RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (12)
FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (07) da (08)
(vii) Fikira ta bakwai ita ce tsare-tsare na sirri da boyo da takiyya, wannan wata fikira ce da suke dasa ta a zukatan masu sauraren su wacce manufar ita wannan fikira shine burun-burun ta yadda za'a koyar dasu boye abin da suke kudurtawa daga shauran mutane gama-gari, domin cimma manufofin su na kungiyanci (hizbiyyah) da binne barna a cikin kasa, shi yasa Abdullāh 'Alwān yake cewa a cikin "العقبات" mujalladi na biyu shafi na dari biyar da tis'in da shida (2/596) , yake cewa:
"حين تبتلى الحركة الإسلامية بحاكم إرهابي لا ديني متسلط يعتقل الدعاة، تكون الخطة على الشكل الآتي:
١ - الاقتصار في تبليغ الدعوة على السر... ".
A lokacin da gwagwarmayar Musulunci ta jarabtu da shugaba dan ta'adda ba mai addini ba mai karfin mulki wanda yake garkame masu da'awa, to take-taken zai kasance ne a cikin yanayi kamar haka:
1 - takaituwa wajen isar da da'awa a kan sirrantawa ...".
GANI YA KORI JI!
Nayi halartar majalisin wani almajirin Ahmad Adam Al- Garkawiy -Allah ya shiryar dasu- na tsawon kimanin shekaru tara, a cikin garin mu, sai ya kasance idan an kai wata gaba cikin karatun littafin gwagwarmaya sai yayi umurni da a murde "loudspeakers" , kafin nan idan ya karanta wata gaba sai aji yace: "mai littafi ne ya fada ba nine na fada ba!" , da sauran maganganu da suke nuna cewa akwai tsarguwa da damuwa ace sun fito daga mutum mai da'awar bayar da tarbiyyah islamiyyah, kai daga baya ma soke "loudspeakers" din akayi ga baki daya, har sai da aka kammala wannan littafi aka sanya wani daga baya .
Abu mafi mahimmanci a nan shi ne lallai wannan fikira tasu nima naga wanda ya tabbaka ta ni ganau ne ba jiyau ba, sannan kuma babu inda za'a karantar da addini irin na magabata na kwarai mai karantarwar yaji shakkar bayyanawa a "loudspeakers" ko abu makamancin haka, bal ita da'awa irin ta Annabawa bayyana ta ake so ayi wa'yanda basu san da ita ba ma su san da ita, a haka zata yadu, wa'yanda zasu karba su karba wa'yanda zasu kyamace ta su kyamace ta a cikin asalin surar ta .
(viii) Fikira ta takwas ita ce caza zukata a kan jahadi da kwadaitarwa a kan sa ba tare da sharudda da ka'idoji ba, har hakan yana sanya sharadin izinin shugaba yana buya ga da yawa cikin mutane, da izinin iyaye a cikin jahadi na kai farmaki, sa'annan kuma hakan ya sanya masu zallar kwadayin irin wannan jahadi (na Bid'ah) suna haduwa da kungiyoyin jahadi masu kafirtawa da zubar da jini ba bisa ka'idoji na sharee'ah ba! Kamar yadda da dama daga cikin matasan Izala suka shiga kungiyar Boko Haram a farkon bayyanar ta, kamar yadda kuma da dama daga cikin almajiran Ahmad Adam Al- Garkawiy suka shiga cikin Boko Haram din kamar yadda marigayi Mal. Auwal Adam Albani Zaria ya bayar da shaidar hakan, dukda cewa a tsakanin su ana samun fikirorin da suka dace da juna a cikin su, kamar yadda muka saurari tunzurawar Mal. Auwal Adam Albani Zaria a kan Jahadi babu sharadin izinin shugaba, haka ma Mal. Ja'afar Adam Allah ya jikan su ya kuma haskaka kaburburan su, shima yana da wannan fikirar, kamar yadda yazo a cikin raddoji tare da dalilai wanda Shaikh Adam Zubair Al- Nigeriy -Allah ya datar dashi- ya gabatar cikin kasusuwa hudu (zaku same su a cikin channel din "دار المحجة" (*)
Alhali kuma Annabi Sallallāhu 'alayhi wasallama yana cewa:
"وإنما الإمام جنة، يقاتل من ورائه ويتقى به".
