المشاركات

عرض المشاركات من 2019
صورة
Raddi ga Sururiyyah
صورة
*SHAIKH SĀLEH AL- FAUZAN YANA KARFAFAR SALAFAWAN GASKIYA!* An tambayi Shaikh Saleh Al- Fauzan -Allah ya kiyaye shi- Mai tambayar yake cewa: السؤال:  نحن مجموعة من الشباب ندعوا إلى منهج السلف الصالح، وملازمة الجماعة والسمع والطاعة لولي الأمر في غير المعصية، ونحذر من الجماعات الحزبية، ولكنهم يحذّرون منا، ويسموننا "جامية" فهل نستمر على ما نقوم به؟ Tambaya: mu wasu taro ne na matasa, muna kira zuwa ga Manhajin Al- Salaf Al- Sālih, da kuma lazimtar jama'ah, da sauraro da biyayya ga shuwagabanni a cikin abinda ba sabon Allah bane, kuma muna tsoratarwa daga kungiyoyi "na hizbiyyah", sai dai su suna tsoratarwa daga garemu, kuma suna kiranmu da (lakabin) "Al- Jāmiyyah"  shin zamu ci gaba da abin da mukeyi ne? الجواب: استمروا واصبروا ولا يهمكم ما يقولون -  [📖 رسالة وجوب لزوم الجماعة ص38] Amsa: kuci gaba da abinda kukeyi, kuma kuyi hakuri, kuma kar abinda suke fade ya dame ku, domin ku ba yardar su kuke nema ba, haka kuma ba yabon su kuke nema b...
صورة
GASKIYAR LAMARI (2) : Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan gaskiya, shi yasa Allah yake taimakon su, babu wani karkatacce, ko mabiyin karkataccen tafarki da zasu soka sai wannan suka ta zama gyambo garesa, dalili akan haka: Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan turba ta musulunci irin na musulman farko, kuma Allah yayi alkawarin taimakon muminai, yayi alkawarin tseratar da muminai daga fitintinu kamar yadda yayi alkawarin tseratar da manzannin sa, wannan tseratarwa daga fitintinun duniya ne wa'yanda fitina ba zata sanya su su karkace daga tafarkin gaskiya ba, kuma a lahira zai tseratar dasu daga azabar wuta, wacce yayi alkawarin azabtar da masu sabawa Manzannin sa ne da ita, sannan kuma yayi alkawarin gidaje na Aljannah da rayuwa ta jin dadi ga Muminai a ranar lahira, jin dadi na har abada saboda tsayuwa da sukayi akan Imani da abinda Imanin yake kunshe dashi, wanda ya kunshi martanin abinda ya sabawa gaskiya, zuwa wanda ya aikata shi ko ya furta shi, sannan All...
صورة
GASKIYAR LAMARI (1) Komai daren dadewa Allah zai bayyana gaskiya, kuma zai daukaka ma'abotan ta, ambatonsu zai ci gaba da wanzuwa tare da ambaton gaskiyar da suka tsayu akan ta, kuma suka bata kariya, sukayi martanin abinda ya saba wa tafarkin Annabi da Sahabbai, na maganganu ne ko na ayyuka, ta yadda su kuma ma'abota karkata suke mutuwa ambatonsu ya mutu, ko kuma ambatonsu ya wanzu tare da sukar tafarkin da suka rayu akan sa, sukayi turjiya wajen kariya ga barna, suka bata lokacinsu da surutai wajen kishiyantar gaskiya da bata sunan mabiyanta na gaskiya, ambatonsu zai wanzu ne a bakin ma'abota gaskiya tare da martani ga barnar da suka shayar da mutane da sunan addini, ko da sunan Sunnah, ko da sunan Salafiyyanci, shi tafarkin Sunnah na gaskiya yana nan dama tun tuni yana rabewa tsakanin gaskiya da karya, ba yau aka fara ba, kuma Ahlus- Sunnah na gaskiya Allah ne yake musu yaki, kuma shine yake daukaka ambaton su, ba don komai ba, sai don sun tsaya akan turba ta gaski...
صورة
Wani yayi tambaya yace: "menene ma'anar Sururiyyah?" Sai nace dashi: Kungiya ce wacce ake nasabta ta ga Muhammad Surur Zainul Abideen, wanda asalin sa dan Syria ne, yayi zama a Saudiyyah shekaru 8, yayi karatu a Kwalejin ilimi a Buraidah, daga nan ya koma Brtaniya, ya koma Qatar wanda a nan ya mutu a shekarar 2016, wannan kungiya ta Sururiyyah an san ta ne da gauraye tsakanin Sunnah da Ikhwaniyan ci, sune suka kawo rudanin cewa Aqeedar Mutum Salafiyyah amma Manhajin sa Ikhwaniyyah, an san su da tawaye ga shuwagabanni Musulmai, tawaye na kalma da kuma karfafar Khawarijawa masu yakar gwamnatocin su, da yaba musu, da kuma tunzura matasa a kan zanga-zanga ma gwamnatocin su, da da'awar neman 'yanci ko kuma inkari ga azzalumai, sannan suna kambama Sayyid Qutb da tawagar sa 'yan ta'adda, basa kuma ganin cewa akwai gwamnatin Musulunci a wannan zamanin, suna kiran shuwagabanni Musulmai da الطواغيط (ma'ana: dagutai) sannan suna jifan Malaman Sunnah wa...
