*SO DA DAMA MAI DA'AWAR NEMAN GASKIYA DA ADALCI YANA AUKAWA CIKIN TAFARKIN AZZALUMAI BA TARE DA YA SANI BA!* So tari zakaga mutane masu son addini da adalci ga bayin Allah, sai suyi rashin dace sai su auka tarkon mabarnata fasikai basu sani ba, yana da kyau ya kai mai amfani da Facebook, ko mai neman gaskiya, ya kasance da gaske gaskiyar kake nema, ba yawan mabiya ko masu yin muwafaka da ra'ayin ka kake nema ba, ya kasance gaskiya ce abar neman ka, kuma da gaske, ka saki ta'assubanci, domin duk mai son ya zama "Salafi" (ma'abocin Sunnah na gaskiya) to sai ya yakice rigar ta'assubanci ya wurga wa shedan kayan sa, domin ta'assubanci ba tufafin mumini bane, kuma wuyan rigar gaskiya da adalci tayi kunci ga fasikai masu bada kariya ga 'yan Bid'ah da son zuciya. Idan ka gane wannan, zaka ga marubuta da yawa masu da'awar su ma'abota Sunnah ne, wani ma zakaji yana cewa shi mabiyin Tafarkin Salaf ne, zaka dinga cin karo da maganganun Ibnu Taimi...
تعليقات
إرسال تعليق