RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (11)



FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (06)

(v) Fikira ta shida ita ce: hada mutane a kan ka'ida mai suna "قاعده المعذرة والتعاون" ma'ana: "ka'idar bayar da uzuri da taimakekeniya", ma'ana: idan dan Ikhwan yayi kowace irin barna ce to ba za'ayi martani gare shi ba, kuma ba za'a kushe shi ba, wanda hakan yana bayar da babbar gudummawa wajen lalata addini daga tushen sa, ta hanyar rufe kofar umurni da kyakyawa da hani daga mummuna wanda ya kunshi ayi cin gyara ga duk wanda ya saba, kuma a soki wanda ya cancanci suka a shar'ance, wacce kuma ita wannan ka'ida a wajen 'yan Ikhwan ka'ida ce ta zinariya, suna cin moriyar wannan ka'ida ne wajen kame baki a kan barnar wa'yanda suke tarayya dasu domin cimma hadafofin su na siyasa da kungiyanci (hizbiyyah) .

Lura da hadurran dake cikin wannan la'ananniyar ka'ida ta Ikhwan wanda ya hada da kamanceceniya da wa'yanda Allah ya la'anta daga cikin "banu isra'ila" na yin shiru a kan barna da mabarnata, hakan ya sanya Malaman Sunnah jagororin al- umma suka sanya baki wajen fada da wannan rubabbiyar ka'ida da ankarar da Musulmai a kan sharrin ta, wanda a takaice in sha Allahu zamu ambaci maganganun Malamai guda hudu domin kaucema tsawaitawa.

(1) Shaikh  Abdul Al- 'Azeez bin Abdillāh bin Bāz -Allah ya jikan sa- yana cewa a cikin martanin da yayi ga Muhammad Aliyu Al- Sābuniy kamar yadda yazo a cikin "مجموع فتاوى ومقالات متنوعه" mujalladi na uku shafi na hamsin da takwas (3/58) yake cewa:

 نقل ـ أي الصابوني ـ في المقال المذكور عن الشيخ حسن البنا رحمه الله ما نصه ( نجتمع فيما اتفقنا عليه ويعذر بعضنا بعضاً فيما اختلفنا فيه ) .

Al- Sābuniy ya nakalto maganar Shaikh Hassan Al- Banna Allah ya jikan sa wacce take kamar haka: (mu hadu a cikin abin da mukai ittifaki a kan sa, kuma sashen mu yayi uzuri ga sashe a cikin abin da muka saba cikin sa).

والجواب أن يقال : نعم يجب أن نتعاون فيما اتفقنا عليه من نصر الحق والدعوة إليه والتحذير مما نهى الله عنه ورسوله ، أما عُذر بعضنا لبعض فيما اختلفنا فيه فليس على إطلاقه بل هو محل تفصيل ، فما كان من مسائل الاجتهاد التي يخفى دليلها فالواجب عدم الإنكار فيها من بعضنا على بعض .

Kuma amsar da zamu bayar shine ace: eh, wajibi ne muyi taimakekeniya a cikin abin da mukai ittifaki a kan sa, na daga taimakon gaskiya da kira zuwa gare ta, da tsoratarwa daga abin da Allah da Manzon sa suka hana, amma cewa sashen mu yayi uzuri ga sashe a cikin abin da mukai sabani to wannan waje ne na fayyace magana, abin da ya kasance cikin mas'alolin ijtihadi ne wanda dalilan su ya boyu to wajibi shine rashin martanin sashen mu ga sashe a cikin su.

