ASSASA KUNGIYOYI BAYA CIKIN ABINDA ADDINI YA YARDA DASHI!
Shaikh Sālih Al- Fauzan Allah ya kiyaye shi yana cewa:
التفرق ليس من الدين ، لأن الدين أمرنا بالاجتماع وأن نكون جماعة واحدة وأمة واحدة على عقيدة التوحيد وعلى متابعة الرسول ﷺ،
Rarrabuwa (cikin kungiyoyi) baya daga addini, domin addini ya umurcemu da haduwa, kuma mu kasance jama'ah guda daya, al'ummah guda daya, akan Aqidah ta Tauhidi, da biyayya ga Manzo Sallallāhu 'alayhi wasallam,
Nace: anan Shaikh ya bayyana mana akan abinda ya zama wajibi Musulmi su hadu a karkashinsa, a karkashin Aqida ta Tauhidi, ba a karkashin kungiyoyi ba, masu kungiya sun fahimci kalmar jama'ah a baude, shiyasa karan kansu suke akan dimuwa da rikici, a sahun 'yan kungiya zaka taras har da wanda yake akan Aqidar mu'utazilanci kuma sun san da haka sama da shekaru goma sha, amma har yanzu suna kirga wannan bamu'tazile a cikin Ahlus Sunnah, Allah ya kiyaye mu daga son zuciya da bata.
يقول تعالى {إنَّ هَذه أمَّتُكم أمَّةً وَاحدَة وَأنا رَبُكم فَاعبُدُون} [الأنبياء :92] . يقول تعالى {وَاعتَصِمُوا بحبل اللَّه جَميعاً وَلا تَّفرَّقُوا} [آل عمران : 103] وقال سبحانه وتعالى {إنَّ الذينَ فَرَّقُوا دينهم وَكانُوا شِيَعَاً لستَ مِنْهُم في شَئ إنَما أمْرُهُم إلى الله ثُمَّ ينبئهم بِمَا كانوا يَفعَلُون} [الأنعام : 159]
Kuma Allah madaukaki yana cewa:
{Kuma lallai wannan addinin naku addini ne guda daya, kuma nine ubangijinku don haka ku bauta min}
Ibnu Katheer yana cewa: Hasanul Basri yana fadi a karkashin wannan aya:
بين لهم ما يتقون وما يأتون ، ثم قال: (إن هذه أمتكم أمة واحدة) أي سنتكم سنة واحدة.
Allah ya bayyana masu abinda zasu kiyaye, da kuma abinda zasu aikata, sannan yace: (إن هذه أمتكم أمة واحدة) ma'ana: lallai wannan tafarkinku tafarki ne guda daya.
Kuma Allah yana cewa: {kuma kuyi riko da alkawarin Allah gabaki daya kuma karku rarraba} kamar yadda Ibnu Katheer ya fada, yace Alqur'ani kenan, sannan Al-Tabariy ya ruwaito a tafsirinsa cewa:
وتمسكوا بدين الله الذي أمركم به، وعهده الذي عهده إليكم في كتابه إليكم، من الألفة والإجتماع على كلمة الحق، والتسليم لأمر الله.
Kuma kuyi riko da addinin Allah wanda yayi maku umurni dashi, da alkawarinsa da ya kulla daku a cikin littafinsa, na 'yan uwantaka da haduwa akan kalma ta gaskiya, da sallamawa umurnin Allah.
Nace: wannan aya ce da ma'abota kungiyoyi suke labewa suna cin kasuwancinsu da ita, kuma a hakika martani take musu, sai dai suna jahiltar da kansu ne don su rudar da gama-garin mutane da masu rauni da jahilai, matsalarsu in kace suzo a karanta fassarar magabata zakaga kawai suna kange wannan kofa basa son a bude ta ko kadan, sun fi amincewa da fassararsu sabuwa wacce take ta son zuciya ce, Allah yayi mana kariya daga son zuciya.
