Shimfidaddar Nasiha Ga Dan Uwa A Musulunci Da Da’awah, A Kan Ganin Halaccin Munanan Addu’o’i Da Tsinuwa Ga Azzaluman Shugabanni [Martani Ga Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ‘Shugaban Majalisar Malaman J.I.B.W.I.S Na Kasa, Bangaren Kaduna]
Marubuci: Sheikh Jaafar Saad (H.A)
Matantanci: Ibrahim Lawal Soro (W.A)
Da sunan Allah mai rahma mai jinqai, tsira da aminchin Allah su tabbata ga Annabin Rahma, wanda yazo da miqaqqen tafarki, ba wanda zai karkace daga barinsa face ya halaka, da sahabbansa da iyalan gidansa wadanda basu gaza ba wajen isar wa mutane saqonsa, bisa amana da cikakkiyar biyayya.
Bayan haka:
Annabi -sallallahu alaihi wasallam- ya ce:
“Addini nasiha ce.”
A kan wannan bangaren na ga cewa wajibi ne akai na na yi Magana a kan wannan al’amari ba don na kai ba, sai don sauke nauyin dake kaina.
Haafidh Ibn Rajab (R.A) a ckin (Jaami’ al- UluUm) ya ce:
"ومن أنواع النصح لله تعالى وكتابه ورسوله - وهو مما يختص به العلماء - رد الأهواء المضلة بالكتاب والسنة، وبيان دلالتهما على ما يخالف الأهواء كلها وكذلك رد الأقوال الضعيفة من زلات العلماء، وبيان دلالة الكتاب والسنة على ردها، ومن ذلك بيان ما صح من حديث النبي صلى الله عليه وسلم، وما لم يصح منه بتبيين حال رواته ومن تقبل رواياته منهم ومن لا تقبل، وبيان غلط من غلط من ثقاتهم الذين تقبل روايتهم"
“Na daga cikin nau’o’in nasiha ga Allah (S.W.T) da littafinsa da manzonsa –kuma wannan ya kebanta ne ga malamai kawai- raddi akan son zuciyoyi masu batarwa da littafin Allah da sunnah, da kuma bayanin nuninsu ga abin da ya saba wa son zuciyoyin dukansu, haka nan kuma raddin maganganu masu rauni daga cikin tuntuben malamai, da bayanin nunin littafin Allah da sunnah zuwa ga raddinsu….”
zuwa qarshen maganarsa.
Hakanan malamai magabata sun yi ijma’I a kan wajibcin fahimtar nassosin Alqurani da sunnah a bisa fahimtar magabata nagartattu, na daga sahabban manzon Allah -sallallahu alaihi wasallam- da wadanda suka biyo bayansu a kan tafarkinsu, na daga imaman addini.
Imam Abu Amr al-Auzaa’ee (R.A) ya ce:
"عليك بآثار من سلف وإن رفضك الناس، وإياك وآراء الرجال، وإن زخرفوه لك بالقول"
“Kayi riqo da tafarkin magabata koda ko mutane sunki karbarka, kuma ahir dinka daga bin raayoyin mazaje, koda kuwa sun qawata maka shi da zance”
Duk da cewa ban dauki kaina malami ba amma na dauki wadannan magabatan a matsayin malamai, kuma babu wani mutum face ana yi masa raddi shima yanayi, sai manzon Allah (s.a.w) (maganar imam malik ce).
Mu ji tsoron Allah mu sani cewa: ilmi amana ce, kuma duk wanda yai wa mutane fatawa rubabba suka bi haqqinsu yana kansa, kamar yadda Abu Khaisamata, da Zuhair dan Harb ya rawaito cikin littafinsa al’ilm daga sashen magabata, an kuma rawaito irinsa marfu’i.
Hakika aikinku na dora wadannan hadisai a kan shugabanni da suka yi zalunci ya saba wa karantarwar magabata, kuma ma tafarki ne na khawarij, zan taqaita naqalina saboda yanayin waje, amma idan malam yaso buda mas’alar zan iya ware mata bahasi mai fadi, amma bata duniyar internet ba.
