DAGA CIKIN LITTAFAN 'YAN GWAGWARMAYA, A GUJE SU! - AMINU THALITH YA'QUB
DAGA CIKIN LITTAFAN ‘YAN GWAGWARMAYA, A GUJE SU!
بسم الله الرحمن الرحيم، وصلى اللهم وسلم وبارك على النبي الكريم وعلى آله وصحبه أجمعين، ومن تمسك بسنته وسار على نهجه إلى يوم الدين.
Bayan haka Assalāmu ‘alaykum warahmatullāhi wabarakātuh.
To da farko dai bayan godiya ga Allah madaukaki, wannan gabatarwa ce a kan littafan ‘yan gwagwarmaya wanda aka nemi mu ambata su, bayan karanta rubutun Dr. Muhammad Sabi’u Sulaimān da kuma bayan sauraron bayanai a kan Kungiyar Sururiyyah gabatarwar Ustadh Huzaifah Aminu Daurawa da Dr. Isma’il Aliy Yahya Maikwano, Allah ya kiyaye su -dukkanin su guda ukun suna karatu yanzu haka a Jami’ar Musulunci ta Madeenah, Allah ya datar da su da mu ma baki daya.
Mai comment -Allah ya datar da shi da mu baki daya- yana cewa:
“Jazakallahu khairan, bayanan da dalibai da malamai ke bukata kenan, domin matsalar da ake fama da shi kenan ga yawancin masu daawar sunnah, yanzu ma muna cikin tattaunawa da wani dalibin sunnah game tasirantuwarsa da wadannan malaman mabarnata”.
“Zai yi kyau ka fada sunan litattafansu domin mutane sun fi rike sunnan littafi akan sunan mai littafin”
Ba tare da tsawaitawa ba, naga muhimmancin aikata hakan, kuma ina fatan wa’yannan ‘yan uwa suci gaba da wayar da kan ‘yan uwa Musulmai game da wa’yannan kungiyoyi da hadurran su, kamar yadda suka tarar Malaman Sunnah wa’yanda suka tsayu a kan Manhajin magabata na kwarai suke yi a cikin Jami’o’in Saudiyyah ko a wajen su, ko ma a Kasar Misra da makamantan wajeje da Malaman Sunnah suke .
Nayi farin ciki da wannan comments din guda biyu matuka, kuma ina fatan Allah ya sanya tattaunawar dake gudana tsakanin wa’yannan ‘yan uwa biyu ta fita da natija mai kyau, kuma ya azurta kowannen mu da karbar gaskiya a lokacin da ta bayyana, kuma muyi watsi da akasin ta a duk lokacin da ilimi ya isa gare mu, kuma kar ya kama mu da laifn da bamu sani ba, da wanda mukayi a kan kuskure ko mantuwa.
BAYAN HAKA
Shaikh Abdulsalām Bin Sālim Al- Suhaimiy (Malami a Jami’ar Musulunci ta Madeenah, kuma daya daga cikin masu karantarwa a Masallacin Madeenah mai daraja) Allah ya kiyaye shi yana cewa a cikin littafin sa mai suna
“فكر التكفير قديما وحديثا وتبرئة أتباع مذهب السلف من الغلو والفكر المنحرف”
’Ma'ana: littafi ne da yake bayani a kan “Fikirar kafirtawa, a da can da kuma yanzu, da kuma barrantar mabiya Manhajin magabata daga guluwwi -wuce gona da iri- da kuma karkataccen tunani”
“فكر التكفير قديما وحديثا وتبرئة أتباع مذهب السلف من الغلو والفكر المنحرف”
’Ma'ana: littafi ne da yake bayani a kan “Fikirar kafirtawa, a da can da kuma yanzu, da kuma barrantar mabiya Manhajin magabata daga guluwwi -wuce gona da iri- da kuma karkataccen tunani”
Yana cewa a cikin wannan littafin (daga shafi na 91 zuwa na 29) :
وإن من أسباب وجود هذا الفكر في هذا العصر: هو وجود الكثير من المؤلفات المعاصرة، والتي اتخذت مسميات عديدة، وأساليب متنوعة، لكنها في النهاية إنما هي خلاصة للفكر الخارجي التكفيري
Ma’ana: kuma yana daga cikin sabubban samuwar wannan fikira a cikin wannan zamanin: shine samuwar da yawa na daga wallafe-wallafe na wannan zamanin, wa’yanda suke dauke da sunaye da dama, da hanyoyin isar da sako iri-iri, sai dai kuma a karshe abin sani kawai shine su (wa’yannan littafai) takaicewa ne ga fikira ta khawarijanci da kafirtawa
وهذه المؤلفات تتبع لفكر جماعات إسلامية ذات تنظيمات سرية، وتتسم دعوتها بالتكتم والخفاء والتلون وعدم إظهار حقيقة أمرها
Kuma wa’yannan littafai bibiya ne ga fikirorin kungiyoyin musulunci wa’yanda suke da tsare-tsare na sirri, wa’yanda da’awar su take siffantuwa da boye-boye, da canza launoni, da rashin bayyana hakikanin lamurran su.