صورة
*DA'AWAR MA'ABOTA SUNNAH KIRA NE ZUWA GA TAFARKIN ALLAH, BA DA'AWA CE TA TARA KUDIN MUTANE BA!* ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﻣﻘﺒﻞ ﺑﻦ ﻫﺎﺩﻱ ﺍﻟﻮﺍﺩﻋﻲ - ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :- ..." ﻓﺄﻧﺼﺢ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻣﻮﺍ ﺑﻮﺍﺟﺒﻬﻢ ﻧﺤﻮ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ، ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ، ﻧﺤﻦ ﻟﺴﻨﺎ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺍﺗﺒﺎﻋﻨﺎ ﻓﻠﺴﻨﺎ ﺃﻫﻼ ﻷﻥ ﻧﺘﺒﻊ، ﺑﻞ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺃﻥ ﻧﺘﺒﻊ ﻧﺤﻦ ﻭﻫﻢ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ .- ﻭﻟﺴﻨﺎ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺃﺧﺬ ﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ، ﻭﻟﻮ ﺫﻫﺒﺖ ﺇﻟﻰ ﺃﻱ ﺑﻠﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﻼﺩ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ ﻓﻠﻦ ﺗﺮﻯ ﺳﻨﻴﺎ ﻳﻘﻮﻡ ﻭﻳﻌﻆ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺣﺘﻰ ﻳﺒﻜﻴﻬﻢ، ﺛﻢ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻳﻔﺮﺵ ﻋﻤﺎﻣﺘﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﺒﺎﺏ ." ‏[ ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻟﻤﺠﻴﺐ ‏( 75 - 76)]. Al- Allāmah Muqbil Bin Hādiy Al- Wādi'iy -Allah ya jikan sa- yana cewa: Ina yiwa ma'abota Sunnah nasiha da su tsayu da wajibin su ta bangaren da'awah, amma don fuskar Allah mai girma da buwaya, mu bama kiran mutane don su bimu, domin mu bamu cancanci a bimu ba, sai dai muna kiran mutane ne damu dasu mubi littafin Allah da Sunnar Manzon Allah -Sallallāhu 'alayhi wasallam- Kuma mu ba kiran mutane muke don mu karbi k...
MAGANA AKAN 'YAN BID'AH DA MASU KARKATACCEN MANHAJI BA GIBA (GULMA) BACE  ❁❁❁❁❁❁       ــــــ ❁❁❁❁❁❁ ـــــ       ❁❁❁❁❁❁ Fatawar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen (Allah ya jikansa) : ❍ الشيخ محمد بن صالح العثيمين : السّـؤال : الكلام في أهل البدع ، مثل أن يقال مثلاً: أنهم يؤولون الآيات والأحاديث، ويقولون: يفعلون كذا وكذا.. أيعتبر هذا غيبة إذا كان بين الطلبة ؟ Tambaya: Magana akan 'yan Bid'ah, kamar misali ace: sunayin tawilin ayoyi da hadisai, kuma suna aikata kaza da kaza, shin wannan ana daukarsa giba (gulma) ce in ya kasance a tsakanin dalubai ne? »» الجواب: الكلام في أهل البدع ومن عندهم أفكار غير سليمة أو منهج غير مستقيم، هذا من النصيحة وليس من الغيبة ، بل هو من النصيحة لله ولكتابه ولرسوله وللمسلمين ، فإذا رأينا أحداً مبتدعاً ينشر بدعته ، فعلينا أن نبين أنه مبتدع حتى يسلم الناس من شره ، وإذا رأينا شخصاً عنده أفكار تخالف ما كان عليه السلف فعلينا أن نبين ذلك حتى لا يغتر الناس به ، Amsa: Magana akan 'yan Bid'ah da ma...
