?MECECE SALAFIYYAR GASKIYA

بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، وعلى آله وصحبه ومن والاه.. وبعد: السلام عليكم ورحمة الله وبركاته.

Abdulmalik Almaimooniy Allah ya jikansa yace:

قال لي الإمام أحمد رحمه الله: «يا أبا الحسن، إياك أن تتكلم في مسألة ليس لك فيها إمام».
انظر مناقب الإمام أحمد (١٧٨) ابن الجوزي.

Yace: Al-Imamu Ahmad yace dani: «Ya kai baban Alhassan, kashedinka, karkayi magana akan wata mas'ala da baka da Jagora(magabaci) acikinta» .
(A duba Manaqibul Imam Ahmad (178) wallafar Ibnu Al- Jawzi).

*MUNA DA JAGORORI MAGABATA NA KWARAI AKAN DA'AWAR MU TA SALAFIYYAR GASKIYA!*

Al-Imāmu Al-Auzā'iy Allah ya jikansa yana cewa:

«اصبر نفسك على السنة، وقف حيث وقف القوم، وقل بما قالوا، وكفّ عما كفوا، واسلك سبيل سلفك الصالح فإنه يسعك ما وسعهم»
(اللالكائي في شرح أصول الاعتقاد ١٥٤/١).

Yace:
«Ka hakurar da kanka akan (ruko da) Sunnah, kuma ka tsaya iyakar inda ma'abota Sunnah(wato Annabi da Sahabbai) suka tsaya, sannan ka furta dai-dai abinda suka furta, kuma ka kame daga abinda suka kame(daga garesa), kuma kabi tafarkin Magabatanka na kwarai, domin kaima abinda ya wadacesu (wato Sunnah kenan) ya wadaceka» .
(Duba Sharhu I'tiqadi Ahlis-Sunnati Wal-Jama'ah na Al- Imām Allalaka'iy 1/154).

Al-Imām Al—Safāriyniy yana cewa:

«ﺍﻟﻤﺮﺍﺩ ﺑﻤﺬﻫﺐ ﺍﻟﺴﻠﻒ :ﻣﺎﻛﺎﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔﺍﻟﻜﺮﺍﻡ ﺭﺿﻮﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺍﻋﻴﺎﻥ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﺣﺴﺎﻥ, ﻭﺍﺗﺒﺎﻋﻬﻢ ﻭﺍﺋﻤﺔﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﻤﻦ ﺷﻬﺪ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻻﻣﺎﻣﺔ ﻭﻋﺮﻑ ﻋﻈﻢ ﺷﺎﻧﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﺗﻠﻘﻰﺍﻟﻨﺎﺱ ﻛﻼﻣﻬﻢ ﺧﻠﻔﺎ ﻋﻦ ﺳﻠﻒ , ﺩﻭﻥ ﻣﻦ ﺭﻣﻲ ﺑﺒﺪﻋﺔ ﺍﻭﺍﺷﺘﻬﺮ ﺑﻠﻘﺐﻏﻴﺮ ﻣﺮﺿﻲ , ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﻭﺍﻟﺮﻭﺍﻓﺾ ﻭﺍﻟﻘﺪﺭﻳﺔ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺌﺔ ﻭﺍﻟﺠﺒﺮﻳﺔ,ﻭﺍﻟﺠﻬﻤﻴﺔ ﻭﺍﻟﻤﻌﺘﺰﻟﺔ ﻭﺍﻟﻜﺮﺍﻣﻴﺔ ﻭﻧﺤﻮ ﻫﺆﻻﺀ» .
(ﻟﻮﺍﻣﻊ ﺍﻻﻧﻮﺍﺭ ﻡ 1ﺹ 20).

 Yace: «Abinda ake nufi da Mazhabar Salaf ita ce: abinda ya kasance Sahabbai (Allah ya kara yarda a garesu) suka tafi a kansa, da Tabi'ai masu daraja wadanda suka bisu da kyautatawa, da wadanda suka biyosu cikin wadanda aka yi musu shaida da shugabanci aka san da girman matsayinsu a addini, mutane na gari suka karbi maganarsu na baya ya karba daga na gaba, banda wanda aka jefeshi da wata bid'ah, ko ya shahara da wani lafazi ba yardajje ba, kamar: Khawarijawa, Rafidhawa, Kadariyyawa, Murji'awa, Jabariyyawa, Jahamiyyawa, Mu'utazilawa, Karramiyyawa, da makamantan wadannan». (Duba Lawami'ul anwar 1/20).
 Kenan Salafiyyah ba kungiya bace, kawai tana nufin tataccen musuluncin da musulman farko sukayi kenan, wanda suka karbeshi a hannun Annabi (S.A.W.) .