Hakika manzon Allah -sallallahu alaihi wasallam- ya yi umurni da a yi wa shugaba musulmi da’a, mai adalci ne ko azzalumi ne, a kan wannan kuma gaba daya magabatan al’umma suka tafi, suka kuma sanya cewa na daga cikin aqidar ahlussunnah yi wa shugaba addu’a mai kyau da kuma kamewa daga yi masa mummunar addu’a ba tare da rabewa tsakanin azzalumi da mai adalci ba, jingina musu wanin wannan zaluntar su ne, kamar yadda zai zo, haka kebance hadisan da’a da hana mummunar addu’a a kan shugabanni ban san yadda malam ya samo kebance su ga shugaba mai adalci kawai ba, kamar yadda zamu gani daga maganganun magabata.
Imam al-Sam’aanee (R.A) ya rawaito a littafinsa ‘ al’Intisar Li Ashabil Hadeeth’ daga Imaam al- Shafi’ee(R.A ) ya ce:
"كل من تكلم بكلام في الدين أو في شيء من هذه الأهواء ليس له فيه إمام متقدم من النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه فقد أحدث في الإسلام حدثا"
“Duk wanda yayi Magana da wani zance a cikin addini ko cikin wani abu na son zuciya (bidi’o’i) alhalin bashi da wani imami magabaci a cikinsa, na daga manzon Allah, ko sahabbansa haqiqa ya qirqiri sabon abu a musulunci”
Wasu daga cikin dalilai akan wajibcin biyayya ga shugaba azzalumi da adali:
1-Imam Muslim ya rawaito daga Sahabi Huzaifah (R.A) daga manzon Allah -sallallahu alaihi wasallam- ya ce :
"يكون بعدي أئمة لا يهتدون بهداي، ولا يستنون بسنتي، وسيقوم فيهم رجال قلوبهم قلوب الشياطين في جثمان إنس»، قال: قلت: كيف أصنع يا رسول الله، إن أدركت ذلك؟ قال: «تسمع وتطيع للأمير، وإن ضرب ظهرك، وأخذ مالك، فاسمع وأطع"
“Wasu shuwagabanni zasu kasance a bayana, basa shiryarwa da shiryarwata, ba kuma sa tafiya akan tafarkina, kuma wasu mutane zasu tsaya a cikinsu zukatansu zukatan shedanu ne a cikin gangan jikin mutum, huzaifa yace sai nace ya zanyi in na riski wannan? Sai yace “kaji kayi biyayya ga shugaba koda ya doki bayanka ya dauke dukiyarka kaji kayi biyayya”
Malam da mabiyanka ku duba wannan hadisin, sa’annan ku kwatantashi da shugabannin Nigeria, ban san ko banda su a cikin hadisin ba, ko kuma wannan hadisin na nufin shugabanni masu adalci ne!!!
2-Imaam al-Bukhaaree da Imaam Muslim sun rawaito daga ‘Ubaadah dan Saamit (R.A ) ya ce:
"بايعنا رسول الله صلى الله عليه وسلم على السمع والطاعة في المنشط والمكره، وأن لا ننازع الأمر أهله، وأن نقوم أو نقول بالحق حيثما كنا، لا نخاف في الله لومة لائم"
“Mun yi mubaya’a ga manzon Allah akan ji da biyayya (ga shugaba) cikin jin dadi ko wahala, kuma kada mu yi sa’insan al’amari da ma’abotansa….”
A wata riwayar:
"وعسرنا ويسرنا وأثرة علينا"
“Da cikin tsananinmu da saukinmu, da kuma halin an mana qarfa-qarfa.”
3-Imaam al-Bukhaaree ya rawaito daga Abdullahi dan Mas’uud (R.A ) daga manzon Allah -sallallahu alaihiwasallam- ya ce:
"إنكم سترون بعدي أثرة وأمورا تنكرونها» قالوا: فما تأمرنا يا رسول الله؟ قال: «أدوا إليهم حقهم، وسلوا الله حقكم"
“Lalle ku za ku gani a bayana, wani irin mulkin mallaka, da abubuwa da dama da zakuke inkarinsu, sai suka ce: to me kake umartarmu dashi ya manzon Allah? Sai yace “ku sauke hakkokinsu dake kanku, ku kuma ku roqi Allah haqqinku”
Dukkanin hadisan nan basu rabewa wajen wajibcin biyayya ga shugaba da haramcin yi masa tawaye tsakanin azzalumi da kuma adali, ban kuma san malami daya daga cikin malaman sunnah ba da ya rabe tsakaninsu ba, Alhamdulillah kuma ina da malami a kan wannan magana tawa.
