RADDI GA MASU JINGINA MA WASU MALAMAI TAWAYE (01)



(1) Duk wanda yace maka Al- Imamu Malik yayi khuruji ga shugaba musulmi yayi ma Al- Imamu Malik kirkira . yana daga cikin dabi'un munharifai jingina tafarkin su da magabata domin samar masa da gindin zama.

(2) Abin da aka ruwaito daga Al- Imamu Ahmad kuma shi ne hani daga tawaye, bal Malaman Fiqhu na Baghdad sun yi gangami domin su labarta masa kuma su nemi shawarar sa a kan cewa zasu yi tawaye ga Al- Wathiq, wanda yake azzalumin shugaba ne kuma yana da kafirar akidar cewa Al- Qur'ani halittar Allah ne, amma sai Al- Imamu Ahmad yace suyi hakuri, daga cikin abin da aka ruwaito daga gare shi a kan hani daga tawaye ma Al- Wathiq akwai fadin sa:

"عليكم بالنكرة بقلوبكم، ولا تخلعوا يدا من طاعة، ولا تشقوا عصا المسلمين، ولا تسفكوا دماءكم ودماء المسلمين معكم، انظروا في عاقبة أمركم، واصبروا حتى يستريح بر أو يستراح من فاجر".

Yace: ku rinka inkari da zukatan ku, amma karku fita daga yi masa biyayya, kuma karku fita daga hadin kan musulmai, karku zubda jinanen ku da jinanen musulmai tare da jinanen ku, kuyi nazari a kan karshen lamarin ku, kuma kuyi hakuri har na kwarai ya huta, ko kuma a huta daga na banza".

سبحان الله!، الدماء!! الدماء!!!، لا أرى ذلك، ولا آمر به.
الصبر على ما نحن فيه خير من الفتنة...

Tsarki ya tabbata ga Allah! Jini!! Jini!!! bana ganin halascin haka (ma'ana: yin tawaye), kuma bana umurta da haka.
Yin hakuri a kan abinda muke cikin sa yafi alheri a kan fitina..

Sa'annan an tambaye shi game da tawaye ga Al- Wathiq din shin hakan ya dace? Sai ya bada amsa da cewa:
لا، هذا خلاف الآثار التي أمرنا فيها بالصبر".
Yace: a'a (ma'ana tawaye bai dace ba) wannan ya saba ma hadisai da akai mana umrni da hakuri a cikin su".

Duk wa'yannan maganganu Al- Khallal ya ruwaito su a cikin littafin "السنة" .

Kuma Al- Imamu Ahmad an ruwaito a cikin Akidar sa cewa: "duk wanda yayi tawaye ga shugaba dan bid'ah ne" ka duba risalar sa mai suna "أصول السنة" .

 A kan haka; cewa Ahmad yayi khuruji labarin kanzon kurege ne!

(3) Ibnu Taimiyyah bai yi khuruji ba, na kalma ko na makami, maganganun sa suna nan birjik a kan muzanta khawarijawa da bankade sharrorin su, duk wanda ya jingina masa tawaye jahili ne ko dan Bid'ah wanda yake son kare bid'ar sa ta hanyar jingina ta ga muhakkikai.

(4) Ba maganar kame-kame domin asali shine kore batun har sai in wanda yayi da'awar danganta hakan ya kawo dalilai ingantattu a kan abin da yayi da'awa, in ba haka ba ya cika fasiki wanda ya hada tsakanin bid'ah da karya ga nagartattun mutane ta hanyar jingina musu mummunan tafarkin sa domin ya samu karbuwa gurin jahilai da munharifai irin sa.

أمين ثالث يعقوب
13 / 10 / 1441
05 / 06 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!