فديننا دين الجماعة ودين الألفة والاجتماع ، والتفرق ليس من الدين ،
Shaikh Fauzan yaci gaba da cewa: addinin mu fa jama'ah daya ce, kuma addinin 'yan uwantaka da haduwa, sannan rarrabuwa (cikin kungiyoyi) baya cikin addini,
فتعدد الجماعات هذه ليس من الدين ، لأن الدين يأمرنا أن نكون جماعة واحدة
Saboda haka karkasuwar kungiyoyi baya cikin addini, domin addini yana umurtar mu ne da mu kasance jama'ah daya
والنبي ﷺ ،يقول : (مثل المؤمنين في توادهم وتراحمهم وتعاطفهم كمثل الجسد الواحد)
Kuma Annabi Sallallāhu 'alayhi wasallam yana cewa: (misalin muminai a soyayyar su ga juna, da tausayawa junansu, da taimakon junansu, kamar gangar jiki guda daya ne)
فمعلوم أن البنيان وأن الجسد شئ واحد متماسك ليس فيه تفرق ، لأن البنيان إذا تفرق سقط ، كذلك الجسم إذا تفرق فقد الحياة ،
Kuma sananne ne cewa shi gini da kuma gangar jiki, abu ne guda daya, mai karfafar juna, ba'a samun rarrabuwa cikinsa, domin shi gini in rabuwa ta samu garesa faduwa yake, haka in gangar jiki ta rarrabu an rasa rayuwa,
فلا بد من الاجتماع وأن نكون جماعة واحدة أساسها التوحيد ومنهجها دعوة الرسول ﷺ ، ...
Yace: babu makawa sai an samu haduwa, kuma mu kasance jama'ah guda daya, tushen wannan jama'ah ya kasance Tauhidi, kuma manhajinta ya kasance da'awar Manzon Allah sallallāhu 'alayhi wasallam,
Zuwa inda Shaikh Fauzan yake cewa:
وهذا التفرق الحاصل على الساحةاليوم لا يقره دين الإسلام، بل ينهى عنه أشد النهي ويأمر بالاجتماع على عقيدة التوحيد وعلى منهج الإسلام، جماعة واحدة وأمة واحدة كما أمرنا الله سبحانه وتعالى بذلك .
Kuma wannan rarrabuwa da aka samu a fadin duniya a yau, addinin musulunci bai tabbatar(yadda) dashi ba, sai dai ma yayi hani ne daga gareshi, mafi tsaurin hani, kuma yayi umurni da haduwa ne akan Aqida ta Tauhidi, sannan akan tafarki na Musulunci, jama'ah daya, kuma al'umma daya kamar yadda Allah mai tsarki da daukaka ya umurcemu da hakan.
والتفرق وتعدد الجماعات إنما هو من كيد شياطين الجن والإنس لهذه الأمة، فما زال الكفار والمنافقون من قديم الزمان يدسون الدسائس لتفريق الأمة ،
Kuma rarrabuwa da samuwar kungiyoyi mabanbanta, abin sani kawai wannan yazo ne daga makircin shedanun aljanu da mutane ga wannan al'ummar, kafirai da munafukai basu gushe ba suna yin dashe-dashe domin rarraba wannan al'umma,
أقول : وفي الجملة فعلماء الإسلام وعلماء السنة في السابق واللاحق لايجيزون هذا التفرق ولا هذا التحزب ولا هذه الجماعات المختلفة في مناهجها وعقائدها ؛
Ina cewa: kuma a dunkule, lallai malaman Musulunci kuma Malaman Sunnah wa'yanda suka gabata da mamaya bayansu basa halasta wannan rarrabuwar da wannan kungiyancin, da wa'yannan kungiyoyin wa'yanda suke masu sabani ne a Manhajojinsu da Aqidunsu;
لأن الله قد حرم ذلك وكذلك رسوله صلى الله عليه وسلم ، والأدلة كثيرة وقد سبق سردها في مواطنها .
[انظر كتاب مراجعات في فقه الواقع السياسي والفكري على ضوء الكتاب والسنة، للدكتور عبد الله بن محمد الرفاعي ص ٤٤ - ٤٥].
Domin lallai Allah ya haramta hakan, sannan haka ma Manzon sa Sallalallahu 'alaihi wasallama ya haramta hakan, kuma dalilai suna nan da yawa, kuma ambatonsu ya gabata a inda suka dace dasu.
[Muraji'āt fee Fiqhi Al- wāqi' Al- siyāsiy na Dr. Abdullāhi Bin Muhammad Al- Rufā'iy, page 44 - 45].
Zaku iya sauke littafin a na'urorin ku don karin fa'idoji ko bincike, kai tsaye ta hanyar bin wannan link din dake kasa
https://archive.org/download/mvxp3/mvxp3.pdf
Dan uwanku a musulunci da Sunnah:
أمين ثالث يعقوب
8/11/1439
22/07/2018

تعليقات
إرسال تعليق