1- Sheikh Muhammad Amaan (R.A ) yake cewa:
لا يشترط أن يكون الوالي الذي تجب طاعته والسماع له والولاء له والدعوة له لا يشترط أن يكون عادلا"
..."
“Ba sharadi ba ne ya zama shugaban da da’arsa ta wajaba, da jin maganarsa da yi masa biyayya, da yi masa addu’ar alheri, ba sharadi bane sai ya zama mai adalci…..” Ka duba “Sharh al-Usuul al-Sittah”.
2- Imaam al-Barbahaaree haka (R.A) ya ce:
"ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه وإن جار"
“Ba ya halatta a yaqi shugaba ko kuma ayi masa tawaye koda ya yi zalunci”
3-Imaam al-Wawaawee shi ma ya ce:
"وأنه لا تسقط طاعتهم بظلمهم"
“Kuma da’a gare su bata faduwa don sun yi zalunci”
Da dama daga cikin malamai sun yi naqalin ijma’i a kan wajibcin biyayya ga shagabanni da kuma haramcin yi musu tawaye, sawa’un adilai ne ko azzalumai koma qwatar mulkin sukayi.
Kamar Haafidh Ibn Hajr a cikin ‘Fath al-Baaree [7\13] da kuma al-Nawaawee a cikin minhaj [12\229].
Amma abin da ya shafi yin mummunan addu’a ga shugabanni malamai suna sanya shi a qarqashin tawaye ga shugaba, kuma suna ganin wanda ya aikata haka ya bi hanyar khawarij.
‘Umar dan khattab (R.A ) ya ce:
"وإن ظلمك فاصبر وإن حرمك فاصبر"
“Idan shugaba ya zalunce ka ka yi haquri idan ya haramta maka hakkinka ka yi haquri”
Ban sani ba ko wannan Sahabin shi ma bai fahimci nassoshin shari’ah ba!
Hasan al-Basaree (R.A ) ya ce:
"لو أن الناس إذا ابتلوا من قبل سلطانهم صبروا ما لبثوا أن يرفع الله عنهم"
“Da a ce mutane idan aka jarrabe su ta fuskar shugabanninsu za su yi haquri da ba za su dau lokaci ba face Allah ya dage musu”
Imam al-Barbahaaree (R.A) ya ce:
"وإذا رأيت الرجل يدعو على السلطان فاعلم أنه صاحب هوى، وإذا رأيت الرجل يدعو للسلطان بالصلاح فاعلم أنه صاحب سنة إن شاء الله"
“Idan ka ga mutum na mummunar addu’a ga shugaba to kasan cewa: wannan mutumin dan bid’a ne, idan kuma ka ga mutum na kyakkyawar addua ga shugaba yana roqa masa shiriya to wannan maabocin sunnah ne inshaallah.”
Ya kuma ce:
"فأمرنا أن ندعو لهم بالصلاح، ولم نؤمر أن ندعو عليهم وإن ظلموا، وإن جاروا"
“Sai aka umarce mu da mu yi musu kyakkyawar addu’a ta neman shiriya, ba a kuma umarce mu yi musu mummunar addu’a ba koda sun yi zalunci”
Imaam Tahaawee ya ce:
"ولا نرى الخروج على أئمتنا وولاة أمورنا وإن جاروا ولا ندعوا عليهم ولا ننزع يدا من طاعتهم ونرى طاعتهم من طاعة الله عز وجل فريضة ما لم يأمروا بمعصية وندعو لهم بالصلاح والمعافاة"
.
“Kuma ba ma ganin halaccin tawaye ga shugabanninmu koda sun yi zalunci, kuma bama musu munanan addu’o’i …….muna kuma roka musu shiriya da kubuta.”
Wadannan kadan ne daga cikin abin da aka rawaito daga sahabbai, tabi’ai da jagororin ahlussunnah, sai dai malam ya ce: wannan fahimtar tasu ta hana a yi mummunan addu’a ga shugaba azzalumi kuskure ne, alhali wannan maganar tasu akanta magabatan al’umma suka kasance kuma ahlussunnah suke kanta, lalle ina shaidawa ya kamata malam ya raja’a fahimtarsa, ya mata garam bawul data wadannan.