وإن من أعظم ما ابتلي به المسلمون في هذا العصر من هذه الجماعات: جماعة الإخوان المسلمين بتوجهاتها الثلاث:
البنائية: نسبة لمؤسس الجماعة حسن البنا
والقطبية: نسبة لسيد قطب
والسرورية: نسبة لمحمد سرور.
Kuma lallai daga cikin mafi girman ibtila’in da aka jarabci musulmai da shi a wannan zamanin sune wa’yannan kungiyoyin: Kungiyar Al- Ikhwān-ul Muslimoon (Suna kiran ta da Hausa: kungiyar 'yan uwa Musulmi, ko 'yan Brothers) , da matafiyar ta guda uku:
Al- Banna’iyyah: jinginuwa zuwa ga wanda ya assasa kungiyar, Hassanu Al- Bannā
Al- Qutubiyyah: jinginuwa zuwa ga Sayyid Qutub
Al- Sururiyyah: jinginuwa zuwa ga Muhammad Suroor
Haka kuma yana cewa (a cikin shafi na 95) :
وإن سيد قطب يعتبر ممن أحيا فكر الخوارج التكفيري في هذا العصر؛ ولهذا تعتبر مؤلفاته هي الأخطر؛ لأنها المرجع التي يرجع إليها المتأثرون بهذا الفكر من أبناء هذه البلاد وغيرها؛ لأنه قلّ أن تخلو مكتبة عامة أو خاصة من كتب سيد قطب، بل قل أن توجد مدرسة متوسطة، أو ثانوية للبنين أو البنات إلا وتوجد بها كتب هذا الرجل، بل يحث الطلاب على الرجوع إليها والاستفادة منها، وقلّ أن يوجد من العلماء من يحذر من الأخطاء التي حوتها مؤلفاته،
Yake cewa: kuma lallai Sayyid Qutub yana daya daga cikin wa’yanda suka raya fikirar Khawarijawa ta kafirtawa a wannan zamanin; kuma saboda haka ne ma ake daukan littafan sa a matsayin mafiya hatsari; domin su ne makoma wacce wa’yanda suka tasirantu da wannan fikirar daga cikin ‘ya’yan wannan kasa (yana nufin Saudiyyah) da ma wasu kasashen daban suke komawa gare ta; domin ba’a samu wata maktaba(library) ta kowa da kowa ko kebantacciya wacce babu littafan Sayyid Qutub a cikin ta sai kadan, bal ma zaiyi wuya a samu makarantar junior secondary ko senior secondary ta yara maza ko ta ‘ya’ya mata wacce za’a ce babu littafan Sayyid Qutub a cikin ta sai dai kadan, haka zaiyi wuya a samu wata kwaleji ko wata Jami’ah face sai an samu littafan wannan mutumin sai dai kadan, bal ma ana kwadaitar wa a kan komawa zuwa wa’yannan littafai, da fa’idantuwa daga gare su, kuma ba’a samun mai tsoratarwa a kan kura-kuran da ke kunshe cikin littafan sa dai kadan ne ake samu,
بل إن قادة الجماعات المتطرفة ومنظريها جعلوا كتب سيد هي الأساس التي يربى عليها الشباب، وهناك إرهاب فكري منظم لدى الجماعات الحزبية يتضمن محاربة كل من ينتقد فكر الجماعات الحزبية عموما، وفكر سيد قطب خصوصا.
وهذه الجماعات بتوجهاتها الثلاث انتهجت منهجا يخالف منهج السلف في أبواب العلم والعمل
Bal ma lallai shuwagabannin kungiyoyin ta’addanci da masu tsara su sun sanya littafan Sayyid su ne ginshikai wa’yanda suke tarbiyyantar da matasa da su, kuma akwai ta’addanci na fikira wanda kungiyoyin hizbiyyah suka tsara wanda yake kunshe da yakar duk wanda yake raddi ga kungiyoyin hizbiyyah a game, da kuma fikirar Sayyid Qutub a kebe.
Kuma wa’yannan kungiyoyin da matafiyar su guda uku sun bi wani Manhaji wanda ya saba wa Manhajin Salaf a cikin babuka na ilimi da aiki
DAGA CIKIN LITTAFAN ‘YAN GWAGWARMAYA, A GUJE SU!