[البخاري ٢٧٩٧ ، مسلم ١٨٣٥].
"Kuma abin sani kadai shine shi shugaba garkuwa ne, ana yaki a bayan sa kuma ana kariya dashi".
[Bukhari 2797, Muslim 1835].
WASU DAGA CIKIN MAGANGANUN MALAMAI A KAN SHARADIN JAHADI TARE DA SHUGABA KODA NA BANZA NE!
قال الإمام أحمد - رحمه الله تعالى - في "أصول السنة" : "والغزو ماض مع الأمراء إلى يوم القيامة، البر والفاجرلا يترك، وقسمة الفيء وإقامة الحدود إلى الأئمة ماض ليس لأحد أن يطعن عليهم ولا ينازعهم".
[اللالكائي في شرح أصول الاعتقاد (٣١٦) ١٢٦/١].
Al- Imamu Ahmad -Allah ya jikan sa- yana cewa a cikin risalar sa mai suna: " Usulu Al- Sunnah" ma'ana: "Ginshikan akidun Sunnah" yake cewa:
"Kuma jahadi zai ci gaba da wanzuwa ne tare da jagorori har zuwa tashin kiyama, na kwarai din su da lalatattun su....
وقال الإمام البربهاري - رحمه الله تعالى - في "شرح السنة" :
"والغزو مع الإمام ماض وصلاة الجمعة خلفهم جائزة ويصلى بعدها ست ركعات يفصل بين كل ركعتين هكذا قال أحمد ابن حنبل"
Al- Imāmu Al- Barbahāriy -Allah ya jikan sa- shima yana cewa a cikin "Sharhu Al- Sunnah" :
"Kuma jahadi zai ci gaba ne tare da shugaba...
وقال الإمام ابن قدامة المقدسي - رحمه الله - في "لمعة الاعتقاد" : "ونرى الحجّ والجهاد ماضيان مع كلّ إمام ،برّا كان أو فاجرا، وصلاة الجمعة خلفهم جائزة"
Al- Imāmu Ibnu Qudāmah -Allah ya jikan sa- shima yana cewa:
"Kuma muna da akidar cewa aikin hajji da jahadi suna tafiya ne tare da duk wani jagora na kwarai ne koko na banza ne....
وقال الإمام ابن تيمية - رحمه الله - :
ولهذا كان من أصول أهل السنة والجماعة لزوم الجماعة وترك قتال الأئمة وترك القتال في الفتنة
[الأمر بالمعروف والنهى عن المنكر ص ٢٠]
Al- Imāmu Ibnu Taimiyyah -Allah ya jikan sa- yana cewa:
" kuma saboda haka ne ma ya kasance daga cikin ginshikan akidar ma'abota Sunnah da jama'ah lazimtar jama'ah (ma'ana: wa'yanda suke tare da shuwagabanni) da rashin yakar shuwagabanni.....
قال سفيان الثورى -رحمه الله تعالى- :
والجهاد ماض إلى يوم القيامة والصبر تحت لواء السلطان جار أم عدل
[شرح أصول الإعتقاد (٣١٤) ١٢٠/١]
Al- Imāmu Sufyān Al- Thauriy yana cewa:
"Kuma jahadi yana tafiya ne har zuwa tashin kiyama da hakuri a karkashin tutar shugaba yayi zalunci ko yayi adalci".
وقال علي بن المديني - رحمه الله تعالى - :
والغزو مع الأمراء ماض إلى يوم القيامة البر والفاجر لا يترك
[شرح أصول الإعتقاد (٣١٨) ١٣١/١]
Al- Imāmu Aliyu bin Al- Madeeniy -Allah ya jikan sa- yana cewa:
" jahadi yana tafiya ne har zuwa ranar kiyama tare da jagorori na kwaran su da lalatattun su ba'a barin shi".