صورة
TABBAS FADIN GASKIYA MUSAMMAN WACCE TA SABA WA MUTANE TANA JANYO WA MUTUM: 1 - kiyayya/bakin jini 2 - rashin yardar mutane 3 - fushin mutane 4 - bata suna da sura. AMMA IN KAYI DON ALLAH TANA JANYO : 1 - soyayyar mahaliccin mutane 2 - kusanci ga Allah da muminai 3 - Yardar Allah mahaliccin mutane 4 - Bayyanar gaskiya a asalin surar ta 5 - Bayyanar karya a asalin surar ta 6 - Fita daga sahun fasikai 7 - Cike alkawarin da ka dauka na Allah cewa zaka bayyana gaskiya kuma ba zaka boye ba 8 - Tsira daga tsinuwar Allah da Mala'iku da Mutane da dabbobi da kifayen dake cikin ruwa 9 - Tsira daga linzamin jahannama wanda za'a sanyawa wa'yanda suka ki bayyana gaskiya 10 - Samun alkawarin Allah na taimakon sa, da tseratarwar sa idan ya tashi kama azzalumai tun a nan duniya, da samun Aljannar sa wacce ita ce masaukin bayin sa ma'abota tsayuwa da gaskiya KIN BAYYANA GASKIYA KUMA YANA JANYO : 1 - La'antar Allah da la'antar masu la'anta 2 - Koyi d...
صورة
DAGA CIKIN LITTAFAN 'YAN GWAGWARMAYA, A GUJE SU! - AMINU THALITH YA'QUB DAGA CIKIN LITTAFAN ‘YAN  G WAGWARMAYA, A GUJE SU! بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى اللهم وسلم وبارك على النبي الكريم وعلى آله وصحبه أجمعين، ومن تمسك بسنته وسار على نهجه إلى يوم الدين. Bayan haka Assalāmu ‘alaykum warahmatullāhi wabarakātuh. To da farko dai bayan godiya ga Allah madaukaki, wannan gabatarwa ce a kan littafan ‘yan gwagwarmaya wanda aka nemi mu ambata su, bayan karanta rubutun Dr. Muhammad Sabi’u Sulaimān da kuma bayan sauraron bayanai a kan Kungiyar Sururiyyah gabatarwar Ustadh Huzaifah Aminu Daurawa da Dr. Isma’il Aliy Yahya Maikwano, Allah ya kiyaye su -dukkanin su guda ukun suna karatu yanzu haka a Jami’ar Musulunci ta Madeenah , Allah ya datar da su da mu ma baki daya. Mai comment -Allah ya datar da shi da mu baki daya- yana cewa: “ Jazakallahu khairan, bayanan da dalibai da malamai ke bukata kenan, domin matsalar da ake fama da shi kenan ga yawancin masu daawar su...
صورة
AHLUS - SUNNAH WAL- JAMA'AH: SALAFAWAN GASKIYA, BASU YARDA DA FITO NA FITO KO KASHE SHUWAGABANNI BA, KO DA AZZALUMAI NE, HAKA KUMA BASU YARDA DA TAFARKIN QA'ADIYYAH ZAUNANNUN KHAWARIJAWA BA!: Al- Imam Al- Nawawiy Allah ya jikan sa yana cewa: وأما الخروج عليهم وقتالهم فحرام بإجماع المسلمين وإن كانوا فسقة ظالمين، وقد تظاهرت الأحاديث بمعنى ما ذكرته، وأجمع أهل السنة أنه لا ينعزل السلطان بالفسق [شرح مسلم ٢٢٩/١٢]. Amma fito na fito garesu da yakar su haramun ne da ijma'in musulmai, ko da sun kasance fasikai ne azzalumai, kuma tabbas hadisai sun bayyana ma'anar abinda na ambata shi, kuma Ahlus- Sunnah sunyi ijma'i akan cewa ba'a tunbuke shugaba saboda fasikan cin sa. [Sharhu Muslim 12/229]. Al- Imamu Ahmad Bin Hanbal Allah ya jikansa yana cewa: ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه لأحد من النَّاس، فمن فعل ذلك فهو مبتدع على غير السّنة والطريق. [أصول السنة ص ٤٦]. Kuma bai halasta a yaki shugaba ba, haka kuma bai halasta ayi fito na fito garesa ba, ga...
صورة
SAURARON BID'AH HARAMUN NE KAMAR YADDA KIRA ZUWA GARETA YAKE HARAMUN! Al- ‘Allāmatu Bnu Al- Qayyim (Allah ya jikan sa) yana cewa: «وأما محرّمه: فهو النطق بكلّ ما يبغضه الله ورسوله ﷺ ، كالنطق بالبدع المخالفة لما بعث الله به رسوله ﷺ ، والدعاء إليها ، وتحسينها وتقويتها ، وكالقذف وسب المسلم ، وأذاه بكلّ قول . والكذب ، وشهادة الزور ، والقول على الله بلا علم . وهو أشدّها تحريما» [التفسير القيم ص ١١٦]. « Amma kuma haramtaccen sa (ma'ana: furuci na harshe) shine yin furuci da dukkan abinda Allah yake kin sa,  Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ma  yake kinsa , kamar furuci da Bid'ah wacce take sabanin abinda Allah ya aiko Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - dashi ne , da kira zuwa ga wannan Bid'ah , da kayata ta , da karfafar ta , haka kuma yin kazafi haramun ne haka zagin musulmi , da cutar dashi da kowacce irin magana . haka kuma karya haramun ce , da shaidar zur , da magana akan Allah ba tare da ilimi ba . kuma haramcin...