 أما ما خالف النص من الكتاب والسنة فالواجب الإنكار على من خالف النص بالحكمة والموعظة الحسنة والجدال بالتي هي أحسن عملاً بقوله تعالى : (وتعاونوا على البر والتقوى ولا تعاونوا على الإثم والعدوان) [المائدة :٢ ] وقوله سبحانه : ( والمؤمنون والمؤمنات بعضهم أوليآء بعض يأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر ) [التوبة : ٧١] . وقوله عز وجل : ( ادع إلى سبيل ربك بالحكمة والموعظة الحسنة وجادلهم بالتي هي أحسن ) [النحل : ١٢٥] ، وقوله صلى الله عليه وسلم : " من رأى منكم منكراً فليغيره بيده ، فإن لم يستطع فبلسانه ، فإن لم يستطع فبقلبه ، وذلك أضعف الإيمان " ، وقوله صلى الله عليه وسلم : " من دل على خير فله مثل أجر فاعله "
أخرجهما مسلم في صحيحه. والآيات والأحاديث في هذا كثيرة ) اهـ .
Amma kam abin da ya saba ma nassi na Al- Qur'ani da Sunnah to wajibi ne yin martani ga wanda saba ma nassi cikin hikima da wa'azi mai kyau da jayayya a cikin fuska mafi kyawo, ana masu aiki da fadin Allah madaukaki: (kuma sashen ku ya taimaki sashe a kan ayyukan da'a da barin hane-hane , kuma kada sashen ku ya taimaki sashe a kan rashin umurtuwa da umurnin Allah da wuce iyakokin sa) [Al- Ma'idah: 2].  Da kuma fadin sa: (kuma su muminai maza da muminai mata sashen su majibincin sashe ne, suna umurni da imani da biyayya kuma suna hani daga shirka da sabon Allah) [Al- Taubah: 71] da kuma fadin sa Mai girma da buwaya: (kayi kira zuwa ga tafarkin mahaliccin ka a cikin hikima da wa'azi mai kyawo kuma kayi jayayya dasu a cikin fuska mafi kyawo) [Al- Nahl: 125]. Da fadin (Manzon sa) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (wanda yaga abin ki daga cikin ku to ya sauya shi da hannun sa, idan ba zai iya ba to ya sauya shi da harshen sa, idan ba zai iya ba to ya sauya shi da zuciyar sa(ma'ana: sai ya kyamaci abin a zuciyar sa) kuma wannan shine mafi raunin imani) da fadin sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (wanda yayi nuni zuwa ga wani alheri to zai samu kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi) .
Al- Imamu Muslim ne ya ruwaito su cikin Sahih din sa, kuma ayoyi da hadisai da suka zo a kan wannan suna da yawa.

(2) Shaikh Muhammad Nāsiru Al- Deen Al- Albāniy -Allah ya jikan shi- shima yana cewa kamar yadda yazo a cikin kaset mai lamba ta dari uku da hamsin da shida (365) daga cikin "Silsilatu Al- Hudā wa Al- Nur" wanda ya kasance cikin tattaunawa da daya daga cikin almajiran Muhammad Surur! (Shugaban Sururiyyah)!! Shaikh yake cewa:

الإخوان المسلمون ينطلقون من هذه القاعدة التي وضعها لهم رئيسهم الأول، وعلى إطلاقها، و لذلك لا تجد فيهم التناصح المستقى من نصوص كتاب الله وسنة رسول الله ؛ ومنها سورة العصر: ( والعصر [١] إن الإنسان لفي خسرٍ [٢] إلا الذين آمنوا وعملوا الصالحات وتواصوا بالحق وتواصوا بِالصبر [٣] ) ؛ هذه السورة كان أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم إذا تلاقوا ثم أرادوا ان يتفرقوا قرأ أحدهم هذه السورة لأهميتها ( وتواصوا بالحق وتواصوا بِالصبر ) ؛
Yan Ikhwan suna tafiya kan wannan ka'ida wacce jagoran su na farko(yana nufin Hassan Al- Banna) ya dora musu, kuma suna tafiya da ita ne a saken ta (ma'ana: ba fayyacewa koda mutum yayi barna cikin akida ne zasu kame baki a kan sa!) Kuma saboda hakane ma ba zaka samu nasiha ma juna a tsakanin su ba, wacce ake shayo ta daga littafin Allah da Sunnar Manzon sa; kuma daga cikin ta akwai Suratu Al- 'Asr (Ina rantsuwa da lokaci [1] lallai dan Adam yana cikin asara [2] sai wa'yanda sukai imani kuma suka aikata kyawawan ayyuka, kuma sashen su yayi wasici ga sashe da gaskiya kuma sashen su yayi wasici ga sashe da hakuri [3] ) ; wannan surar ya kasance  Sahabbai in suka hadu da juna kuma suka so rabuwa daya daga cikin su yana karanta ta domin muhimmancin ta. (kuma sashen su yayi wasici ga sashe da gaskiya kuma sashen su yayi wasici ga sashe da hakuri).