Saboda muhimmancin wannan mas’alar (addu’a kyakkyawa ga shugaba da hani a kan mummunar addu’a) daya daga cikin bijiman malaman sunnah al-Imaam ahl al-Sunnah Yahya Bn Mansuur al-Harraanee ya kebance littafi sukutun da guda a kan wannan mas’alar kadai, ya yi masa suna "دعائم الإسلام في وجوب الدعاء للإمام".
Idan kuma kana so ka ga wanene wannan Imaamin ka duba littafin Ibn Rajab (R.A)
"ذيل طبقات الحنابلة"
Duk da cewa malam zai iya samun shubuhar cewa: ai wadannan ba khalifofin musulunci ba ne, ta hanyar ‘Dimokradiyya’ [Democracy] suka hau, to wannan za mu iya bada jawabi a taqaice ta fuskoki biyu.
1-Fuskar Naqali; lalle malaman sunnah suna ganin wajibci da kuma tabbatuwar dukkanin hukuncen shugabanci ga kowane shugaba musulmi ko da bai zama khalifa a tsarin musulunci ba matiqar shugabane.
Sheikh Muhammad Bn Abd al-Wahhaab (R.A ) ya ce:
"الأئمة مجمعون من كل مذهب، على أن من تغلب على بلد أو بلدان له حكم الإمام في جميع الأشياء، ولولا هذا ما استقامت الدنيا، لأن الناس من زمن طويل قبل الإمام أحمد إلى يومنا هذا، ما اجتمعوا على إمام واحد، ولا يعرفون أحدا من العلماء ذكر أن شيئا من الأحكام، لا يصح إلا بالإمام الأعظم"
“Imamai sun yi ijma’i daga dukkanin mazhabai cewa: duk wanda ya galabci wani gari ko wasu garuruwa shi keda hukuncin shugaba a cikin dukkanin abubuwa,…….kuma basu san daya daga cikin malamai da ya ce akwai wani abu na hukunci da baya inganta ba sai da babban jagora (khalifa).”
Haka an tambayi Sheikh Muhammad Bn Saalih Uthaimeen (R.A) a kan shugaban da yake hukunci da ‘Constitution’ kuma ya hau ta hanyar ‘Dimokradiyya’ shin za a yi masa biyayya?
Sai ya ce, ‘Yana sallah? Suka amsa, ‘Yana yi,’ sai ya ce, ‘Wannan shugaba ne na sharia wanda ya wajaba a yi masa da’a” Ya zo a ‘Liqa’ Baab al-Maftuuh’ ka kara duba littafin‘ al’Ilmaam Bi Manhaj al-Salaf Fee Mu’aamalah al-Hukkaam’.
2-Fuskar Hankali: malam yana ganin a shiga tsarin Dimokradiyya a yi zabe, wannan kuma daliline a kan yana ganin cewa shugaban da ya hau ta wannan hanyar na da hukuncin shugabanci a musulunci, to me zai sa a bashi wani sashen hakkin a hana shi wani, in ba dalili mai qarfi ba!
Malam zai iya cewa: “Ai arna ne!”
A nan za mu buqaci tafsili, na san cewa ni da malam duk mun yarda cewa mutum ba ya kafirta saboda sabo da ya yi matuqar bai halatta shi ba, haka ba kowane mai taimakon kafiri ba ne ke zama kafiri, bisa ginshikai da suka tabbata a wajen Ahl al-Sunnah wa al-Jamaa’ah, saboda haka mun yarda cewa wadannan azzaluman mafi yawansu musulmai ne, idan ko har musulmai ne, to akwai sabani mai girma a kan halaccin ka ayyana fasikin musulmi ka tsine masa, kuma maganar da tafi qarfi ita ce bai halatta a ayyana shi a tsine masa ba, Ibn al-Arabee al-Maalikee (R.A ) ya ce:
"فأما العاصي المعين، فلا يجوز لعنه اتفاقا"
“Amma ayyanannen mai sabo bai halalta a tsine masaba bisa ittifaqi”
Sheikh al-Islaam Ibn Taimiyyah ya ce:
"أما ما نقله عن أحمد، فالمنصوص الثابت عنه من رواية صالح أنه قال: " ومتى رأيت أباك يلعن أحدا؟ لما قيل له: ألا تلعن يزيد؟ فقال: ومتى رأيت أباك يلعن أحدا؟ وثبت عنه أن الرجل إذا ذكر الحجاج ونحوه من الظلمة وأراد أن يلعن يقول:( ألا لعنة الله على الظالمين) وكره أن يلعن المعين باسمه" :
“Amma abin da ya naqalto daga Ahmad, to abin da aka nassanta ya kuma tabbata daga gare shi daga riwayar salihu ita ce cewa: shi ya ce yaushe ka ga babanka yana tsinewa wani? Lokacin da aka ce ya tsinewa Yazid, kuma ya tabbata daga gare shi cewa: mutum in an ambaci Hajjaaj da wasunsa na daga azzalumai in yaso ya tsine cewa yake “tsinuwar Allah ta sauka a kan azzalumai” yana qin ya tsine wa mu’ayyani da sunansa.