صورة
FA'IDOJI DAGA MUHADARAR SHAIKH SĀLEH AL- FAUZĀN 01 A cikin muhadara ta Shaikh Sāleh Al- Fauzān (Allah ya kiyaye shi) mai suna: ((موقف المسلم من الفتن والمظاهرات والثورات)) Ma'ana: ((Matsayar Musulmi a kan fitintinu da zanga-zanga da juyin juya hali)) Wacce aka buga ta a matsayin littafi kuma ya bayar da izinin buga ta a Ashirin da hudu ga watan Jumādal Ula shekara ta alif da dari hudu da talatin da biyu (24/05/1432) bayan hijira. Yayi wasu maganganu wa'yanda suka ja hankali na kamar haka: (1) "فهذه الفتن فيها خير؛ لأنها تميز بين الكفر والإيمان وتبين أهل النفاق والمخادعات وتكشف حقيقتهم فلا يغتر بهم بل يحذر منهم، هذه حكمة الله سبحانه وتعالى". ص ١١ Ma'ana: "wa'yannan fitintinun akwai alkhairi a cikin su; domin suna banbance tsakanin kafirci da imani, kuma suna bayyana ma'abota munafurci da yaudara kuma suna bankade hakikanin su, ta yadda ba za'a rudu da su ba, bal ma sai dai a tsoratar daga gare su, wannan hikimar Allah ce mai tsa...
صورة
ASSASA KUNGIYOYI BAYA CIKIN ABINDA ADDINI YA YARDA DASHI! Shaikh Sālih Al- Fauzan Allah ya kiyaye shi yana cewa: التفرق ليس من الدين ، لأن الدين أمرنا بالاجتماع وأن نكون جماعة واحدة وأمة واحدة على عقيدة التوحيد وعلى متابعة الرسول  ﷺ، Rarrabuwa (cikin kungiyoyi) baya daga addini, domin addini ya umurcemu da haduwa, kuma mu kasance jama'ah guda daya, al'ummah guda daya, akan Aqidah ta Tauhidi, da biyayya ga Manzo Sallallāhu 'alayhi wasallam, Nace: anan Shaikh ya bayyana mana akan abinda ya zama wajibi Musulmi su hadu a karkashinsa, a karkashin Aqida ta Tauhidi, ba a karkashin kungiyoyi ba, masu kungiya sun fahimci kalmar jama'ah a baude, shiyasa karan kansu suke akan dimuwa da rikici, a sahun 'yan kungiya zaka taras har da wanda yake akan Aqidar mu'utazilanci kuma sun san da haka sama da shekaru goma sha, amma har yanzu suna kirga wannan bamu'tazile a cikin Ahlus Sunnah, Allah ya kiyaye mu daga son zuciya da bata. يقول تعالى {إنَّ هَذه أمَّتُكم...
صورة
?MECECE SALAFIYYAR GASKIYA بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، وعلى آله وصحبه ومن والاه.. وبعد: السلام عليكم ورحمة الله وبركاته. Abdulmalik Almaimooniy Allah ya jikansa yace: قال لي الإمام أحمد رحمه الله: «يا أبا الحسن، إياك أن تتكلم في مسألة ليس لك فيها إمام». انظر مناقب الإمام أحمد (١٧٨) ابن الجوزي. Yace: Al-Imamu Ahmad yace dani: «Ya kai baban Alhassan, kashedinka, karkayi magana akan wata mas'ala da baka da Jagora(magabaci) acikinta» . (A duba Manaqibul Imam Ahmad (178) wallafar Ibnu Al- Jawzi). *MUNA DA JAGORORI MAGABATA NA KWARAI AKAN DA'AWAR MU TA SALAFIYYAR GASKIYA!* Al-Imāmu Al-Auzā'iy Allah ya jikansa yana cewa: «اصبر نفسك على السنة، وقف حيث وقف القوم، وقل بما قالوا، وكفّ عما كفوا، واسلك سبيل سلفك الصالح فإنه يسعك ما وسعهم» (اللالكائي في شرح أصول الاعتقاد ١٥٤/١). Yace: «Ka hakurar da kanka akan (ruko da) Sunnah, kuma ka tsaya iyakar inda ma'abota Sunnah(wato Annabi da Sahabbai) suka tsaya, sannan ka furta dai-dai abinda suka furta, ...