TABBAS FADIN GASKIYA MUSAMMAN WACCE TA SABA WA MUTANE TANA JANYO WA MUTUM:
1 - kiyayya/bakin jini
2 - rashin yardar mutane
3 - fushin mutane
4 - bata suna da sura.
AMMA IN KAYI DON ALLAH TANA JANYO :
1 - soyayyar mahaliccin mutane
2 - kusanci ga Allah da muminai
3 - Yardar Allah mahaliccin mutane
4 - Bayyanar gaskiya a asalin surar ta
5 - Bayyanar karya a asalin surar ta
6 - Fita daga sahun fasikai
7 - Cike alkawarin da ka dauka na Allah cewa zaka bayyana gaskiya kuma ba zaka boye ba
8 - Tsira daga tsinuwar Allah da Mala'iku da Mutane da dabbobi da kifayen dake cikin ruwa
9 - Tsira daga linzamin jahannama wanda za'a sanyawa wa'yanda suka ki bayyana gaskiya
10 - Samun alkawarin Allah na taimakon sa, da tseratarwar sa idan ya tashi kama azzalumai tun a nan duniya, da samun Aljannar sa wacce ita ce masaukin bayin sa ma'abota tsayuwa da gaskiya
KIN BAYYANA GASKIYA KUMA YANA JANYO :
1 - La'antar Allah da la'antar masu la'anta
2 - Koyi da ashararan mutane Yahudawa
3 - Bacewar addinin gaskiya da cakudewar sa ga wa'yanda basuda galihu na tantance gaskiya da karya
4 - Dawowar jahilci da yawaitar mabarnata da nishadin su a kafafen yada tsiyataku, bal harma a wajaje masu girma
5 - Kiyayya ga ma'abota gaskiya da kulla fada dasu
6 - Rashin hutu tun a nan gidan duniya, domin a kowane lokaci ma'abota gaskiya zasu ta martani ga kifaffu suna tona asirin su da yaye labulen da suke lullube sabanin gaskiya dashi
7 - Tsoratarwa da mummunar sheda daga ma'abota gaskiya tun da ran su, dama bayan mutuwar su
8 - Barrantar ma'abota gaskiya daga kangararru da ran su har ma bayan mutuwar su
9 - Nadama a yayin barin duniya, kamar yadda wasu jagororin Bid'ah suka yi a yayin mutuwar su, amma idan wasu ayyanannu basu yi ba baya kore hakan, bal nadamar takan iya aukuwa ba tare da wa'yanda suke halarce sun sani ba
10 - Tashi a sawun makiya gaskiya a ranar tashin kiyama, da duhun fuska, lallai a ranar Al- kiyamah akwai rini wanda za'ayi ga ma'abota gaskiya wanda shine hasken fuska, su kuma ma'abota karya za'a rina fuskar su tayi baki
**** **** ****
Muna rokon Allah ya sanya mu cikin ma'abota gaskiya kuma yasa rahamar sa ta kewaye mu, ba don ayyukan mu ba, kuma muna rokon sa ya rufa mana asiri ranar da za'a banbance a rarrabe rarrabewa ta hakika ya tashe mu cikin masu hasken fuska kamar yadda muke kokarin kamanta biyayya ga tafarkin su a nan duniya, kuma ya nesanta mu daga masu bakin fuska kamar yadda muke kokarin fallashe tafarkin su da nisantar su da rabewa daga gare su tun anan duniya.
أمين ثالث يعقوب
14 / 12 / 1440
15 / 08 / 2019

تعليقات
إرسال تعليق