Shi kuma shugaba kafiri malamai da dama kamar Ibn Munzur sun naqalto ijma’in al’umma a kan cewa: ba shi da haqqin shugabanci a kan musulmai, amma duk da haka malamai sun sanya sharuda da sai sun cika ake iya fito-na –fito da shi, kamar samun cikakken iko da kuma qarancin mafsada.
Sheikh Ibn Baaz (R.A ) ya ce:
"أما إذا كان الخروج يترتب عليه فساد واختلال الأمن وظلم الناس واغتيال من لا يستحق الاغتيال، إلى غير هذا من الفساد العظيم فهذا لا يجوز"
“Amma idan ya zama sababin tawayen za a haifar da barna da matsalolin tsaro [Security] da amincin mutane , da kashe wanda bai cancanci kisa ba, da wasun wadannan na daga barna mai girma, to wannan bai halatta ba.”
Sheikh Muhammad Bn Saalih al‘Uthaimeen (R.A) ya ce :
"وإذا فرضنا أن ولي الأمر كافر فهل يعني ذلك أن نوغر صدور الناس عليه حتى يحصل التمرد والفوضى والقتال؟ لا هذا غلط ولا شك في ذلك"
“Mu qaddara cewa shugaban ya zama kafiri ma, shin hakan na nufin mu ingiza zukatan mutane akansa, har ya jawo tawaye, da hayaniya, da kashe-kashe? A’a wannan kuskure ne kuma ba bu shakka a kan hakan.”
Lura : duk da cewa bana inkarin mutane su roqi Allah ya canja musu, ya kuma qwata musu haqqinsu, kuma banbanci ne bayyananne tsakanin wannan da kuma tsinuwa da zage-zage wanda ba abin da za su haddasa face fitina da barna a doron qasa.
Dalilan malam kuma:
1-Hadisin qunutin Annabi -sallallahu alaihi wasallam- da munana addu’a ga Quraishawa da kuma hadisin tsinuwarsa ga Riil da Zakwaan da ‘Usayyah ba nan ne mahallinsa ba, saboda ba bu malami daya cikin malaman sunnah –iya sanina- da ya dora wadannan hadisai a kan halaccin mutum ya yi qunutin munanan addu’o’i ko tsinuwa ga shugabanninsa azzalumai, hasalima sun fito qarara sun ce wadannan hadisan suna nuna halaccin tsinewa kafurai da yahudawa ne, kamar yadda suka sarraha hakan, daga cikin wadanda suka sarraha hakan akwai Imaam Maalik, da Ibn Abd al-Bar a cikin ‘al-Istizkaar’ da ‘Tamheed’, haka ma al-Nawaawee a cikin ‘Minhaj’, da kuma Ibn Battal, haka Muhallab, da wasunsu. Ban san a ina malam ya samo dora su a kan shugabannin mutane azzalumai ba!
