbiyyah) . Lura da hadurran dake cikin wannan la'ananniyar ka'ida ta Ikhwan wanda ya hada da kamanceceniya da wa...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (10) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (05) (vi) fikira ta biyar ita ce: tabbatar da mas'alar Al- Muwazanāt (ma'ana: yin gwaji tsakanin kyawawan ayyuka da munana) a yayin yin martani ga dan Bid'ah, ta yadda za'a ambaci kyawawan ayyukan sa da munanan a yayin yi masa raddi, wanda hakan yana kaiwa zuwa ga yin sakaki da ko in kula a kan martani ga 'yan Bid'ah da son zuciya . Shaikh Bin Baz yana martani ga wannan Manhaji na Al- Muwazanāt wanda yake lazimta yin awo tsakanin ayyukan 'yan Bid'ah yake cewa: "من أظهر المنكر أو البدعة، يحذر منه، ولا ينظر إلى حسناته، حسناته بينه وبين ربه.." Ma'ana: duk wanda ya bayyana abin ki ko Bid'ah za'a tsoratar ne daga gare shi, kuma ba za'a yi dubi zuwa kyawawan ayyukan sa ba, domin kyawawan ayyukan sa tsakanin sa ne da Ubangijin sa! Kana iya sauraren wannan magana tare da maganar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen -Allah ya ...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (09) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (04) (iv) Suna kore ingancin jagoranci na yanki-yanki, da daukar jagoranci ya takaita ne ga shugabanci mafi kololuwa kawai, kuma basa ganin wajabcin biyayya ga shuwagabanni musulmai da suke da shugabanci na yankuna . Alhalin Annabi Sallallāhu 'alayhi wasallam yana cewa "koda bawa ne ya karbi jagorancin ku" . ma'ana ku saurare shi kuma kuyi masa biyayya, kuma ya kasance ya aika wasu daga cikin Sahabban sa zuwa wasu wurare kamar yadda ya aiki Mu'adh Bin Jabal zuwa Yemen kuma yace dashi ya kiraye su zuwa ga kadaita Allah da bauta zuwa shauran ababen da ya aike shi wanda a ciki ya kunshi ya karbi zakka a hannayen mawadatan su kuma ya bayar da ita zuwa talakawa daga cikin su, haka ya nada wasu jagoranci ga tawagogin yaki wanda ya wajabta biyayya a kan su ga wa'yannan jagorori matukar ba akan sabon Allah bane, haka kuma ya aiki Abu Musa Al- Ash'ariy, haka kuma...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (08) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (03) Fikira ta gaba ita ce: (¡¡¡) Yin sakaki da raini ga abin da ya shafi tawaye ga shuwagabanni musulmai da daukar mas'alar a matsayin mas'ala ce ta sabani, kuma sabani yana da mashiga a cikin ta, manufa idan wani yana ganin halascin tawaye ga shuwagabanni wani kuma yana ganin haramcin hakan to babu wanda za'a zarga a cikin su, wanda kuma hakan sabani ne ga Manhajin Annabta, baudewa ce ga tafarkin magabata na kwarai, kuma wannan tunanin tunani ne na Bid'ah, saboda Malaman Sunnah sun yi ijma'i a kan haramcin tawaye ga shuwagabanni musulmai, bal jagororin Sunnah sun rubuta a Aqeedar ma'abota Sunnah cewa haramun ne yin tawaye ga shugaba musulmi, kuma suna kirga tawayen a matsayin tafarki ne na 'yan Bid'ah, kuma a wajen ma'abota Sunnah wannan ba mas'ala ce wacce sabani yake da mashiga a cikin ta ba. Hadisan da suka zo da umurni da biyayya ga sh...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (07) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (02) . Kamar yadda bayani ya gabata a rubutu na shida a kan fikirar 'yan Sururiyyah don karfafar ginshikin hakimiyyah ta kafirtawa a mas'alar hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar, a nan bayani zai ginu ne a kan fikira ta biyu wacce ita ce: (¡¡) Wuce iyaka a kan mu'amala da kafirai, ta yadda suke daukar duk wanda ya jibinci kafirai ta kowace fuska ya zama kafiri, wannan kuma a bayyane yake a Aqeedar Sururiyyun kuma kudurin nasu ya bayyana a fili lokacin yakin Khaleej da kasar Saudiyyah ta nemi taimakon sojin Amurka a kan tunkude ta'addancin Saddam, daga cikin wa'yanda suka fito suka bayyana wannan kudurin akwai Abdulazeez Al- Turaifee (wanda dan gidan Dr. Sani R/Lemu mai suna Abdurrahman Muhd Sani Umar yake yawan yada rubuce-rubucen sa ta kafar Facebook, wanda hakan a bayyane yake) Al- Turaifee ya bayyana hakan da bakin sa a cikin wani video nasa dake kan you...