GASKIYAR LAMARI (2) :

Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan gaskiya, shi yasa Allah yake taimakon su, babu wani karkatacce, ko mabiyin karkataccen tafarki da zasu soka sai wannan suka ta zama gyambo garesa, dalili akan haka: Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan turba ta musulunci irin na musulman farko, kuma Allah yayi alkawarin taimakon muminai, yayi alkawarin tseratar da muminai daga fitintinu kamar yadda yayi alkawarin tseratar da manzannin sa, wannan tseratarwa daga fitintinun duniya ne wa'yanda fitina ba zata sanya su su karkace daga tafarkin gaskiya ba, kuma a lahira zai tseratar dasu daga azabar wuta, wacce yayi alkawarin azabtar da masu sabawa Manzannin sa ne da ita, sannan kuma yayi alkawarin gidaje na Aljannah da rayuwa ta jin dadi ga Muminai a ranar lahira, jin dadi na har abada saboda tsayuwa da sukayi akan Imani da abinda Imanin yake kunshe dashi, wanda ya kunshi martanin abinda ya sabawa gaskiya, zuwa wanda ya aikata shi ko ya furta shi, sannan Allah ya haramtawa muminai yin zalunci kamar yadda shi din ya haramta hakan ga kansa, muminai na gaskiya sune Sahabban Manzon Allah Sallallahu 'alaihi wasallama wa'yanda sukayi biyayya garesa a lokacin kunci da lokacin walwala, haka suma Ahlus- Sunnah wa'yanda sukabi tafarkin Sahabbai suka kasance, sannan Allah yayi umurni abi tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama, kuma yayi hani ga saba masa, yayi alkawarin azaba ga wa'yanda suke sabawa Manzon Allah Sallallahu 'alaihi wasallama kuma suke sabawa tafarkin muminai, hakika a lokacin da wahayin Al- Qur'ani yake sauka babu wasu muminai da sukafi dacewa da Allah ya tsarkake tafarkinsu kuma yayi alkawarin azaba ga wanda ya kama wanin tafarkin nasu in ba Sahabbai ba, kuma Allah yayi umurni da abi tafarkin wa'yanda suka komar da lamurransu gareshi.

Al- 'Allamatu Ibnu Al- Qayyim Allah ya jikan sa yana cewa:

«وكلّ من الصحابة منيب إلى الله، فيجب اتباع سبيله، وأقواله واعتقاداته من أكبر سبيله». [إعلام الموقعين ٩٩/٤].

Yace: «kuma kowanne daya daga cikin Sahabban Manzon Allah -Sallallaahu 'alayhi wasallama- mai komawa ne da -lamurran sa- zuwa ga Allah, saboda haka ya zama wajibi abi tafarkin sa, kuma maganganun sa da Akidun sa suna daga cikin mafi girman tafarkin sa».
[I'ilaam Al- Muwaqqi'een 4/99].

Wannan ma martani ne ga masu cewa ba za'a dauki Aqida daga Hadisan Ahad ba! Allah ne mafi sani.

Abinda ya hada muminan kowane zamani shine dacewar Aqidarsu da Aqidar Sahabbai, bal Aqidar Tauheedi itace ta hada tsakanin muminai na farko da na karshe, kuma itace mafi girman tushe wanda 'yan uwantaka take kulluwa, a karkashin bin abinda wannan da'awa ta Tauheedi ta kunsa na kadaita Allah da bauta da kuma kadaita biyayya ga Manzon Allah a wajen bautawa Allah, wannan 'yan uwantaka ta Imani tana da matukar muhimmanci, domin 'yan uwantaka ce wacce take rayayyiya bata mutuwa, menene yafi dadi ace Mumini ya duba tafarkin da yake kai yaga tafarki ne wanda Annabi da Sahabbai sukayi wa Allah bauta dashi?

Kuma lallai a bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu 'alaihi wasallama to babu shakka Sahabbai sune ma'aunin gane tafarki na gaskiya daga jabun tafarki na 'yan 419.

Annabi Sallallahu 'alaihi wasallama yayi bayanin cewa sabani mai yawa zai barke, kuma yayi umurni da a rike tafarkin sa da tafarkin khalifofi shiryayyu masu shiryarwa, babu shakka Muminai suna riko ne da umurnin Manzon Allah a fili kuma a boye, basa daukar umurnin sa kadai a wajen dora hannu a kirji a yayin Sallah, ko kadai a wajen tsaida gemu, ko kadai a wajen gajarta tsayin tufafi ga maza ko sakin sutura da hijabi ga mata, bal suna aikata umurninsa ne a kowace gaba ta addini, saboda sun kasance mabiya tafarkinsa da kyautatawa, idan ka gane hakan, kaga damu dakai mun yarda cewa Annabi yayi bayanin faruwar wannan sabanin, to meyasa kai kaki binsa wajen riko da Sunnarsa da ta khalifofinsa shiryayyu? Shin baka son ka shiga cikin sawun masu biyayya ga Manzo da kyautatawa ne? Ko Sunnar da kakeyi silsilar ta bata tikewa ne zuwa ga Manzon Allah, ko ta yanke ne zuwa wani Shehi ko shugaban wata Kungiya? Meyasa kake fadin abinda baka aikatawa?

Manzon Allah yake cewa:

أوصيكم بتقوى الله عزّ وجلّ، والسمع والطاعة. وإن تأمر عليكم عبد، فإنه من يعش منكم بعدي فسيرى اختلافا كثيرا، فعليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين من بعدي، عضوا عليها بالنواجذ، وإياكم ومحدثات الأمور، فإن كل بدعة ضلالة».
[رواه أحمد ، وأبو داود ، والترمذي].