Qari a kan haka, gaba daya in ka duba wadannan hadisai babu daya daga cikin mutanen da Annabi –sallalhu alaihi wasallam- ya tsine wa da ya kasance shugaba a kansa a lokacin tsinuwar, sa’annan ba bu daya daga cikinsu da ya kasance musulmi, dukkaninsu shugabannin kafirai ne, ta yaya wannan zai zama dalili a kan abin da malam ya kawo?! Bayan yadda haqiqanin surar take ita ce: “Shugaban musulmai na alqunut da tsinuwa ga shugabannin kafirai wadanda ba ya qarqashinsu” sa’annan kuma su kansu wadannan kafurai akwai wadanda Annabi –sallallahu alaihi wasallam- ya yi alqunut a kansu ya tsine musu Allah (S.W.T) kuma ya hana shi kamar yadda Imaam al-Bukhaaree ya rawaito:
"عن ابن عمر أنه سمع رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا رفع رأسه من الركوع من الركعة الآخرة من الفجر يقول: «اللهم العن فلانا وفلانا وفلانا» بعد ما يقول «سمع الله لمن حمده، ربنا ولك الحمد» فأنزل الله: {ليس لك من الأمر شيء} [آل عمران": 128]- إلى قوله - {فإنهم ظالمون} [آل عمران: 128]
A wata riwayar:
" "يدعو على صفوان بن أمية، وسهيل بن عمرو، والحارث بن هشام
Wannan na qarfafa maganganun malaman da suka ce koda kafiri ne ayyananne haramun ne ka tsine masa.
Haka shi ma ‘Ali (R.A ) a lokacin siffin ne ya yi alqunut a kan wasu mutane da ya yaqa, ka ga nan ma ‘Ali shugaba ne ya yi addu’a a kan wadanda ke mulkar wasu mutane daban, shi ma baka da dalili a ciki.
Ga kuma abin da Imaam al-Nawawee ya ce a kan wannan hadisin da ka kafa hujja dashi:
"وفيه جواز لعن الكفار جملة أوالطائفة منهم بخلاف الواحد بعينه"
Ibn Taimiyyah kuma da ka yi naqalin maganarsa, ga tafarkinsa a kan haramcin tawaye wa shugaba, ya ce :
"إن المشهور من مذهب أهل السنة أنهم لا يرون الخروج على الأئمة وقتالهم بالسيف وإن كان فيهم ظلم"
Za ka samu wannan magana a cikin ‘Minhaaj al-Sunnah’.
Ya kuma cewa:
"وأمر بالصبر على جور الأئمة وظلمهم"
Za ka samu wannan a cikin ‘al-Fataawa’.
Wannan shi ne ra’ayin Imaam, wannan ya nuna cewa abin da hadisan nan da malaman nan ke Magana akai daban da abin da malam yake kafa hujja dasu akai.
Sa’annan kuma babin ilmi in ba a hado hanyoyinsa ba ba a gane kuskurensa kamar yadda magabata suka fada.
2-Hadisan da Annabi -sallallahu alaihi wasallam- ke addu’a ga azzaluman shugabanni basa halatta wa mutane su yi munanan addu’o’i a kan shugabanninsu, saboda hadisansa da suke mutawatirai dake umurni da haquri a kan zaluncin shugaba, kuma suna fassara wadannan hadisan ne, suna karantar da cewa kada shugaba ya ga don an hana talaka qwatan haqqinsa ya dauka ko Allah ya ba shi damar ya yi zalunci ne, sa’annan kuma suna tsoratar da azzalumin shugaba makomar zaluncinsa, domin Annabi ba wani shugaba mu’ayyani ya yi wa wannan addu’ar ba, sa’annan ba bu wani magabaci da ya fahimci wadannan hadisan a bisa wannan fahimtar taka, dauko tun daga sahabban da suka rawaito hadisan, da kuma wadanda suka rayu a lokacin azzaluman shugabannni, misali: Ummu al-Mumineen A’ishah (R.A ) ita ta rawaito hadisin addu’a, amma ba za ka iya samo harafi daya nata da ta yi mummunar addu’a ga wani shugaba dake mulkanta ba, hakanan sahabban da suka riski Hajjaaj duk an rawaito maganganunsu a kan a yi haquri da zaluncinsa amma babu riwaya daya tal a kan mummunar addu’a ko tsinuwa, kamar sahabi Abdullahi dan ‘Umar, da Anas (wanda shi ya rawaito hadisin Ri’il da Zakwaan), Ibn Abbas, D.S. Haka nan Maaqal dan Yasaar (R.A) da ya rawaito hadisin haramtawa shugaba mai ha’inci al-Jannah, ya riski ‘Ubaid Allah dan Ziyaad wanda anyi ittifaqi a kan zaluncinsa, amma ba bu harafi daya na mummunar addu’a ko tsinuwa daga daya daga cikin sahabbai dukkaninsu suna umarni da hakuri da roqon Allah ya kawo musu mafita.