 الحق كما تعلم ضد الباطل ، والباطل أصولي و فروعي ، كل ما خالف الصواب فهو باطل ، هذه العبارة هي سبب بقاء الإخوان المسلمين نحو سبعين سنة عملياً بعيدين فكرياً عن فهم الإسلام فهماً صحيحا وبالتالي بعيدين عن تطبيق الإسلام عملياً لأن فاقد الشيء لا يعطيه" اهـ

Ita gaskiya kamar yadda ka sani kishiyar karya ce, kuma ita karya tana da tushe kuma tana da reshe, dukkan abin da ya saba ma dai-dai to bata ne, wannan ibarar (yana nufin fadin su: kuma sashen mu yayi uzuri ga sashe a inda mukai sabani) ita ce sababin wanzuwar 'yan Ikhwan kusan shekaru saba'in a cikin aiki sunyi nesa a fikira basu fahimci musulunci fahimta nagartacciya ba, kuma sunyi nesa daga tabbaka musulunci a aikace, domin marashin abu baya iya bayar dashi!" .

(3) Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- 'Uthaymeen -Allah ya jikan sa- shima yana cewa kamar yadda yazo a cikin "الصحوة الإسلامية ضوابط وتوجيهات" shafi na dari da saba'in da daya, yana mai bayar da amsa ga tambaya da akai masa cewa:

ما رأيكم فيمن يقول : نجتمع فيما اتفقنا فيه ويعذر بعضنا بعضاً فيما اختلفنا فيه ؟

Menene ra'ayin ku (ku Malamai) game da wanda yake cewa: mu hadu a cikin abin da mukai ittifaki a kan sa, kuma sashen mu yai uzuri ga sashe a cikin abinda muka saba ma juna?

أما نجتمع فيما اتفقنا فيه فهذا حق. وأما يعذر بعضنا بعضاً فيما اختلفنا فيه فهذا فيه تفصيل، فما كان الاجتهاد فيه سائغاً فإنه يعذر بعضنا بعضاً فيه ، ولكن لا يجوز أن تختلف القلوب من أجل هذا الخلاف . وأما إن كان الاجتهاد غير سائغ فإننا لا نعذر من خالف فيه ويجب عليه أن يخضع للحق فأول العبارة صحيح وأما آخرها فيحتاج إلى تفصيل) اهـ
Sai yace: amma fadin cewa mu hadu a cikin abin da mukai ittifaki a kai wannan gaskiya ce, amma cewa sashen mu yayi uzuri ga sashe a kan abinda mukayi sabani cikin sa wannan akwai fayyacewa a cikin sa, abin da ya kasance ijtihadi nada mashiga cikin sa to sashen mu zai uzuri ga sashe a cikin sa, sai dai baya halasta zukata su saba a kan wannan sabanin. Amma idan ya kasance ijtihadi baya da mashiga a cikin sa, to lallai mu ba zamui uzuri ga wanda ya saba a cikin sa ba, kuma wajibi ne a kan sa da ya risina wa gaskiya, saboda haka farkon ibarar dai-dai ne, amma karshen ta yana bukatar fayyacewa!.

(4) Wannan dai ka'idar ta uzuri ga wanda ya saba ita ce ka'idar da 'yan Sururiyyah suke aiki da ita wajen bayar da kariya ga duk wani gawurtaccen mabarnaci wanda yake cikin Ikhwan komai bayyanar barnar sa kuwa, suna cin moriyar ta ne domin yada kungiyancin su da manufofin su na siyasa kamar yadda bayani ya gabata, shi yasa suke kiran ta da "القاعدة الذهبية" ma'ana: "ka'ida ta zinariya" wacce Shaikh Sāleh Al- Fauzān Allah ya kiyaye shi cikin martanin sa ga wannan ka'ida yayi musu cin gyara yace da ita "قاعدة طاغوتية" ma'ana "ka'ida ce 'yar dagutu" , domin ya saba ma 'yan bid'ar Ikhwan kuma ya bayyanar da kiyayyar sa ga rubabbiyar ka'idar tasu!

Domin kaucema tsawaitawa zan baka adireshin da zaka saurari wannan magana da kunnuwan ka daga Shaikh Sāleh Al- Fauzān din!
Latsa wannan rubutun dake kasa:
⤵️⤵️⤵️

https://ar.alnahj.net/audio/328

Ko kuma kabi wannan adireshin domin sauke shi a na'urar ka kai tsaye : ⤵️⤵️⤵️

https://ar.alnahj.net/sites/default/files/audio/fo-101.mp3

Kai raba ni da bonono... Rufin kofa da barawo!

أمين ثالث يعقوب
08 / 10 / 1441
31 / 05 / 2020

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!