المشاركات

صورة
Raddi ga Sururiyyah
صورة
*SHAIKH SĀLEH AL- FAUZAN YANA KARFAFAR SALAFAWAN GASKIYA!* An tambayi Shaikh Saleh Al- Fauzan -Allah ya kiyaye shi- Mai tambayar yake cewa: السؤال:  نحن مجموعة من الشباب ندعوا إلى منهج السلف الصالح، وملازمة الجماعة والسمع والطاعة لولي الأمر في غير المعصية، ونحذر من الجماعات الحزبية، ولكنهم يحذّرون منا، ويسموننا "جامية" فهل نستمر على ما نقوم به؟ Tambaya: mu wasu taro ne na matasa, muna kira zuwa ga Manhajin Al- Salaf Al- Sālih, da kuma lazimtar jama'ah, da sauraro da biyayya ga shuwagabanni a cikin abinda ba sabon Allah bane, kuma muna tsoratarwa daga kungiyoyi "na hizbiyyah", sai dai su suna tsoratarwa daga garemu, kuma suna kiranmu da (lakabin) "Al- Jāmiyyah"  shin zamu ci gaba da abin da mukeyi ne? الجواب: استمروا واصبروا ولا يهمكم ما يقولون -  [📖 رسالة وجوب لزوم الجماعة ص38] Amsa: kuci gaba da abinda kukeyi, kuma kuyi hakuri, kuma kar abinda suke fade ya dame ku, domin ku ba yardar su kuke nema ba, haka kuma ba yabon su kuke nema b...
صورة
GASKIYAR LAMARI (2) : Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan gaskiya, shi yasa Allah yake taimakon su, babu wani karkatacce, ko mabiyin karkataccen tafarki da zasu soka sai wannan suka ta zama gyambo garesa, dalili akan haka: Ahlus- Sunnah na gaskiya sun tsaya ne akan turba ta musulunci irin na musulman farko, kuma Allah yayi alkawarin taimakon muminai, yayi alkawarin tseratar da muminai daga fitintinu kamar yadda yayi alkawarin tseratar da manzannin sa, wannan tseratarwa daga fitintinun duniya ne wa'yanda fitina ba zata sanya su su karkace daga tafarkin gaskiya ba, kuma a lahira zai tseratar dasu daga azabar wuta, wacce yayi alkawarin azabtar da masu sabawa Manzannin sa ne da ita, sannan kuma yayi alkawarin gidaje na Aljannah da rayuwa ta jin dadi ga Muminai a ranar lahira, jin dadi na har abada saboda tsayuwa da sukayi akan Imani da abinda Imanin yake kunshe dashi, wanda ya kunshi martanin abinda ya sabawa gaskiya, zuwa wanda ya aikata shi ko ya furta shi, sannan All...
صورة
GASKIYAR LAMARI (1) Komai daren dadewa Allah zai bayyana gaskiya, kuma zai daukaka ma'abotan ta, ambatonsu zai ci gaba da wanzuwa tare da ambaton gaskiyar da suka tsayu akan ta, kuma suka bata kariya, sukayi martanin abinda ya saba wa tafarkin Annabi da Sahabbai, na maganganu ne ko na ayyuka, ta yadda su kuma ma'abota karkata suke mutuwa ambatonsu ya mutu, ko kuma ambatonsu ya wanzu tare da sukar tafarkin da suka rayu akan sa, sukayi turjiya wajen kariya ga barna, suka bata lokacinsu da surutai wajen kishiyantar gaskiya da bata sunan mabiyanta na gaskiya, ambatonsu zai wanzu ne a bakin ma'abota gaskiya tare da martani ga barnar da suka shayar da mutane da sunan addini, ko da sunan Sunnah, ko da sunan Salafiyyanci, shi tafarkin Sunnah na gaskiya yana nan dama tun tuni yana rabewa tsakanin gaskiya da karya, ba yau aka fara ba, kuma Ahlus- Sunnah na gaskiya Allah ne yake musu yaki, kuma shine yake daukaka ambaton su, ba don komai ba, sai don sun tsaya akan turba ta gaski...
