SAURARON BID'AH HARAMUN NE KAMAR YADDA KIRA ZUWA GARETA YAKE HARAMUN!
Al- ‘Allāmatu Bnu Al- Qayyim (Allah ya jikan sa) yana cewa:
«وأما محرّمه: فهو النطق بكلّ ما يبغضه الله ورسوله ﷺ ، كالنطق بالبدع المخالفة لما بعث الله به رسوله ﷺ ، والدعاء إليها ، وتحسينها وتقويتها ، وكالقذف وسب المسلم ، وأذاه بكلّ قول . والكذب ، وشهادة الزور ، والقول على الله بلا علم . وهو أشدّها تحريما»
[التفسير القيم ص ١١٦].
« Amma kuma haramtaccen sa (ma'ana: furuci na harshe) shine yin furuci da dukkan abinda Allah yake kin sa, Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ma yake kinsa , kamar furuci da Bid'ah wacce take sabanin abinda Allah ya aiko Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - dashi ne , da kira zuwa ga wannan Bid'ah , da kayata ta , da karfafar ta , haka kuma yin kazafi haramun ne haka zagin musulmi , da cutar dashi da kowacce irin magana . haka kuma karya haramun ce , da shaidar zur , da magana akan Allah ba tare da ilimi ba . kuma haramcin wannan yafi tsanani »
[Al- Tafseeru Al- Qayyim, shafi na 116].
Yake cewa akan sauraro:
«ويحرم عليه : استماع الكفر والبدع ، إلا حيث يكون في استماعه مصلحة راجحة : من ردّه ، أو الشهادة على قائله ، أو زيادة قوّة الإيمان والسنّة بمعرفة ضدّهما من الكفر والبدعة ونحو ذلك»
[التفسير القيّم ص ١١٧].
«kuma ya haramta a gare shi: sauraron (magana) ta kafirci da ta Bid'ah , sai a yanayin da akwai maslaha mai rinjaye : na daga raddi ga wannan magana , ko don zama shaida akan wanda ya fade ta , ko don karin karfin imani da Sunnah ta hanyar sanin abinda ya saba musu na kafirci da Bid'ah da makamancin haka»
[Al- Tafseeru Al- Qayyim, shafi na 117].
Sai Ibnul Qayyim ya ambaci sharudda guda uku ga wanda zai saurari Kafirci ko Bid'ah a inda yake cewa: “sai a yanayin da akwai maslaha mai rinjaye : na daga raddi ga wannan magana , ko don zama shaida akan wanda ya fade ta , ko don karin karfin imani da Sunnah ta hanyar sanin abinda ya saba musu na kafirci da Bid'ah da makamancin haka”.
Kenan in ba akan wa'yannan sharudda ba sauraron kalamai na kafirci ko na Bid'ah yana nan a asalin sa na haramun , sannan wa'yannan sharudda da ya ambato suna nuna mana cewa sai ma'abota Sunnah wa'yanda suke da masaniya akan ta su ne aka yi wa rangwame cikin saurarawar , kenan jahilan mutane ko gama-gari wa'yanda basa da masaniya akan Sunnah , basu san ginshikan da Sunnah ta kafu a kansu ba , bare ma su iya banbance Sunnah daga Bid'ah wa'yannan kamewa daga sauraron shine zaman lafiya gare su , kai ba ma jahilai ko gama-gari kadai abin ya shafa ba , nawa ne cikin wa'yanda suke ma'abota Sunnah amma zama da 'yan Bid'ah yasa suka koma tafarkin nasu?!
Wannan yana daga cikin dalilan da Salaf suke kin sauraron 'yan Bid'ah , kamar yadda wa'yannan atharai zasu bayyana mana:
قال ابن عباس - رضي الله عنهما - :
«لا تجالسوا أهل الأهواء؛ فإن مجالستهم ممرضة للقلوب»
[أخرجه الآجري في الشريعة 1/453].