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (06) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (01) . Fitinar Sururiyyah tana da fikirori da suke karfafar wa'yancan ginshikai da ambaton su ya gabata, wa'yannan fikirori kuma sun hada da: (¡) Wuce iyaka a kan batun hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar,  kamar dai yadda Khawarijawa suka kasance, dama idan mai karatu bai mance ba mun ambata a baya cewa 'yan Ikhwan khawarijawa ne, Lallai 'yan Ikhwan sune wa'yanda suka jaddada Mazhabar Khawarij a wannan zamanin, dari bisa dari, kuma a wajen su suna ganin cewa lallai hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar kafirci ne babba kai tsaye, babu rarrabewa a kan wanda yayi wannan hukunci, sabanin tafarkin ma'abota Sunnah wanda asali shine yin hukunci da sabanin abin da Allah ya saukar babban zunubi ne ba kafirci kai tsaye ba, kamar yadda Ibnu 'Abdi Al- Barr ya hakaito ijma'i a kan haka, sannan kuma tafarkin Salafawan gaskiya (ma'abota Sunnah) tafa...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (05) MANYA MANYAN GINSHIKAN DA MANHAJIN SURURIYYAH YA GINU A KAN SU Manhajin Sururiyyah ya ginu ne a kan manyan ginshikai guda uku (3) wa'yanda shauran bala'o'in suke resantuwa daga wa'yannan ginshikan, kana suke hidimtawa don tabbatar dasu, ginshikan kuma sune: ♦ TAUHIDIN HAKIMIYYAH — (Ma'ana: Tauhidin da yake kunshe da tabbatar da hukunci ga Allah shi kadai) - 'Yan Sururiyyah suna bayar da mahimmanci wajen tabbatar da wannan Tauhidin Hakimiyyar kuma suna sanya shi ya zama wani kaso ne mai zaman kan shi daga karkasuwar Tauheedi, ma'ana a wajen su Tauhidi ya kasu kashi hudu, kamar yadda akwai Tauhidin Ibādah da Tauhidin Rububiyyah (ayyukan Allah) da Tauhidin Sunayen Allah da siffofin sa, to sai suka kara wannan ya zama kashi na hudu, bal suna daukar shi a matsayin shine mafi mahimmanci a cikin karkasuwar Tauheedi din, wanda kuma Malaman Sunnah sunyi cin gyara a kan wannan aika-aikar tasu, kuma suka bayyana...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (04) - Lokaci ya ja, wasu suna ta maye gurbin na baya dasu, sai wa'yanda basu san mafarin waccan Salafiyyar ta munafinci ba (ma'ana: sururiyyah) suka gan ta, sai suka rudu da ita, kuma suka riki jagororin ta, har suka tasirantu dasu, lallai akwai banbanci kwarai tsakanin Salafawan gaskiya da kuma 'yan Sururiyyah, akwai banbanci tsakanin mutanen da suka tarbiyyantu a kan Sunnah da kwadayin kasancewa tare da gaskiya, da kuma mutanen da suka tarbiyyantu a kan ta'assubanci ga kungiya da karfafar kungiyanci . - Akwai banbanci sosai tsakanin wa'yanda suka tarbiyyantu karkashin ilimin Al- Qur'ani da Akidar Sunnah, da kuma mutanen da suka tarbiyyantu a karkashin kissoshi da fina-finai da ababen da suke tayar da tausayi na daga wakoki (Anasheed) da suke cakude da gurnani . - Akwai banbanci tsakanin wa'yanda suka tarbiyyantu a kan son sahabbai da koyi dasu da tafiya a kan gwadaben su, da gwadaben tabi'ai da jagoro...
صورة
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (03) - 'Yan Sururiyyah ('yan Ikhwan mabiya bangaren Muhammad Surur) sun fita daga mataki na rauni zuwa mataki na karfi, domin mabiyan su sunyi yawa, kuma gama garin mutane suna bayan su, haka kuma shantakakku daga cikin daliban ilimi suna karfafar su (kamar yadda bayani zai zo a kan shantakewar wasu cikin daliban Nigeria da suka bi tafarkin Sururiyyah din in sha Allahu), sai halin su yake cewa: "ku fada mu kuma muna tsaye da nusarwar ku, ku tafi mu kuma muna biye daku" . - Sai 'yan Sururiyyah suka fara sukar Malaman Sunnah a bayyane, suna jifan su da cewa "ai Malaman fada ne, kuma ai fatawoyin su suna rusunawa gwamnatoci ne, tare da kuma basu da fahimtar siyasar zamani, kuma ai wa'yannan Malaman masu sukar mu ne, 'yan ghuluwwi (wuce  iyaka) ne a Jarhi da ta'deeli, masu kokari ne wajen raba mutane, basa hada kan mutane, da kuma zallan tankade da rairaye, basa hada sahun mutane... Wa'yannan irin k...