Salafawa Ba 'Yan Ta'adda Ba Ne!
Karyar jingina wa Salafiyyah kashe Dr. Nadir al-'Umraanee (R. A) Su Dr. Mansur Sokoto da Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo suka koya wa almajiransu tun November 2016 a cikin wancan Group na Whatsapp mai suna 'Mu'assasatu AhlIl Hadeeth'.
Saboda haka ba komai ba ne don wani mabarnaci daga cikin matasan da suke neman gindin zama a wajensu ya jefi Salafawa da shi a bainar jama'a, tare da cewa malamansa sun kudurce haka, amma sun kasa bayyanawa sai a kebe, sai shi saboda neman kusanci gare su, tare da cewa wannan jinginawa karya ce tsagoranta, dalilai mabambanta sun tabbatar da haka, kamar:
1. Ganin halaccin kashe wani musulmi ba tafarkin Salafiyyah ba ne, koda kuwa ya aikata abin da ya cancanta a kashe shi suna wakilta kisansa ga mahukunta.
Hakika Salafawa ba sa daukar doka a hanunsu kamar yadda Khawarijawa, da Shi'ah, da Ikhwaniyawa da sauran kungiyoyin bidi'ah da zafin kai suke yi.
2. Sheikh Muhammad Sa'eed Raslan (H. A) da ake jingina dalibtar wanda ya yi kisan a wajensa babu wani dalili da yake tabbatar da haka, bal ya karyata ta, kuma haka dalibansa da suke alaka da kowane dalibi da ya halacci kauyen nasa domin daukar karatu.
3. Wannan yana kara tabbatar da zaluncin da yake wajensu ga Salafawa mai yawa ne, in har za su-yi-ruwa su-yi- tsaki a wajen barrantar da Sheikh Ja'afar da Albanin Zaria (R. A) daga badakalar alaka da jagororin Khawarijawan Nigeria 'Boko-Haram' tare da samuwarta a wani lokaci wanda ba za a iya karyatawa ba, saboda me ba za su iya haka ba domin barrantar da wani malamin sunnah wanda ya fi su kyakkyawar akida da tsaftataccen manhaji?!
Saidai wadancan malamai sun barrantar da kansu daga wadancan Khawarijawa a karshe, kuma sun bayyana matsayinsu a kansu, amma wasu mutane ba su bar jingina musu da su ba, wannan jinginawa ba za ta zama abar dauka ba koda ta kasance tabbatacciya a baya.
A karshe: Inda a kan adalci da insafi suke tafiya da ba za su rinka jingina wa Salafawa abin da suka barranta daga gabarinsu ba, kamar wannan batu da batun Kungiyanci wanda suka koya wa mabiyansu jifan Salafawa da shi saboda barna da barnatarwa.
Kuma inda suna da gaskiya da kunya da ba za su barrantar da malamansu a Nigeria daga Ta'addanci ba, sa'annan kuma su rinka jingina ta'addanci ga malaman da suka fi su ingantacciyar akida da tsaftaccen manhaji!
Wannan shi ne zaluncin nasu, kuma shi ne yake nuna kokarinsu na kange daliban ilmi daga malaman sunnah na hakika wadanda suka karantar da duniya gangariyar sunnah!
Shi ya sa ban ji mamakin tsoratarwar Dr. Mansur Sokoto ga dalibai a lokacin da ya zo Egypt shekarun baya a kan zuwa karatu wajen Sheikh Dr. Muhammad Sa'eed Raslan (H. A) ba, saboda kawai yana bankade halin Ikhwaniyawa 'Yan Kungiyarsa, in kuwa bayyana halin Ikhwaniyawa ya kai a ce kar a halarci karatun malami, lallai wanda ya ce yana goyon bayan fito-na-fito da shugabanni shi ya cancanta a tsoratar gabarin halartar karatunsa, haka mai sharri ga Sallafawa da jingina musu sunayen banza da wofi.
Wanda ya fada min wannan labari na tsoratarwar shi Dr. Mansur Sokoto din wani dalibi ne dan kasar Niger da ya zauna a Kano, Nigeria, kuma yake karatu a nan Egypt, sunansa Yusuf, ana yi masa lakabi da al-Kutuby, kuma ya tabbatar min cewa a dakinsu dake Masaukin Daliban Jami'ah ta Azhar ya fada masa, kuma na aminta da wannan labari, domin ya kawo shi ne yana mai kokarin kafa min hujja da tsoratarwar Dr. Mansur din, sa'annan da rashin amincewarsa da malamin, da kuma bayyana goyon bayansa ga Ikhwaniyawa da tausaya musu.
Kari a kan haka: Dalilin da ya sa muka fara magana da shi a kan wannan batu shi ne: Wata rana muna cikin Jami'atul Azhar a 'Bangaren Gudanarwa' (Administrative Block) sai 'Yan Tsakin Ikhwaniyawa suka kewaye shi suna zanga-zanga, a karshe saida ya kai ga kulle kofofinsa gaba daya, domin burinsu shigowa cikinsa.
Kasancewa tare da shi a cikin wannan yanayi shi ne dalilin da ya sa muka fara tattaunawa a kan wannan batu, har ya kai ga fada min matsayin malaminsa a kansu da mai musu martani.
A tare da rubutun nan za ku ga wasu hotuna da suke tabbatar da abin da nake fada, a cikinsu za ku ga bayan kokarin tabbatar da wancan zargin da Dr. Mansur ya yi, kuma za ku ga yana kokarin jifan Salafawa da Murji'anci tare da shugabanni, alhali kungiyar da yake karkata zuwa gare ta, wato Ikhwan al-Muslimeen su ne Murji'ah, saboda matukar mutum ya kira kansa musulmi shi kenan a wajensu, shi ya sa kungiyar tasu ta zama ta matattarar kowane mai karkataccen tunani da bidi'ah.
Kuma shin biyayya wa Shugabanni kuskure ne, ko Dr. Mansur yana kokarin bayyana manhajinsa ne na Ikhwaniyanci wanda yake da alaka da tawaye ga Shugabanni da muzanta su?!
Fadinsa cewa Salafawa Khawarijawa ne tare da Malamai, wannan karya ce ita ma, domin ba su kangare wa wani malami na kirki ne, bal sune Khawarijawa ga malamai, domin malamai sun yi bayanin haramcin fito-na-fito da shugabanni, amma ire-irensa suna ganin halaccin haka, malamai suna ganin rashin halaccin inkari ga shugaba a kan minbarori, su kuma suna ganin halaccin haka, tare da cewa malamai ba su haramta wadancan batutuwa da ra'ayinsu ba, bal sun haramta su ne da nassoshin shari'ah, duk abin da ya tabbata da nassi kuma bai halatta ga wani ya saba masa da sunan Ijtihadi ba, saboda ba a ijtihadi a gurbin nassi.
©Ibrahim Lawal Soro
26. 01. 2018 C. E

تعليقات
إرسال تعليق