Sahabi Abdullahi Bin Abbas -Allah ya kara yarda a gare sa shi da mahaifin sa - yana cewa: «karku zauna tare da ma'abota son zuciya, domin zama tare dasu yana cutar da zuciya»
[Al- Aajurriy ya fitar da ita a Al- Sharee'ah 1/453].
Kenan: zama da ma'abota son zuciya yana cutar da zuciya, ta fuskoki kamar haka:
1. In ma dai zaman ya sabbaba shakka akan Sunnar da wanda yayi zaman tare dasu yake a kanta, ya rika kokonto shin akan gaskiya yake kuwa , ko kuma zaman ya sabbaba karkatar zuciyar sa zuwa ga ra'ayoyin su , sai ya kasa zama akan tafarki guda daya , yau yana can gobe yana can!
2: ko kuma su sanya masa shubuha ko ya tashi daga gurin su yaje yayi ta wahala yana binciken yadda zai warware shubuhar, ko kuma ya rika kai-komo akan imanin sa , wannan karan kanta ta isa bala'i ga zuciyar bawa.
قال أبو قلابة - رحمه الله - :
«لا تجالسوا أهل الأهواء، ولا تجادلوهم؛ فإني لا آمن أن يغمسوكم في الضلالة، أو يَلْبِسوا عليكم في الدين بعض ما لبس عليهم»
[أخرجه الآجري في الشريعة 1/453-436]
Abu Qilābah - Allah ya jikan sa - yana cewa:
«Karku zauna da ma'abota son zuciya , kuma karku yi jayayya dasu ; domin ni ban lamunce ba ina tsoron kar su shigar daku cikin bata , ko su cakuda muku a cikin addini da wani sashe na abinda aka cakuda musu»
[Al- Aajurriy ya fitar dashi a cikin Al- Sharee'ah]
قال سلام بن أبي مُطيع - رحمه الله - :
«إن رجلاً من أصحاب الأهواء
قال لأيوب السختياني : يا أبا بكر، أسألك عن كلمة، فولى أيوب، وجعل يشير بإصبعه: ولا نصف كلمة»
[أخرجه الآجري في الشريعة 1/440].
Salāmu Bin Abi Mutee'in yana cewa:
«Wani mutumi daga ma'abota son zuciya yace da Ayyub Al- Sakhtiyāniy: ya Ababakr , in tambayeka dangane da wata kalma mana , sai Ayyub ya juya baya , yana ishara da hannun sa yana fadin " ko da ma rabin kalma ce»
[Al- Aajurriy ya fitar dashi a cikin Al- Sharee'ah 1/440]
(ma'ana ba zai saurare shi ba, ballantana ya shiga gardama dashi).
قال أسماء بن عبيد - رحمه الله - :
«دخل رجلان من أهل الأهواء على ابن سيرين، فقالا: يا أبا بكر، نحدثك بحديث. قال: لا، قالا: فنقرأ عليك آية من كتاب الله عز وجل، قال: لا، لتقومانِّ عني أو لأقومنَّ . قال: إني خشيت أن يقرآ عليَّ آية فيحرفاها فيقرَّ ذلك في قلبي»
[أخرجه الدارمي 1/81].
Asma'u Bin Ubayd - Allah ya jikan sa - yana cewa:
«Wasu mutane biyu sun shiga wurin Ibnu Sireen , sai suka ce : ya Ababakr , mu karanta maka hadisi , sai yace (dasu) : a'a , sai suka ce: to mu karanta maka aya daya daga cikin littafin Allah mai girma da buwaya , sai yace: a'a , ko dai ku tashi daga ku barni ko ni in tashi . yace: ni naji tsoron kar su karanta min ayah ne su karkatar da ita (daga ma'anar ta) sai hakan ya tabbata a zuciya ta»
[Al- Dāramiy ya fitar dashi 1/81].