Shaikh Abdulsalām Al- Suhaimiy har wa yau – Allah ya kiyaye shi ya tabbatar da shi da mu gabaki daya a kan turba ta gaskiya, da kuma kasancewa tare da ma’abota gaskiya da rabewa daga maha’inta kuma ya karbi ran mu a kan haka. Amin
Yana cewa (daga shafi na 109 zuwa na 110) :
Yana mai hikaito maganar Dr. Muhammad Al- ‘Uwayn:
من كتب هذا الفكر مثلا تلك التي كان الطيبون يهدونها لنا في ختام العام الدراسي، وكنا نحفظ صفحات منها دون وعي [¹] : “معالم في الطريق” لسيد قطب، و “في ظلال القرآن” له أيضا، و “الإسلام بين جهل أبنائه وعجز علمائه” لعبد القادر العودة ، و “الموسوعة الحركية” لفتحي يكن، و “مذكرات الدعوة والداعية” لحسن البنا، و “العدالة الإجتماعية في الإسلام” لسيد قطب، و “جاهلية القرن العشرين” لمحمد قطب، و “قبسات من الرسول” له أيضا، و “طفل من القرية” لسيد قطب، و “ماذا خسر العالم بانحطاط العالم الإسلامي” لأبي الحسن الندوي، و “الجهاد” لأبي الأعلى المودودي، و “جهاد الإخوان المسلمين في فلسطين” لكامل الشريف، و “ملامح الانقلاب الإسلامي في حياة عمر بن عبد العزيز” للدكتور عماد الدين خليل، و “الحجاب” لأبي الأعلى المودودي، و “الحكم الإسلامي” له أيضا، ثم روايات نجيب الكيلاني، وما ماثلها.
Yace:
Daga cikin littafai na wannan fikira a babin misali shine wa’yannan littafan da mutanen kwaran suke bamu su kyauta, a cikin karshen session na karatu a shekara, kuma mun kasance muna haddace wasu shafuka daga cikin su ba tare da sani ba [¹] : (to a nan ne ya fara ambato sunan littafan) “Ma’ālim Fi Al- Tarēq” na wallafar Sayyid Qutub, da “Fi dhilāli Al- Qur’ān”shima wallafar sa ne, da Al- Islāmu baina jahli Abnā’ihi wa ajzi ‘Ulamā’ihiwallafar Abdulqādir Al- ‘Audah da “Al- Mausoo’atu Al- Harakiyyah” wallafar Fathiy Yakan, da “Mudhakkirātu Al- Da’awah Wa Al- Dā’iyah” wallafar Hassan Al- Banna, da “Al- ‘adālah Al- Ijtimā’iyyah fiy Al- Islām” wallafar Sayyid Qutub, da “Jāhiliyyatu Al- Qarni Al- Ishreen” wallafar Muhammad Qutub, da “Qabasātun Min Al- Rasool” shi ma wallafar sa ne, da “Tiflun Min Al- Qaryah wallafar Sayyid Qutub, da “Madha Khasira Al- ‘Ālam Bi inhitāti Al- ‘Ālami Al- Islāmi” wallafar Abu Al- Hassan Al- Nadawiy, da “Al- Jihād”wallafar Abu Al- A’alā Al- Maudoodiy, da “Jihādu Al- Ikhwāni Al- Muslimeen fiy Filisteen” wallafar Kāmil Al- Shareef, da “Malāmihu Al- Inqilābi Al- Islāmi fi hayāti Umar Bin Abdi- Al- ‘Azeez” wallafar Dr. Imādu Al- Deen Khaleel, da “Al- hijāb” wallafar Abu Al- A’alā Al- Maudoodiy, da “Al- hukmu Al- Islāmiy” shi ma wallafar sa ne, sannan da kuma ruwayoyin Najeeb Al- Kailāniy, da makamantan su.
ثم كتب الفكر الحركي الإسلامي الذي يمنهج للفعل والتغيير، مثل كتب محمد أحمد الراشد: “المسار”، ” المنطلق” ، “العوائق” ، “البوارق” .
Sa’annan sai littaafan fikirar gwagwarmaya ta Musulunci wacce take tafiya a kan aiki da canji (kamar yana nufin canjin shuwagabanni ta dadi ko ta bala’i, domin juyin mulki yana daga cikin manhajin su), misalin littafan Muhammad Ahmad Al- Rāshid:“Al- Masāru” , “Al- Muntaliq” , “Al- ‘Awā’iq” , “Al- Bawāriq” .
