HIRATA DA DR. KABIR LAWAL GARBA ASSALAFY KADUNA HAFIZAHULLAH AKAN DA'AWAR SALAFIYYAH (A-1) 📼
HIRATA DA DR. KABIR LAWAL GARBA ASSALAFY KADUNA HAFIZAHULLAH AKAN DA'AWAR SALAFIYYAH (A-1) 📼
MAI TAMBAYA ___ Adam Sanusi Adam (Abu Uthaymeen) Assalafy Kano 🎙️
MAI BADA AMSA ___ Sheikh Dr. Kabir Lawan Garba ( Abu Muhaisin) Assalafy Kaduna 🎤
MAI RUBUTAWA ___ Tasiu Salisu Assalafy Kano 🖋️
--------------------------------------------------------------------------
ADAM SANUSI ASSALAFY :-
--------------------------------------------
Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulillah,
Muhammadin wa'alihi wasahbihi waman wala.
Bayan haka Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu.
DR. KABIR LAWAL ASSALAFY :-
--------------------------------------------------
Wa alaikumussalam warahmatullah wabarakatuhu.
ADAM SANUSI ASSALAFY :-
--------------------------------------------
Muna godiya ga Allah madaukakin sarki wanda yakaddara haduwarmu adaidai wannan lokaci,
safiyar yau 18 gawatan zulhijja shekara ta 1441 hijirar Manzo (S.A.W)
wanda yayi daidai da 8 gawatan ogost (August) 2020 miladiyya.
Mun hadu a daidai wannan lokaci tare da Malam Kabir Lawan Kaduna
bisa wata ziyara da nakawo masa,
asalin ziyarar nazone dan muhadu da Malam mugaisa naganshi,
kasantuwar nasamu labarinshi kuma bantaba haduwa dashiba.
Malaminmu Abu Jabir Samin Dayyib Siraj wanda yake a Kano
Alokacin da karatuttukan malam Kabir suka riskeni nasauraresu nayi kokarin tambayar shi gameda waye Malam Kabir,
To Malam Abu Jabir yasanar dani waye Malam da kuma alakarsu da kuma manhajin da Malam yake akai da da'awarsa.
To Allah da ikonsa tun lokacin wata munasaba tanasa harmuyi waya da shi Malam amma dai bamu taba haduwaba,
To wannan yasa adaidai wannan lokaci naga kyautuwa da dacewa inzo muhadu da ainashin Malam mugaisa,
To wannan shine dalilin zuwana wajen Malam,
To Allah da ikonsakuma yayi daidai kan wata gaba datasa na bujiro da wasu tambayoyi da masa'il zuwa ga shi Malam saboda muhimmancinsu a daidai wannan Lokaci din, abinda nake nufi lokacine da aketa magana Salafiyyah Salafiyyah Salafiyyah,
abubuwa anata tattaunawa game da wannan abudin,
To lura da wannan naga da akwai wasu masa'il wanda zasu taimaki wanda suke Awwam insha a Allah wajan kara fahimtar wannan da'awa ta Salafiyyah.
To batare da na tsawaitaba zanso Malam ya fara gabatar mana da kanshi kafin insha Allah mu dora.
Ni Adam Sanusi Adam Abu Uthaymeen Assalafy daga Kano.
________________________________________________
"Muhadu a (A-2) domin jin yadda Malam Dr. Kabir Lawan Garba Assalafy Kaduna Hafizahullah zai gabatar mana da kanshi"
Tare da Ni Dan uwanku Tasiu Salisu Assalafy Kano
nakecewa wassalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu.
تعليقات
إرسال تعليق