*SHIN LAIFI NE IN CE NI BASALAFE(SALAFIY) NE?*

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyah Allah ya jikansa yana cewa:

«لا عيب على من أظهر مذهب السلف، وانتسب إليه، واعتزى إليه، بل يجب قبول ذلك منه بالاتفاق، فإن مذهب السلف لا يكون إلا حقا» (مجموعة الفتاوى ١٤٩/٤).

Yace:
 «Babu aibi ga wanda ya bayyana mazhabin Salaf, sannan ya jingina kansa dashi, sannan ya nasabta kansa dashi, hasali ma ya zama tilas a karbi hakan daga gareshi da ittifakin Malamai, domin shi Mazhabin Salaf ba komai bane sai gaskiya!»
(Duba Majmu'atul Fatawa 4/149).

*FATAWAR BIN BAZ AKAN HUKUNCIN SANYAWA KAI SUNA SALAFIY KO ATHARIY*

سئل الشيخ عبد العزيز بن عبد الله بن باز رحمه الله فيمن تسمى بالسلفي والأثري هل هي تزكية؟

An tambayi Shaikh Bin Bāz Allah ya jikansa akan wanda ya sanya wa kansa Salafi ko Athariy, shin wannan tsarkake kai ne?

فأجاب: أذا كان صادقا أنه أثري أو أنه سلفي لا بأس، مثلما كان السلف يقولون: فلان سلفي، فلان أثري، تزكية لا بد منها تزكية واجبة.
(انظر الأجوبة المفيدة، حاشية الطبعة الثالثة ١٤٢٣، ص ٣٨ - ٣٩).
Sai ya bada amsa da cewa:

«in dai ya kasance da gaske ne shi Basalafe ne, ko shi Athari ne 'Dan naga Sunnah, to ba matsala, kamar dai yadda magabata suke cewa wane Salafi ne ko wane Athariy ne, ai tazkiyah ce wacce ba makawa sai anyi ta, tazkiyyah ce ta tilas» .

(Duba Al- Ajwibatul Mufeedah bugu na uku wallafar Shaikh Jamāl Al- Hārithiy, shafi na 38 zuwa na 39.

*TO 'YAN KUNGIYOYIN NAN MA SALAFAWA NE?!*

An tambayi Shaikh Muqbil Bin Hādiy Al-Wadi'iy Allah ya jikansa: gameda hukuncin jinginuwa ga Salafiyyah da sanyawa kai suna da sunanta,
Sai yace:

«أمر طيب سواء انتسبت إلى السلفية أم إلى السنة، وهذه النسبة ليست كنسبة الحزبيين» .
(شريط القول النقي في معرفة معنى السلفي).

Sai yace: lamari ne mai kyau, dai-dai ne ka nasabta kanka ga Salafiyyah ko ga Sunnah, sannan fa ba irin nasabci irin na 'yan kungiya ba!.

Allah ya jikan Malam, wato 'yan kungiya suna wasa da kalmar Salafiyyah da Sunnah, sai su dauki wacce suke zaton ta dace da manufar kungiyarsu ko bazata ruguje wata ka'ida ta kungiyar ba, sai su lazimceshi, wanda kuma suke ganin bazai yi dai-dai da tafarkin kungiyarsu ba sai su juya baya gareshi kuma su shirya fada da masu aikata shi da kira zuwa gareshi, inama da sun daina yaudarar Mutane da sunan Sunnah suna rushe Sunnar Annabi don su gina Sunnar kungiyarsu!

*Sannan an Tambayi Shaikh Bin Bāz gameda kubutacciyar tawaga sai yace:*

«هم السلفيون، وكل من مشى على طريقة السلف الصالح»
(انظر إتحاف المهرة للشيخ حسن بن قاسم الريمي، ص ١٦).

Yace: sune Salafiyyuna, sannan sune duk wanda ya tafi akan tafarkin Magabata na kwarai!
Ka duba Ithaful Maharrah shafi na 16, wallafar Shaikh Hassan Bin Qasim Al-Reemiy.