قال محمد بن النضر الحارثي - رحمه الله - :
«من أصغى سمعه إلى صاحب بدعة وهو يعلم أنه صاحب بدعة؛ نزعت منه العصمة وَوُكِّلَ إلى نفسه»
[أخرجه اللالكائي 1/153].
Muhammad Bin Al- Nadhir Al- Hārithee yana cewa:
«Duk wanda ya saurari dan Bid'ah alhalin yana sane cewa dan Bid'ah ne; an cire kariya garesa kuma an wakilta shi ga kansa»
[Al- Lālakā'iy ya fitar dashi 1/53].
كان ابن طاووس جالسا فجاء رجل من المعتزلة، قال: فجعل يتكلم، قال: فأدخل ابن طاووس إصبعيه في أذنيه قال: وقال لابنه: «أي بني، أدخل إصبعيك في أذنيك واشدد ولا تسمع من كلامه شيئاً». قال معمر: يعني أن القلب ضعيف
[أخرجه اللالكائي 1/152].
Ibnu Tāwūs ya kasance a zaune , sai wani mutum daga mu'utazilawa yazo , sai yace: sai ya fara magana, sai Ibnu Tāwūs ya sanya yatsun sa ya toshe kunnuwan sa, kuma yace da dansa: «ya kai da na ka sanya hannayen ka ka toshe kunnuwan ka, kuma ka tsananta, karka saurari wani abu daga cikin maganar sa». Ma'amar yace: yana nufin lallai zuciya mai rauni ce
[Al- Lālakā'iy ya fitar dashi 1/152].
A irin haka ne aka ruwaito daga Abdullahi Bin Al- Busriy yana mai inkarin zama da 'yan Bid'ah:
قال أحمد بن الحواري رحمه الله تعالى:
قال لي عبد الله بن البسري -وكان من الخاشعين؛ ما رأيت قط أخشع منه- -: «ليس السنة عندنا أن ترد على أهل الأهواء، ولكن السنة عندنا ألا تكلم أحدا منهم».
[أخرجه ابن بطة في الإبانة ٤٧٨].
Ahmad Bin Al- Hawāriy - Allah ya jikn sa - yana cewa: Abdullāhi Bin Al- Busriy yace dani: - kuma ya kasance cikin masu tsoron Allah, ban taba ganin wanda ya fi shi tsoron Allah ba - yace: «ba Sunnah bace a wajen mu kayi martani ga ma'abota son zuciya ba, Sunnah a wajen mu ita ce kar ma kayi magana da daya daga cikin su»
[Ibnu Battah ya fitar dashi a cikin Al- Ibānah 478].
Ma'ana: baya daga cikin Sunnah ka zauna dasu suna fade kana mayar musu kuyi ta jayayya, abinda yake Sunnah shine karka ma yi magana dasu, karka kuma saurare su!
وقال الشوكاني - رحمه الله - في تفسيره لقول الله تعالى:
(وإذا رأيت الذين يخوضون في آياتنا...) الآية [الأنعام: 68] :
«وفي هذه الآية موعظة عظيمة لمن يتمسح بمجالسة المبتدعة الذين يحرفون كلام الله، ويتلاعبون بكتابه وسنة رسوله، ويردون ذلك إلى أهوائهم المضلة، وبدعهم الفاسدة. فإنه إذا لم يُنْكِر عليهم ويُغَيِّر ما هم فيه، فَأَقَلُّ الأحوال أن يترك مجالستهم، وذلك يسير غير عسير. وقد يجعلون حضوره معهم مع تنزهه عما يتلبسون به شبهةً يشبهون بها على العامة، فيكون حضوره مفسدة زائدة على مجرد سماع المنكر»
[فتح القدير 2/128].
Kuma Al- Imām Al- Shaukāniy - Allah ya jikan sa - yana cewa a cikin fassarar sa ga fadin Allah:
(وإذا رأيت الذين يخوضون في آياتنا..)
[Al- An'ām aya ta: 68].