صورة
Wani yayi tambaya yace: "menene ma'anar Sururiyyah?" Sai nace dashi: Kungiya ce wacce ake nasabta ta ga Muhammad Surur Zainul Abideen, wanda asalin sa dan Syria ne, yayi zama a Saudiyyah shekaru 8, yayi karatu a Kwalejin ilimi a Buraidah, daga nan ya koma Brtaniya, ya koma Qatar wanda a nan ya mutu a shekarar 2016, wannan kungiya ta Sururiyyah an san ta ne da gauraye tsakanin Sunnah da Ikhwaniyan ci, sune suka kawo rudanin cewa Aqeedar Mutum Salafiyyah amma Manhajin sa Ikhwaniyyah, an san su da tawaye ga shuwagabanni Musulmai, tawaye na kalma da kuma karfafar Khawarijawa masu yakar gwamnatocin su, da yaba musu, da kuma tunzura matasa a kan zanga-zanga ma gwamnatocin su, da da'awar neman 'yanci ko kuma inkari ga azzalumai, sannan suna kambama Sayyid Qutb da tawagar sa 'yan ta'adda, basa kuma ganin cewa akwai gwamnatin Musulunci a wannan zamanin, suna kiran shuwagabanni Musulmai da الطواغيط (ma'ana: dagutai) sannan suna jifan Malaman Sunnah wa...
صورة
*DA'AWAR MA'ABOTA SUNNAH KIRA NE ZUWA GA TAFARKIN ALLAH, BA DA'AWA CE TA TARA KUDIN MUTANE BA!* ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﻣﻘﺒﻞ ﺑﻦ ﻫﺎﺩﻱ ﺍﻟﻮﺍﺩﻋﻲ - ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :- ..." ﻓﺄﻧﺼﺢ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻣﻮﺍ ﺑﻮﺍﺟﺒﻬﻢ ﻧﺤﻮ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ، ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ، ﻧﺤﻦ ﻟﺴﻨﺎ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺍﺗﺒﺎﻋﻨﺎ ﻓﻠﺴﻨﺎ ﺃﻫﻼ ﻷﻥ ﻧﺘﺒﻊ، ﺑﻞ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺃﻥ ﻧﺘﺒﻊ ﻧﺤﻦ ﻭﻫﻢ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ .- ﻭﻟﺴﻨﺎ ﻧﺪﻋﻮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻟﻰ ﺃﺧﺬ ﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ، ﻭﻟﻮ ﺫﻫﺒﺖ ﺇﻟﻰ ﺃﻱ ﺑﻠﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﻼﺩ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ ﻓﻠﻦ ﺗﺮﻯ ﺳﻨﻴﺎ ﻳﻘﻮﻡ ﻭﻳﻌﻆ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺣﺘﻰ ﻳﺒﻜﻴﻬﻢ، ﺛﻢ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻳﻔﺮﺵ ﻋﻤﺎﻣﺘﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﺒﺎﺏ ." ‏[ ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻟﻤﺠﻴﺐ ‏( 75 - 76)]. Al- Allāmah Muqbil Bin Hādiy Al- Wādi'iy -Allah ya jikan sa- yana cewa: Ina yiwa ma'abota Sunnah nasiha da su tsayu da wajibin su ta bangaren da'awah, amma don fuskar Allah mai girma da buwaya, mu bama kiran mutane don su bimu, domin mu bamu cancanci a bimu ba, sai dai muna kiran mutane ne damu dasu mubi littafin Allah da Sunnar Manzon Allah -Sallallāhu 'alayhi wasallam- Kuma mu ba kiran mutane muke don mu karbi k...
MAGANA AKAN 'YAN BID'AH DA MASU KARKATACCEN MANHAJI BA GIBA (GULMA) BACE  ❁❁❁❁❁❁       ــــــ ❁❁❁❁❁❁ ـــــ       ❁❁❁❁❁❁ Fatawar Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen (Allah ya jikansa) : ❍ الشيخ محمد بن صالح العثيمين : السّـؤال : الكلام في أهل البدع ، مثل أن يقال مثلاً: أنهم يؤولون الآيات والأحاديث، ويقولون: يفعلون كذا وكذا.. أيعتبر هذا غيبة إذا كان بين الطلبة ؟ Tambaya: Magana akan 'yan Bid'ah, kamar misali ace: sunayin tawilin ayoyi da hadisai, kuma suna aikata kaza da kaza, shin wannan ana daukarsa giba (gulma) ce in ya kasance a tsakanin dalubai ne? »» الجواب: الكلام في أهل البدع ومن عندهم أفكار غير سليمة أو منهج غير مستقيم، هذا من النصيحة وليس من الغيبة ، بل هو من النصيحة لله ولكتابه ولرسوله وللمسلمين ، فإذا رأينا أحداً مبتدعاً ينشر بدعته ، فعلينا أن نبين أنه مبتدع حتى يسلم الناس من شره ، وإذا رأينا شخصاً عنده أفكار تخالف ما كان عليه السلف فعلينا أن نبين ذلك حتى لا يغتر الناس به ، Amsa: Magana akan 'yan Bid'ah da ma...