*An tambayi Shaikh Sāleh Alfauzan Allah ya kiyaye shi, shin wanda ya sanyawa kansa suna Salafi(Basalafe) shin za'a daukeshi a dan kungiya mai kungiyanci?*

Sai yace:

التسمي بالسلفية إذا كان حقيقة لا بأس به، أما إذا كان مجرد دعوى فإنه لا يجوز له أن يتسمى بالسلفية وهو على غير منهج السلف!
(انظر الأجوبة المفيدة ص ٤٠).

Yace sanyawa kai sunan Salafiyyah in da gaske ne to ba laifi bane, amma in ya kasance tsuran kirari ne kawai to bai halasta ya sanyawa kansa sunan Salafiyyah ba alhali yana kan wani tafarki wanda ba na Salaf ba!
(Duba Al-Ajwibatul Mufeedah shafi na arba'in 40) .

*DA'AWAR SALAFIYYAH SAI DA RARRABEWA!*

Shaikh Bin Baz yana cewa:

وعلى أهل العلم أن يعتنوا بالدعوة إلى الله سبحانه بالتفصيل وإيضاح الإسلام للناس بأدلة الكتاب والسنة، وترغيبهم في الاستقامة عليه، والتواصي والنصح في ذلك مع الترهيب من كل ما يخالف أحكام الإسلام، وبذلك يكونوا قد سلكوا مسلك النبي ﷺ، ومسلك خلفائه الراشدين وصحابته المرضيين في إيضاح سبيل الحق والإرشاد إليه والتحذير مما يخالفه.
(انظر رسالة التحذير من فتنة التكفير ص ٩٩ - ١٠٠).

Yake cewa:
Ya zama wajibi ma'abota sani su kula da kira zuwaga Allah, *tareda rabewa!* da bayyanar da musulunci ga mutane da dalilai daga Al-Qur'ani da Sunnah, da kwadaitar dasu tsayuwa akansa, da yi musu wasici da nasiha cikin wannan tare da *tsoratarwa daga duk abinda ya sabawa hukunce-hukuncen Musulunci, kuma da hakan ne zasu kasance sun bi tafarkin Manzo Sallallahu alayhi wasallam, da tafarkin khalifofinsa shiryayyu, da sahabbansa yardaddu,  wajen bayyana *tafarkin gaskiya* da shiryatarwa zuwa gareshi, da tsoratarwa daga abinda ya saba mishi.
(Risalatu Finatit Takfeer 99-100) .

*Shaikh Sāleh Alfauzan ma yana cewa:*

فالذي يزعم أنه على مذهب أهل السنة والجماعة يتبع طريقة أهل السنة والجماعة ويترك المخالفين، أما أنه يريد أن يجمع بين الضب والنون —كما يقولون—، أي يجمع بين دواب الصحراء ودواب البحر؛

Yace: duk wanda ke raya cewa shi yana kan tafarkin Ahlus Sunnah wal jama'ah, to lallai zai bi tafarkin Ahlus Sunnah wal Jama'ah din ne, kuma zai kyale wa'yanda suka sabawa tafarkin, amma wai shi yayi nufin hada tsakanin damo da kifi - kamar yadda ake cewa- ma'ana: ya hada tsakanin dabban tudu da na ruwa;

 فلا يمكن هذا، أو يجمع بين النار والماء في كفة، فلا يجمع أهل السنة والجماعة مع مذهب المخالفين لهم كالخوارج، والمعتزلة، والحزبيين ممن يسمونهم: «المسلم المعاصر» وهو الذي يريد أن يجمع ضلالات أهل العصر مع منهج السلف، فـ «لا يصلح آخر هذه الأمة إلا ما أصلح أولها» فالحاصل: أنه لا بد من تمييز الأمور وتمحيصها“
(انظر الأجوبة المفيدة ص ٤٠).

Lallai haka ba zai yiwu ba, ko a hada wuta da ruwa acikin gu daya, saboda haka Ahlus Sunnah wal jama'ah  bazai cakudu da masu tafarki wanda ya sabawa Sunnah ba, kamar Khawarijawa, da Mu'utazilawa, da 'yan kungiya daga cikin wa'yanda ake kiransu "Musulman Zamani, kuma shine abinda manufarsa ita ce ya tattara duk wani 'bata na mutanen wannan zamani, sai kuma a cakuda shi da tafarkin Salafus Saleh, don haka babu abinda zai gyara al'umar karshe shine abinda ya gyara na gabansu, abinda yake dai-dai shine banbance lamurra da tsarkakewa.
(Al-Ajwibaul Mufeedah, shafi na 40) .
________________________________________________
Dubi inda Malaman nan sukayi ta maimaita " gaskiya" saboda duk hanya ta kwarai rububi akeyi a jingina da ita, sannan zakaji mamakin mutum yace shi Salafi ne amma kuma yana bin wata hanya daban wacce ta sabawa tafiyar Salafiyyah din...