(¹) Shaikh Abdulsalām Bin Sālim Al- Suhaimiy (Allah ya kiyaye shi) yake cewa a cikin hashiya mai lamba ta daya (1) shafi na dari da tara (109) :
أوافق الدكتور في جميع ما ذكر، وأنا ممن سلم له بعض هذه المؤلفات التي ذكرها، وسلمت لغيري من الزملاء قبلي وبعدي، والتي توزّع في ختام كل عام دراسي. اهـ
Yace:
Nayi muwafaka da Dakta a cikin dukkan abbaben da ya ambata, kuma nima ina cikin wa’yanda aka baiwa wani sashe daga cikin littafan nan wa’yanda ya ambata su, kuma an baiwa wasu na daga cikin abokan karatu kafin ni da bayan ni, kuma su din ake rarrabawa a karshen kowane session na karatu a shekara.
Mun kawo karshen ambaton wasu daga cikin littafan ‘yan gwagwarmaya daga Mutane biyu wa’yanda Allah ya tseratarda su daga farautar ‘yan Ikhwan.
Zaiyi kyau mai karatu ya saurari kuma wata muhadara wacce akayi mata take da:
دعوة الإخوان المسلمين حقيقتها وخطرها، لمعالي الشيخ أ.د سليمان أبا الخيل -حفظه الله تعالى
Ma’ana:
DA’AWAR KUNGIYAR AL- IKHWANU AL- MUSLIMOON(Muslim Brotherhood), HAKIKANINTA DA HADARINTA!
Muhadarah ce da Shaikh Dr. Sulaiman Bin Abdillāh Abal Khayl, V.C. na Imam Muhammad Bin Sa’ud University dake Riyadh Saudi Arabia, sannan kuma daya daga cikin Manyan Malaman kasar Saudiyyah -Allah ya kiyaye su-
Ya gabatar a masallacin Qubah dake Madinar Manzon Allah Sallallāhu ‘alaihi wasallam.
Yana da kyau a saurare ta, ya ambaci strategies din da suka bi wajen farautar Matasan Kasar Saudiyyah da ma wasu kasashen wajen ta, kuma shi ma ya ambaci irin yadda suka so su farauce shi ta hanyar bashi kyautar irin wa’yannan littafai na ‘yan gwagwarmaya, zaka iya saurare kuma zaka iya downloading zuwa na’urar ka kai tsaye ta wannan link din dake kasa
👇🏼👇🏼👇🏼
http://bit.ly/2GEoF7r
A nan ne muka kawo karshen wannan yanki, muna fatan Allah ya datar da ku da mu gabaki daya ya saukake mana hanyoyin riskar gaskiya, kuma ya saukake mana kasantuwa tare da gaskiya da ma’abotan ta, kuma ya saukake mana rabewa daga karya da ma’abotan ta, lallai shi majibincin haka ne kuma mai cikakken iko a kan sa, ga mai bukatar karin bayanai a kan raddojin Malamai da tsoratarwar su daga kungiyar Ikhwan makyankyashiyar kungiyoyin ta’addanci na wannan zamani, da ma wasu ayyanannu daga jagororin ta da masu kira zuwa gareta, daga bakin Manyan Malaman Sunnah, tun daga su Shaikh Bin Bāz, Albani, Muqbil, Ibnu Uthaymeen, Sāleh Al- Fauzān, Sāleh Al- Luhaydān, Rabee’u Al- Madkhaliy, Muhammad Al- Madkhaliy, Muhammad Amān Al- Jāmiy, da shauran Malamai wa’yanda zaku ji muryoyin su wajen murya tananin da biyar (85) in sha Allahu, sai kabi wannan link dake kasa don sauraro ko saukewa (downloading) a na’urar ka
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
http://ar.alnahj.net/tree/254
المراجع:
١ – (فكر التكفير قديما وحديثا وتبرئة أتباع مذهب السلف من الغلو والفكر المنخرف، ص ٩١ ، ٩٢ ، ٩٥ ، ١٠٩ ، ١١٠… الشيخ عبد السلام بن سالم السحيمي الأستاذ المشارك بقسم الفقه بكلية الشريعة بالجامعة الإسلامية بالمدينة المنورة) .
٢ – موقع ميراث الأنبياء “محاضرة بعنوان دعوة الإخوان المسلمين حقيقتها وخطرها لمعالي الشيخ أ.د سليمان أبا الخيل -حفظه الله-“
٣ – موقع النهج الواضح “التحذير من جماعة الإخوان المسلمين”
Dan uwan ku a musulunci da Sunnah:
أمين ثالث يعقوب
05 / 06 / 1440
11 / 02 / 2019
تعليقات
إرسال تعليق