FA'IDOJI DAGA MUHADARAR SHAIKH SĀLEH AL- FAUZĀN 01
A cikin muhadara ta Shaikh Sāleh Al- Fauzān (Allah ya kiyaye shi) mai suna:
((موقف المسلم من الفتن والمظاهرات والثورات))
Ma'ana: ((Matsayar Musulmi a kan fitintinu da zanga-zanga da juyin juya hali))
Wacce aka buga ta a matsayin littafi kuma ya bayar da izinin buga ta a Ashirin da hudu ga watan Jumādal Ula shekara ta alif da dari hudu da talatin da biyu (24/05/1432) bayan hijira.
Yayi wasu maganganu wa'yanda suka ja hankali na kamar haka:
(1) "فهذه الفتن فيها خير؛ لأنها تميز بين الكفر والإيمان وتبين أهل النفاق والمخادعات وتكشف حقيقتهم فلا يغتر بهم بل يحذر منهم، هذه حكمة الله سبحانه وتعالى". ص ١١
Ma'ana: "wa'yannan fitintinun akwai alkhairi a cikin su; domin suna banbance tsakanin kafirci da imani, kuma suna bayyana ma'abota munafurci da yaudara kuma suna bankade hakikanin su, ta yadda ba za'a rudu da su ba, bal ma sai dai a tsoratar daga gare su, wannan hikimar Allah ce mai tsarki da daukaka". Shafi na goma sha daya (p. 11)
(2) "لما جاءت هذه الفتن كشفت حقيقة أناس كانوا ينتسبون إلى الدعوة ألى الله، انحازوا إليها وصاروا يشجعون عليها، ويدعون إليها، فتبين أمرهم، وتلك حكمة الله تعالى". ص ١٢
" kuma a lokacin da wa'yannan fitintinu suka zo, sun yaye hakikanin wasu mutane wa'yanda suke jinginuwa zuwa ga kira zuwa ga Allah, sai suka karkata zuwa ga wa'yannan fitintinu, kuma suka kasance suna karfafawa a kan ta, kuma suna kira zuwa gare ta, sai lamarin su ya fito fili, kuma wannan hikimar Allah ce madaukaki". Shafi na goma sha biyu (p. 12)
(3) "نحن لا نعرف حقيقة هؤلاء إلا عند الفتن؛ حيث يظهر ما عندهم، هذه حكمة الله أن يبينهم ويكشف خفاياهم حتى يكون المسلمون على بصيرة، ولا ينخدعون بكل من ادعى أنه يدعوا إلى الله، وليس منهجه منهج رسول الله ﷺ ، أي : الكتاب والسنة كما هو حال الداعية إلى الله عز وجل على بصيرة".
"Mu bamu san hakikanin wa'yannan ba sai a lokacin fitintinu; lokacin da abin da yake tare da su yake bayyana, wannan hikimar Allah ce da yake bayyana su, kuma yake yaye ababen da suke boye wa, har dai Musulmai su kasance a kan basira, kuma ba zasu rudu da duk wani mai ikirarin cewa shi yana kira ne zuwa ga Allah, alhalin Manhajin sa ba Manhaji ne na Manzon Allah Sallallahu 'alayhi wasallama ba, ma'ana: Al-Qur'ani da Sunnah kamar yadda yake hali ne na mai kira zuwa ga tafarkin Allah a kan ilimi".
فلله الحمد والمنة كم كشفت هذه الحوادث من أسرار وأستار كان يتخفى تحتها من يخدع الناس، فبانت حقيقته، وتبين منهم أهل الصبر وأهل الثبات وأهل العلم، فهذه حكمة إلهية". ص ١٣
Yabo ya tabbata ga Allah, kuma falala tasa ce, nawa ne na sirrori da labululluka wa'yanda wa'yannan fitintinu suka yaye, wa'yanda masu yaudarar mutane suke boyewa karkashin su, sai ta bayyanar da hakikanin su, kuma ta banbance daga gare su ma'abota hakuri da tabbatuwa da ilimi, wannan hikima ce ta Allah". Shafi na goma sha uku (p. 13)
(4) "وهم من مسافة بعيدة من خلال الشبكات يدعون المسلمين إلى الاعتصامات وإلى التخريب.. إلخ، ولكن الله رد كيدهم في نحورهم، فالمسلمون في هذه البلاد انتبهوا، والعلماء والخطباء وأئمة المساجد -جزاهم الله خيرا- حذّروا منهم، وكشّفوا عوارهم، فالله -جل وعلا- يكفينا شرهم ويخزيهم، وينصر عباده المؤمنين، كما نصر إخوانهم من قبل". ص ١٥
Kuma sunyi nisa a tafiyar tasu, ta hanyar yanar gizo, suna kiran musulmai zuwa ga yajin aiki da rushe-rushe... Zuwa karshe, sai dai Allah ya mayar musu da kaidin su a kan su, domin musulmai a wannan garuruwan sun fadaku, kuma Malamai da masu hudubobi da limaman masallatai -Allah ya saka musu da alheri- sun tsoratar daga gare su, kuma sun yaye tsiraicin su, Allah ya tsare mu daga sharrukan su, kuma ya tabar da su, kuma ya taimaki bayin sa muminai, kamar yadda ya taimaki 'yan uwan su a can baya". Shafi na goma sha biyar (p. 15)