Ina muku wasiyyah da tsoron Allah mai daukaka da buwaya, kuma ina muku wasiyyah kuyi sauraro da biyayya, ko da bawa ne yake shugabancin ku, domin lallai duk wanda yayi tsawon rai daga cikin ku a baya na to tabbas zai ga sabani mai yawa, to ina muku wasiyyah kuyi riko da Sunnah ta da Sunnar khalifofi Shiryayyu masu shiryatar wa a baya na, kuyi riko da ita da hakoran tauna, kuma ku guji kirkirarrun lamurra, domin dukkan Bid'ah bata ce.

AL- IMAM AL- BAGHAWIY YANA CEWA:

وقوله: «فإنه من يعش منكم فسيرى اختلافا كثيرا» إشارة إلى ظهور البدع والأهواء، والله أعلم، فأمر بلزوم سنته، وسنة الخلفاء الراشدين، والتمسك بها بأبلغ وجوه الجدّ، ومجانبة ما أحدث على خلافها.
إلى أن قال:  وأراد بمحدثات الأمور: ما أحدث على غير قياس أصل من أصول الدين،  فأما ما كان مردودا إلى أصل من أصول الدين فليس بضلالة.
[شرح السنة للبغوي ١٤٢/١].
Yake cewa:
Kuma fadin sa: «Kuma lallai duk wanda ya rayu a cikin ku zai ga sabani mai yawa» ishara ce zuwa ga bayyanar Bid'o'i da son zuciya, Allah ne mafi sani, sai yayi umurni da lazimtar Sunnar sa da Sunnar Khalifofi shiryayyu, da kuma riko da ita da mafi kololuwar fuska ta jajircewa (wajen rikon), da kuma nisantar abin da aka kirkira sabanin ta.

Zuwa inda yake cewa: kuma abinda yake nufi da kirkirarrun lamurra : shine duk abinda aka kirkireshi ba tare da kiyasin wani asali daga asullan addini ba, amma duk abinda ake mayar dashi zuwa ga wani asali na asullan addini to wannan ba bata bane.
[Sharhu Al- Sunnah ta Al- Baghawiy 1/142].

Kenan duk abinda baida asali a addini daga cikin ababen da ake aikatawa da niyyar neman lada da neman kusanci zuwa ga Allah wannan Bid'ah ne kuma bata ne, ba kyawon niyya kadai ake lura da ita ba, ana kuma lura da bangaren Al- mutaba'ah, wato bin tafarkin Manzon Allah, to gashi mutane sun kirkiri kungiyoyin addini kowacce kungiya tana ganin itace akan dai-dai, sannan kowacce kungiya tana da irin tata da'awar, yau wa'yancan suyi hadin kai ba bisa gaskiya ba gobe su dare, suyi baran-baran, kungiyoyi gasu nan da sunan addini, wasu kungiyoyin na 'yan ta'adda ne, wasu kuma komai rubewar Aqidar mutum suna tare dashi da sunan hadin kai.

Ma'abota Sunnah na gaskiya basa cewa kar ayi magana,  suna cewa ne ayi adalci wajen zance, iya barnar mutum ita zasu fadi, babu kari, babu kage ga kowa, domin addinin gaskiya ba da karairayi ake kariya garesa ba.

Al- Imam Ibnu Katheer yana cewa:

 «وهذان ركنا العمل المتقبل، لا بدّ أن يكون خالصا لله، صوابا على شريعة رسول الله صلى الله عيه وسلم»
[تفسير القرآن العظيم ٢٠٨/٣].

Yace: kuma wa'yannan sune sharudda biyu na aiki karbabbe, babu makawa sai ya kasance don Allah akayi shi, kuma sai ya kasance ya dace da tafarkin Manzon Allah Sallallahu 'alayhi wasallama.
[Tafseeru Al- Qur'an Al- 'Adheem 3/208].

Duk wata Darika ko wata kungiya ma'abotan ta suna tutiyar cewa don Allah suke yi ba don a biyasu ba, kuma son addini ne ya kaisu ga hakan, to amma shin hakan ba zai yiwu ba sai kun raba kanku daga Sunnah da tafarkin Ma'abota Sunnah na farko kun kirkiri kungiyoyi kun kacaccala addini? Ina biyayya ga Annabi? Ina umurnin da yayi a rike tafarkin sa da na Khalifofi shiryayyu?
Me yasa kuke jin zafi in munce tafarkin Annabi da Sahabbai ba kungiyoyi bane? Aqeedah ce da Manhaji kwaya daya tal wanda ya wadaci magabatan mu, ko kuna ganin ku bazai wadace ku bane shi yasa kuke kirkirar sababbin tafarkoki, da mabanbantan da'awoyi wa'yanda sun sabawa Tafarkin Annabi da Sahabbai?.

Ya 'yan uwa Musulmai ku zama mabiyan Annabi da kyautatawa karku zama masu cin gyaran tafarkin Annabi, domin sakon Annabi ya cika, babu gibi da wani zaizo ya cike masa daga baya, kuma tafarkinsa cikakke ne, baya bukatar kwaskwarima, domin kwaskwarima a addini Bid'ah ce, kuma Allah da Manzanninsa da dukkan bayinsa muminai sun barranta daga dukkanin Bid'ah a addini.

Dan uwanku a Musulunci da Sunnah:

أمين ثالث يعقوب

30 / 01 / 1440
10 /10 / 2018

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!