وقال الإمامان أبو زرعة وأبو حاتم الرازيان - رحمهم الله تعالى - :
ونقيم فرض الجهاد والحج مع أئمة المسلمين في كل دهر وزمان ، ولا نرى الخروج على الأئمة ولا القتال في الفتنة ، ونسمع ونطيع لمن ولاه الله عز وجل أمرنا ولا ننزع يداً من طاعة ونتبع السنة والجماعة، ونجتنب الشذوذ والخلاف والفرقة . فإن الجهاد ماض منذ بعث الله عز وجل نبيه عليه الصلاة والسلام إلى قيام الساعة مع أولي الأمر من أئمة المسلمين لا يبطله شيء!
[شرح أصول الإعتقاد (٣٢١) ١٣٨/١].
Al- Imāmu Abu Zur'ah Al- Rāziy da Al- Imāmu Abu Hātim Al- Rāziy -Allah ya jikan su- suna cewa:
"Kuma muna tsaida faralin jahadi da aikin hajji tare da jagororin musulmai a cikin kowanne lokaci da kowanne zamani kuma bama da akidar tawaye ga shuwagabanni haka bama yaki cikin fitina...."
وقال الإمام أبو منصور معمر بن أحمد الأصبهاني - رحمه الله تعالى - :
وَمن السّنة الْحَج مَعَهم، وَالْجهَاد مَعَهم، وَصَلَاة الْجُمُعَةوَالْعِيدَيْنِ خلف كل بر وَفَاجِر
[الحجة في بيان المحجة للتيمي ٢٣٥/١].
Al- Imāmu Abu Mansur Ma'mar bin Ahmad Al- Asbahāniy -Allah ya jikan sa- yana cewa:
قال الحافظ ابن حجر - رحمه الله تعالى - :
أجمع الفقهاء على وجوب طاعة السلطان المتغلب، والجهاد معه، وأنّ طاعته خير من الخروج عليه، لما في ذلك من حقن الدماء، وتسكين الدهماء".
[فتح الباري ١٣/٧].
Al- Hāfidh Ibnu Hajar -Allah ya jikan sa- yana cewa:
"Malaman Fiqhu sunyi ijma'i a kan wajabcin biyayya ga shugaba wanda ya kwaci mulki da karfi, da yin jahadi tare dashi, kuma lallai yi masa biyayya yafi alheri a kan yi masa tawaye....
وقال شيخ الإسلام ابن تيمية - رحمه الله تعالى - :
ويرون -أي الطائفة المنصورة- إقامة الحج والجهاد والجمع والأعياد مع الأمراء أبرارا كانوا أو فجارا
[الواسطية ص ١٢٩]
Shaikhul Islāmi Ibnu Taimiyyah -Allah ya jikan sa yana cewa:
" Kuma su (kubutacciyar tawaga ma'ana: ma'abota Sunnah) suna da akidar cewa tsayar da faralin aikin hajji da jahadi da sallar jam'i da idoji musulmai suna yin su ne tare da shuwagabanni na kwarai ne ko lalatattu ne!
A takaice dai; abin da yake Sunnah shine yin jahadi karkashin jagorancin shuwagabanni, kuma lallai zaburarwa a kan jahadi ba tare da sharudda da ka'idoji ba wannan hanya ce ta 'yan taratsi wacce 'yan Sururiyyah suke bin ta domin kaiwa zuwa ga hadafofin su na kungiyanci (hizbiyyah) saboda haka, duk wani mai kira irin nasu ya zama wajibi mutane su nisance shi, don yana kira ne zuwa ga halaka ba zuwa ga Salafiyyar gaskiya ba!
__________________________________
(*) Raddojin Shaikh Adam Zubair Al- Nigeriy
1 - kashi na daya: https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/112
2 - kashi na biyu: https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/128
3 - kashi na uku: https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/133
4 - kashi na hudu: https://t.me/daralmahajjatalbaydhaa/135
Raba ni da bonono.. Rufin kofa da barawo!
أمين ثالث يعقوب
09 / 10 / 1441
01 / 06 / 2020

تعليقات
إرسال تعليق