«Kuma a cikin wannan ayar akwai wa'azi mai girma ga wanda yake mudahana yana zama da 'yan Bid'ah, wa'yanda suke karkatar da maganar Allah, kuma suna wasa da littafin sa da Sunnar Manzon sa, kuma suke mayar dashi(ma'ana suna murde fassarar sa) zuwa son zuciyar su batacce, da Bid'ar su gurbatacciya. Domin shi in bai yi inkari ba, kuma bai canza abinda suke cikin sa ba, to mafi karancin halaye shine ya daina zama dasu, kuma hakan abu ne mai sauki ba mai wahala bane. Kuma suna ma iya daukar zaman nasa tare dasu ya zama tsarkakewa ga abinda suke cakudawa na daga shubuhohi wa'yanda hakan zai zama shubuha ga gama-garin mutane , (ma'ana: gama-garin mutane zasu ce ai da ace su wane ba mutanen kirki bane ai Malam wane ba zai zauna dasu ba! Sai hakan ya zama shubuha gare su) sai zaman nasa tare dasu ya kasance doriya ce ga barna sama da tsuran sauraron(sa) ga abin kin»
[Fathu Al- Qadeer 2/128].
وقال البغوي - رحمه الله - :
«فعلى المرء المسلم إذا رأى رجلا يتعاطى شيئا من الأهواء والبدع معتقدا، أو يتهاون بشيء من السنن أن يهجره ويتبرأ منه، ويتركه حيا وميتا»
[شرح السنة 1/224].
Al- Imām Al- Baghawiy - Allah ya jikan sa - yana cewa:
«Ya zama wajibi akan mutum musulmi idan yaga wani mutumi yana aikata wani abu na son zuciya da Bid'ah, yana mai kudurin sa, ko kuma yana raina wani abu daga cikin Sunnoni, ya zama wajibi garesa da ya kaurace masa, kuma yayi bara'a dashi, kuma ya barsa yana raye ne ko yana mace!»
[Sharhu Al- Sunnah 1/224].
Wannan misali ne daga yadda magabata na kwarai (Salafu Al- Sālih) suka kasance suna kyamatar sauraron 'yan Bid'ah da son zuciya, da za'a ci gaba da ambaton su da ba zasu ginshi mai neman gaskiya ba, kuma ba zasu daina rikitar da ma'abota son zuciya ba, har ya kasance magabata na kwarai suke kirga zama tare da 'yan Bid'ah da son zuciya a matsayin mudahana, da batar da gama-garin bayin Allah, suna tsoratarwa daga hakan, maganganun su gabaki daya suna nuna yadda sukayi Ijma'i akan haramcin zama da Sauraron 'yan Bid'ah da son zuciya, lallai nagartacciyar fahimta ga addini tana cikin tafarkin su, zo kaga jahilci da dakikanci da kidahumancin cikakken dan bana bakwai, wanda yake cin gyara ga tafarkin Musulman farko, yana cin karo ga tafarkin nasu ta hanyar fadin a tsinci dai-dai abar kuskure, ko shakka babu wannan batarwa yake yi ko da ma ba'a ganin sa tare da 'yan Bid'ar, saboda sharrin sa mai girma ne kuma magabata na kwarai basu furta irin wannan maganar ba a babin tsoratarwa daga Bid'ah da ma'abota Bid'ah da son zuciya, haka kuma sakarcin wanda ya dauki zama da ma'bota Bid'ah da son zuciya su fada ya fada a matsayin gwaninta ko iya jayayya, zaka fahimci cewa mai wannan aikin bai san inda ke mai ciwo ba.
Allah yayi mana kariya daga ma'abota son zuciya da Bid'ah da katanga ta karfe (amin).
Dan uwan ku a musulunci da Sunnah:
أمين ثالث يعقوب
01 / 03 / 1440
09 / 11 / 2018

تعليقات
إرسال تعليق