GASKIYAR LAMARI (1)

Komai daren dadewa Allah zai bayyana gaskiya, kuma zai daukaka ma'abotan ta, ambatonsu zai ci gaba da wanzuwa tare da ambaton gaskiyar da suka tsayu akan ta, kuma suka bata kariya, sukayi martanin abinda ya saba wa tafarkin Annabi da Sahabbai, na maganganu ne ko na ayyuka, ta yadda su kuma ma'abota karkata suke mutuwa ambatonsu ya mutu, ko kuma ambatonsu ya wanzu tare da sukar tafarkin da suka rayu akan sa, sukayi turjiya wajen kariya ga barna, suka bata lokacinsu da surutai wajen kishiyantar gaskiya da bata sunan mabiyanta na gaskiya, ambatonsu zai wanzu ne a bakin ma'abota gaskiya tare da martani ga barnar da suka shayar da mutane da sunan addini, ko da sunan Sunnah, ko da sunan Salafiyyanci, shi tafarkin Sunnah na gaskiya yana nan dama tun tuni yana rabewa tsakanin gaskiya da karya, ba yau aka fara ba, kuma Ahlus- Sunnah na gaskiya Allah ne yake musu yaki, kuma shine yake daukaka ambaton su, ba don komai ba, sai don sun tsaya akan turba ta gaskiya, kuma sun wadatu da ita daga barin duk wani tafarki da yake karkatacce yayi hannun riga da tafarkin gaskiya.

Ya Allah ka raya mu akan Musulunci da Sunnah, kuma ka dauki ranmu muna kan wannan tafarki na gaskiya.

أمين ثالث يعقوب

30 / 01 / 1440
10 / 10 / 2018

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!