RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO ! (01) - Hassan Al- Banna shine ya assasa kungiyar Ikhwan wanda shi ya mutu tun shekarar turawa na alif da dari tara da arba'in da tara (1949) kawo yanzu yana da shekaru saba'in da daya (71) a kasa . - Wannan kungiya ci gaba ne ga fikirorin khawarijawa (bayanai zasu fito in sha Allah) kuma tana da tarbiyya ne ta Sufaye tare da tsare-tsare na kungiyanci na siyasa, a karon farko ta bayyana ne ba tare da fitowa a rigar Sunnah ba, wanda hakan ya sa mutane da yawa basu karbe ta ba, bal sunyi inkarin ta musamman a yankunan Saudiyyah, Bahrain, Qatar, Kuwait, Imarat, Oman.. Musamman saboda rashin lazimtar su ga Sunnah! - Sai dai ta samu karbuwa a tsakanin wayayyun 'yan Boko zalla haka kuma 'yan inna rududu daga cikin gama-garin mutane sun tasirantu da ita (ja ya fado ja ya dauka kenan!). - Daga cikin ababen da suka yaudari mutane dashi shine bayyanar da yaki da Yahudawa abokan adawa (Zionist), tare da rufe kofar martani ga ...
المشاركات الشائعة من هذه المدونة
MAGANA AKAN 'YAN BID'AH DA MASU KARKATACCEN MANHAJI BA GIBA (GULMA) BACE ❁❁❁❁❁❁ ــــــ ❁❁❁❁❁❁ ـــــ ❁❁❁❁❁❁ Fatawar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen (Allah ya jikansa) : ❍ الشيخ محمد بن صالح العثيمين : السّـؤال : الكلام في أهل البدع ، مثل أن يقال مثلاً: أنهم يؤولون الآيات والأحاديث، ويقولون: يفعلون كذا وكذا.. أيعتبر هذا غيبة إذا كان بين الطلبة ؟ Tambaya: Magana akan 'yan Bid'ah, kamar misali ace: sunayin tawilin ayoyi da hadisai, kuma suna aikata kaza da kaza, shin wannan ana daukarsa giba (gulma) ce in ya kasance a tsakanin dalubai ne? »» الجواب: الكلام في أهل البدع ومن عندهم أفكار غير سليمة أو منهج غير مستقيم، هذا من النصيحة وليس من الغيبة ، بل هو من النصيحة لله ولكتابه ولرسوله وللمسلمين ، فإذا رأينا أحداً مبتدعاً ينشر بدعته ، فعلينا أن نبين أنه مبتدع حتى يسلم الناس من شره ، وإذا رأينا شخصاً عنده أفكار تخالف ما كان عليه السلف فعلينا أن نبين ذلك حتى لا يغتر الناس به ، Amsa: Magana akan 'yan Bid'ah da ma...
MADAKHILAH?!
*SO DA DAMA MAI DA'AWAR NEMAN GASKIYA DA ADALCI YANA AUKAWA CIKIN TAFARKIN AZZALUMAI BA TARE DA YA SANI BA!* So tari zakaga mutane masu son addini da adalci ga bayin Allah, sai suyi rashin dace sai su auka tarkon mabarnata fasikai basu sani ba, yana da kyau ya kai mai amfani da Facebook, ko mai neman gaskiya, ya kasance da gaske gaskiyar kake nema, ba yawan mabiya ko masu yin muwafaka da ra'ayin ka kake nema ba, ya kasance gaskiya ce abar neman ka, kuma da gaske, ka saki ta'assubanci, domin duk mai son ya zama "Salafi" (ma'abocin Sunnah na gaskiya) to sai ya yakice rigar ta'assubanci ya wurga wa shedan kayan sa, domin ta'assubanci ba tufafin mumini bane, kuma wuyan rigar gaskiya da adalci tayi kunci ga fasikai masu bada kariya ga 'yan Bid'ah da son zuciya. Idan ka gane wannan, zaka ga marubuta da yawa masu da'awar su ma'abota Sunnah ne, wani ma zakaji yana cewa shi mabiyin Tafarkin Salaf ne, zaka dinga cin karo da maganganun Ibnu Taimi...
تعليقات
إرسال تعليق