*SHAIKH SĀLEH AL- FAUZAN YANA KARFAFAR SALAFAWAN GASKIYA!*


An tambayi Shaikh Saleh Al- Fauzan -Allah ya kiyaye shi-
Mai tambayar yake cewa:

السؤال:  نحن مجموعة من الشباب ندعوا إلى منهج السلف الصالح، وملازمة الجماعة والسمع والطاعة لولي الأمر في غير المعصية، ونحذر من الجماعات الحزبية، ولكنهم يحذّرون منا، ويسموننا "جامية" فهل نستمر على ما نقوم به؟

Tambaya: mu wasu taro ne na matasa, muna kira zuwa ga Manhajin Al- Salaf Al- Sālih, da kuma lazimtar jama'ah, da sauraro da biyayya ga shuwagabanni a cikin abinda ba sabon Allah bane, kuma muna tsoratarwa daga kungiyoyi "na hizbiyyah", sai dai su suna tsoratarwa daga garemu, kuma suna kiranmu da (lakabin) "Al- Jāmiyyah"  shin zamu ci gaba da abin da mukeyi ne?

الجواب: استمروا واصبروا ولا يهمكم ما يقولون -
 [📖 رسالة وجوب لزوم الجماعة ص38]

Amsa: kuci gaba da abinda kukeyi, kuma kuyi hakuri, kuma kar abinda suke fade ya dame ku, domin ku ba yardar su kuke nema ba, haka kuma ba yabon su kuke nema ba, ku yardar Allah mai daukaka da buwaya kuke nema, so kuke ku bayyana gaskiya, inma wanda zai yarda ya yarda, ko kuma wanda ma zai ki yarda ya ki yarda!

[Risalatu Wujubi Luzum Al- Jamaa'ah page 38].

Kenan zamu fahimci ababe kamar haka a karkashin wannan magana ta Shaikh Sāleh Al- Fauzan -Allah ya kiyaye shi- :

1: Matasa ne suka dauki ragamar da'awa wacce ta ginu akan asullai na addinin Musulman farko, sannan suka tunkari Bid'o'in da suka addabi Musulmai a zamanin da suke rayuwa cikinsa, musamman fito na fito da akewa Shuwagabanni wanda ambaton kura-kuran su a bainar jama'a shine mataki na farko, sai mataki na biyu zagin su da fasikantar dasu, sai mataki na uku kambama kura-kuran nasu a idon gama-garin mutane musamman masu kishin addini, sai kuma kafirta wa'yannan shuwagabanni da kudurta cewa sunyi ridda, biyayya garesu kuma ta fadi ta dalilin haka, sai mataki na yi musu bore, da halasta jinin su, da yunkurin kifar da gwamnatin nasu, wanda hakan ke haddasa lalacewar miliyan amma daya bata gyaru ba, hakan yana sanya a hukunta kafirci ga duk wanda bai yarda cewa wa'yannan shuwagabanni kafirai ne wa'yanda sukayi ridda ba, sai halasta jinin duk wanda bai yarda da Mazhabar su ba ta Khawarijawa... A takaice kenan.

To wa'yanda suke kokarin bayanin Mazhabar Salaf akan mu'amala da shuwagabanni da hana cin zarafin su, da hana fito na fito garesu, da karanta Hadisan sauraro da da'a da haramcin kashe shuwagabanni, sai 'yan Ikhwan suce: wa'yannan sune "Jaamiyyah" (ana nasabta su zuwa ga Shaikh Muhammad Bin Aliy Amān Al- Jāmiy, daya daga Bijiman Malaman Jami'ar Musulunci dake Madeenah a Saudi Arabia)  wanda yayi raddi ga shubuhohin khawarijawa 'yan Ikhwan yayi bayanin Mazhabar Salaf akan mu'amala da shuwagabanni da rashin fito na fito garesu) ko suce "Malaman gwamnati"  da sauran su.

Sai Bid'ar rarrabuwar Musulmai zuwa ga kungiyoyi mabanbanta kowacce kungiya akwai wajajen da tayi hannun riga da Tafarkin Musulman farko, kuma tana alfahari da ayyukan da takeyi na sabawa tafarkin Sunnah na gaskiya wanda shine cikakken ma'anar "Hizbiyyah" din, wato kungiyanci.

2: Shaikh Fauzan ya yarda da aci gaba da fasa kwai , aci gaba da bayanin gaskiya , aci gaba da nunawa mutane aslin Sunnah din, wacce take bayanin mu'amala tsakanin talakawa da shuwagabanni, sannan ya yarda da aci gaba da tsoratar da mutane daga kungiyoyin nan na "hizbiyyah" !

3: Shaikh yana umurni ga matasa suyi hakuri kar su gaza don wasu na sukar su ko suna tsoratarwa daga garesu, kar hakan ya dakatar dasu daga fayyace gaskiya da sukeyi, domin ba yardar kowa suke bukata ba in ba Allah ba.

4: Ashe masu tsoratarwa daga ababen da suka gabata sune suke tare da Malaman Salafiyyah ta gaskiya, dukda ana batanci garesu ana fadin ababen da basu fada ba!

Muna rokon Allah ya taimaki bayin sa na gari Salafawan gaskiya kamar yadda yake taimakon Manzannin sa da ma'abota Imani da tsayuwa akan tafarkin sa madaidaici.

Ga website din Shaikh Sāleh Al- Fauzan nan, -Allah ya kiyaye shi- domin kowa ya fa'idantu daga taskar Ilimi da Allah ya hore masa:

⤵⤵⤵

https://www.alfawzan.af.org.sa/en

Ga website din Shaikh Muhammad Bin Aliy Amān Al- Jāmiy nan, -Allah ya jikan sa- domin kowa ya fa'idantu daga taskar Ilimi da Allah ya hore masa:

⤵⤵⤵

https://www.eljame.com/?m=1

Dan uwanku a musulunci da Sunnah:

أمين ثالث يعقوب

04 / 02 / 1440
14 / 10 / 2018

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!