Za'a iya sauke (downloading) wannan littafin ta links kamar haka:
Shafin Shaikh Sāleh Al- Fauzan, littafi mai lamba arba'in da tara (49)
👇🏼👇🏼👇🏼
https://www.alfawzan.af.org.sa/en/node/75?page=2
Ko kuma ka sauke kai tsaye daga shafin Al- Tauhid 👇🏼👇🏼👇🏼
https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&url=http://www.al-tawhed.net/books/Download.aspx%3FID%3D1151&ved=2ahUKEwjX-trji-7gAhVQXq0KHd3MDXIQFjABegQIARAB&usg=AOvVaw1S1vGZEKYbh0KXDZ03nuIK&cshid=1551895398812
______________________________
A takaice; mun fa'idantu da ababe kamar haka:
(1) Tabbatar da cewa fitintinu suna bayyana halin duk wani wanda ya boye da sunan da'awa zuwa ga tafarkin Allah ko ma wani lakabi wanda yayi dai-dai da hakan, kamar mutum yayi da'awar cewa shi yana kira ne zuwa ga tafarkin Salafiyyah, to idan fitina ta zo ita zata bayyane ma'abota gaskiya daga ma'abota karya a kan da'awar kowane daga cikin su.
(2) Mun fahimci cewa fitintinu suna zama alheri saboda suna banbance tsakanin ma'abota gaskiya da kuma ma'abota karya, wannan wani sashe ne daga cikin bayanin farko, wannan tayi dai-dai da maganar Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah -Allah ya jikan sa- a cikin fadin sa:
"ليس كل من تحلى بالسنة صار سنيا، ولكن الفرق عند الفتن تعرف الرجال، والمعصوم من عصمه الله". [مجموعة الفتاوى ٣١٥/٩].
Ma'ana: "ba dukkanin wanda ya siffantu da Sunnah yake zama ma'aboci Sunnah ba, sai dai rarrabewar ita ce a lokacin fitina zaka san mazaje, kuma wanda Allah ya kare shine a cikin kariya". [Majmu'atu Al- Fatāwā 9/315].
(3) Mun fahimci cewa Malaman gwagwarmaya 'yan da'awar juyin juya hali da masu mara musu baya ba mutanen kirki bane, ko da suna ikirarin su masu kira ne zuwa ga tafarkin Allah, sannan mun fahimci cewa su ma'abota yaudara ne da ha'inci, kuma mun fahimci cewa su makirai ne wa'yanda har Malamai ma suke rokon Allah ya tsare su daga sharrorin su.
(4) Mun fahimci cewa Ma'abota Sunnah na gaskiya kama daga Malamai da masu hudubobi sun tsaya tsayin daka musamman a Kasar Saudiyyah wajen bayyana halin mabarnata da yi musu tonon silili, domin mutane su guji sharrin su kuma su san hadarin makircin su don su guje su, sannan mun fahimci cewa ma'abota gaskiya suna addu'ar Allah ya tabar da masu kira zuwa ga sharri, musamman ma wa'yanda ambaton su ya fito a cikin muhadarar, ma'ana Malaman gwagwarmaya ('yan Ikhwan -Muslim brothers) kenan.
(5) Mun fahimci muhimmancin tsoratarwa daga ire-iren wa'yannan masu kira zuwa ga barnar, wanda tana cikin tsoratarwa daga 'yan Bid'ah wanda asali ne daga cikin asullan Sunnah, wanda kuma maha'inta masu ruwantarwa suke jifan ma'abota sauke wannan aikin da sunan "'yan ghuluwwi" ko "yan bana bakwai" ko "yan kungiyar Salafiyyun" masakai me yasa basa jifan irin Shaikh Al- Fauzan da yake karfafar masu tsayuwa da wannan aikin?!
(6) Mun fahimci cewa ma'abota gaskiya karfafa suke yi ga masu fallasa 'yan Bid'ah da mabarnata, ba kariya sukeyi ga kowane karkatacce ba da sunan "insafi" ma'ana adalci ba! Kamar yadda muke gani daga wa'yanda Shaidan yake taimakar su wajen yakar ma'abota gaskiya da kariya ga mabarnata da nau'ukan su.
أمين ثالث يعقوب
28 / 06 / 1440
06 / 03 / 2019

تعليقات
إرسال تعليق