Haka nan magabatan Al’umma, irinsu Imaam Maalik sun riski irin abu Jaafar al-Mansur azzalumi ne kuma kissar shi da su ba ta buya muku ba, amma ba bu harafi daya na mummunar addu’a ko tsinuwa daga bakinsa, haka nan Imam Ahmad ya yi gwagwarmaya da shugabanni da ke lazimtawa mutane kafirci suke tilasta musu shi, kamar Ma’amun, da Mu’utasim, da al-Wathiq D.S. Amma ba bu kalma daya daga gare shi ta tawaye ko mummunan addu’a ko tsinuwa.
Dukkanin wadannan magabata na al’umma fitulun shiriya ba su fahimci wadannan hadisan a yadda malam ya fahimcesu ba, ba su kuma halatta yi wa azzaluman shugabanni munananan addu’o’i ko tsinuwa ba, kuma gashi malam ya ce ba me fahimtar nassosi irin wannan fahimtar tasu sai wanda ya jahilci nassoshin shari’ah!!
Lalle akwai bukatar malam ya sake duba wannan maganar ya kuma yi wa kansa da dalibansa adalci.
Sa’annan mas’alar Qunuuh al- Nawaazil duk da cewa ba zan yi wa malam ilzamin daukan ra’ayi ba, amma akwai sabani a tsakanin magabatan al’umma a kan halaccin yin qunutin nazilah ba tare da iznin shugaba ba, wannan kuma shi ne zahirin maganar Imaam Maalik, shi ne kuma ra’ayin Imaam Ahmad, Imaam Maalik ya ce :
"فإن دعا الإمام على عدو للمسلمين واستسقى لم أر بذاك بأسا"
“Idan kuma shugaba yayi addua (mummuna) akan maqiyan musulmai, kuma yayi roqon ruwa bana ganin lefin hakan.
Sheikh Ibn ‘Uthaimeen (R.A) ya ce:
"إذا أطلق الفقهاء "الإمام" فالمراد به : القائد الأعلى في الدولة، فيكون القانت هو الإمام وحده، أما بقية الناس فلا يقنتون"
Wannan kuma shi ne abin da Sheikh ‘Uthaimeen ya rajjaha kamar yadda ya gabata, hakaSheikh Saalih Fauzaan, Sheikh Saalih Ali Sheikh D.S.
Wannan kuwa na nuni da cewa wadannan malamai ba su ganin halaccin sanya addu’ar qunuti a kan shugaba, tunda asalin yin qunutin ma sai da izininsa.
Abu na gaba, shin magabata na sanya zaluncin shugaba a matsayin nazilah da ake qunuti a kai?
Ba shakka an rawaito qunutin sahabbai da magabatan al’umma a kan kafurai, amma ba a naqalto cewa su na qunutin nazilah saboda wani shugaba ya yi zalunci ba! Bal ma abin da aka rawaito daga gare su akasin haka ne, domin an rawaito daga wasunsu idan shugaba yana zalunci su kance sabon Allah da mutane ke yi ya jawo wannan zaluncin, wannan kuma ba ya buqatar naqalin misali saboda yawansa.
Abu na qarshe: malam kamata ya yi a matsayinka da Allah ya kai ka ka yi amfani da shi wajen saukar da tarzoma, da hana mutane hayaniya da zage-zage da cin mutunci, wanda hakan kawai shi zai sa qasarmu ta samu gobe mai kyau, ba wai kuma a ce kai zaka kuma mai iza su ba, wallahi idan komai ya rikice minbaran da kake samu ka isar da saqon Allah sai sun gagareka hawa, sukunin da kake samu ka hau internet sai ya gagare ka, ashe kenan ba mafita ba ne wannan karantarwar, kuma dukkan alheri na cikin fahimtar magabata.
Ina roqon Allah (S.W.T) ya gafarta mana da kai, ya kuma shiryar da shi baki daya zuwa ga abin da zai yardar da shi, ya kuma yi mana chanjin shugabanni da mafi alheri, ya kuma shiryar da wadannan azzalumai ya nuna musu gaskiya, yasa su yi abin da zai taimaki talakawansu, da addininsu da qasarsu.
Wallahu A’alam.

تعليقات
إرسال تعليق