*DAGA CIKIN ALAMUN HARAKIYYUN/SIYASIYYUN AKWAI WASA DA NASSOSHIN SHARI'AH!*
Daga alamun sakarkarun harakiyyun/siyasiyyun: karanta aya ko hadisi da sauke wa akan wani dan takara, don yabon sa ko zargin sa, a lokacin siyasa ba ruwan su da komawa zuwa ga fahimtar magabata na kwarai ga nassoshin shari'ah, kuma babu ruwan su da tafarkin magabata domin bace musu yake yi bat a wannan lokacin, saboda fitinar da suka jefa kawunan su ta shiga inda Allah da Manzon sa basu umurce su da shiga ba, ta sanya su suna makancewa basa fahimtar daman su daga hagun su.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyyah -Allah ya jikan sa- yana cewa:
من ظنّ أنه يأخذ من الكتاب والسنة بدون أن يقتدي بالصحابة ويتبع غير سبيلهم فهو من أهل البدع
(الفتاوى ٤/ ٥٥٦).
Duk wanda ya dauka cewa shi zai yi riko da Al- Qur'ani da Sunnah ba tare da yayi koyi da sahabbai ba, kuma in ya kasance yana bin wani tafarki wanda ba nasu ba to shi yana daga cikin 'yan Bid'ah
(Al- Fatawa 4/556).
Abinda yake wajibin Al- Ummah masu da'awa da ma kowa da kowa shine komawa zuwa ga fahimtar magabata na kwarai a dukkanin lokaci, a cikin kowane yanayi da sha'ani na addini, da kuma barin tafarkin rudaddu masu karkatar da maganar Allah madaukaki da ta Annabin sa (Sallallāhu 'alayhi wasallam) don cinma wani buri na rayuwar duniya, na samun yardar wani uban gida ko wani dan takarar siyasa, ko don dadada wa wani ko wasu, ko don muzanta wa wani ko wasu, kuma wajibi ne ga kowa karbar gaskiya da mika wuya ga hukuncin Allah da manzon sa a duk lokacin da hakan ya kai ga mutum, a cikin yardar zuciya ko rashin yardar ta.
Allah ya kare mu da tafiya akan matafiya irin ta Harakiyyun/siyasiyyun, ya kuma datar damu da dukkan musulmi ya zuwa ga bin tafarkin Annabi da Sahabban sa, kuma ya dauki rayukan mu akan haka, ba kwaskwarima ga tafakin mabarnata, kuma babu mudahana ga duk wanda ya sabawa tafarkin Annabta ya fuskanci wani tafarki wanda yake sabanin tafarkin Annabi da Sahabbai.
أمين ثالث يعقوب
08 / 05 / 1440
15 / 01 / 2019

تعليقات
إرسال تعليق