
RABA NI DA BONONO RUFIN KOFA DA BARAWO! (10) FIKIRORIN DA SUKE KARFAFAR GINSHIKAN SURURIYYAH (05) (vi) fikira ta biyar ita ce: tabbatar da mas'alar Al- Muwazanāt (ma'ana: yin gwaji tsakanin kyawawan ayyuka da munana) a yayin yin martani ga dan Bid'ah, ta yadda za'a ambaci kyawawan ayyukan sa da munanan a yayin yi masa raddi, wanda hakan yana kaiwa zuwa ga yin sakaki da ko in kula a kan martani ga 'yan Bid'ah da son zuciya . Shaikh Bin Baz yana martani ga wannan Manhaji na Al- Muwazanāt wanda yake lazimta yin awo tsakanin ayyukan 'yan Bid'ah yake cewa: "من أظهر المنكر أو البدعة، يحذر منه، ولا ينظر إلى حسناته، حسناته بينه وبين ربه.." Ma'ana: duk wanda ya bayyana abin ki ko Bid'ah za'a tsoratar ne daga gare shi, kuma ba za'a yi dubi zuwa kyawawan ayyukan sa ba, domin kyawawan ayyukan sa tsakanin sa ne da Ubangijin sa! Kana iya sauraren wannan magana tare da maganar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen -Allah ya ...