*SAI MAGANA AKAN MASU ZAMANINTAR DA ADDINI*

Wa'yannan mutane sukan juye ma'anoni na kalaman Allah da manzon sa, misali sai suce Annabi Isah da nassoshin hadisai suka nuna zai dawo ba shi din bane Salahu Al- Deen Al- Ayyubi ne, ko kuma suce Dujal mai ido daya Television ake nufi, ko wani abu ya faru suce ai ga fassarar aya kaza nan, suna sarraha cewa aya kaza ko hadisi kaza sai daga baya fassarar su ta fito, ma'ana: Sahabbai ma basu fahimci wannan abu da su suka fahimta ba, duk wannan ba dai-dai bane, bata ne, kuma ya sabawa tafarkin magabata Salafus Sāleh, dole ne Musulmai su takaitu akan fahimtar Sahabbai, domin Sahabbai Almajiran Manzon Allah ne, sun fi kowa sanin ma'anonin kalaman Allah da na Manzon sa, kuma duk wata fahimta da ta saba wa tasu bata ce, abar mayarwa ce.

*Shaikhul Islami Ibnu Taimiyah yana cewa akan irin wannan Bid'ah ta masu zamanintar da Addini*
«ومن أعظم الغلط في فهم كلام الله ورسوله :
أن ينشأ الرجل على اصطلاح حادث ، فيريد أن يفسر كلام الله بذلك الاصطلاح»
[مجموعة الفتاوى ١٠٦/١٢].

Yana daga cikin mafi girman kuskure cikin fahimtar maganar Allah da Manzonsa: shine mutum ya tashi akan wani istilahi fararre, sai ya nufaci fassara maganar Allah da wannan istilahi.
(Duba Majmu'atul Fatawa 12/106) .

Kenan irin wannan Bid'ah ta masu فقه الواقع، na daga harakiyyun masu wa'azin caji da azarbabi wajen halasta jinin wani shugaba ko keta mutuncin wani mai mulki, shugaban kasa ne ko gwamna ko sarakuna, masu ganin cewa a kwatanta addini da zamani har suke cin kafar gogaggun Malamai dattawa a tafarkin koyarda Sunnah da yadata , da sunan basu san zamaninsu ba, misali: Mutum ya dubi Malamin Sunnah kamar Shaikh Muhammad Nasiru Al-Deen Al- Albāniy yace bai san zamaninsa ba don a gurinsa tawaya ce ga mai da'awa in bai iya wasu abubuwa da suke tafiya da zamani ba, wannan tunani ne abin mayarwa!

Ko shakka babu abinda ya shafi lamurran duniya kamar zamani wanda yake da alaka da rayuwa tabbas don mai da'awa bai sanshi ba ba tawaya ce garesa ba, don ko Annabi akwai sa'ilin da ya hana kililin dabino amma sai arzikin dabino bai habaka yadda aka saba kowace shekara ba, sai ya tambayesu sukace ai ka hana kililin dabino! Sai yace ku ne kuka fi sanin lamurran duniyarku! Kuma ya barsu suci gaba da kililinsu..  To sai kace bai halasta ayi amfani da hadisan Annabi ba don shi bai gane lamarin duniya ba a wajenka?! Ko shakka babu wannan wata hanya ce ta baiwa mabarnata mafaka su aukawa Sunnah sai addini ya lalace, ko ya cakudu ga mabiyansa! Wannan misalin kadai ya isa ya rushe masu da'awar فقه الواقع! Allah ya kiyaye!!

Lallai Salafiyyah ba kungiya bace kuma bata yarda da kafa kungiyoyi ba, kuma Malaman Sunnah na gaskiya a wannan zamani basu yarda da kafa kungiya da sunan da'awa ba, kuma basu yarda da shiga kungiyoyi ba, littafansu na nan kuma kasusuwansu na nan godiya ta tabbata ga Allah.

Dan uwanku a Muslunci da Sunnah:

 أمين ثالث يعقوب

01 / 07 / 1439
18 / 04 / 2018

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!