Warware Shubuhohin Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo Cikin Rubutunsa Mai Take ‘Ba Haka Lamarin Yake Ba!!’

Hakika adalci al’amari ne da aka yi umarni da shi a gudanar da kowane bangare a cikin Shari’ar Musulunci, masu tutiya da shi sun yawaita, alhali ma’abotansa na gaskiya sun karanta ma’abotansa sun karanta; ko shakka babu Dr. Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo da ire-irensa daga cikin masu zagon kasa ga Da’awar Salafawa suna cikin masu kururuwar tsaida adalci, amma alakarsu da shi ta karanta, saboda idan ka ga suna magana a kansa, lallai suna bada kansu kariya ne, ba wata gaskiya da suka ga ana son karyatawa ba, ko wani malamin kirki da ya saba musu ana son bata shi ba, zan tabbatar da wannan batu –in sha Allah- a cikin wannan takaitaccen rubutu domin warware shubuhohin da ya kulla.

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Wasu suna daukar duk wanda ya tsawatar a kan sukan malaman sunnah da jifansu da bidi'a cewa shi dan Ikhwan ne, alhali ba haka abun yake ba.”

Na ce:

A farko yana da kyau ya bayyana wadanda yake nufi da ‘wasu’ domin saukake wa masu karatunsa al’amari, sa’annan da yanke wa wadanda yake magana a kansu uzuri, idan ya yi haka tabbas ya dauki Malaman Sunnah a yayin tsoratarwa, musamman dangane da al’amari mai muhimmanci irin wannan, amma sai nake ga kamar dalilin da ya sa yake wannan rara—gefe shi ne: tun asali ya girmama kansa a kan wadanda yake magana a kansu, tare da fadakar da shi cewa: wadanda yake jayayya da su a kan wadannan batutuwa ba kowa ba ne face malaman da ya yi karatu a gaban wasunsu, domin duk wani jifa da yake yi wa Salafawa, musamman a Nigeria, bai tsaya a kansu ba, lallai ya tsallake kan malamansa da ya kangare musu, kuma ya bi bayansu da munanan maganganu marassa dadin ji a kan batutuwan da shi ne jahili a kansu ko dan son zuciya.
Abin da nake nufi: a cikin kashi dari na batutuwan da ire-irensa suke rushewa, tabbas Malamman Sunnah na hakika, kamar: Ibn Baaz, al-Albaanee da ‘Uthaimeen sun tabbatar da su, amma sai ka ga suna daukar maganganun wasu kangararru ga Dalilan Shari’ah, suna barin maganganun wadancan malamai da suke fakewa da su a kan wasu bukatunsu, bal wasu a cikinsu ma suna daukaka kansu zuwa ga matsayinsu, suna ganin kamar yadda suke malamai, haka su ma suke malamai, ma’ana suna tafiya a kan waccar ka’idar ta kangararru, kamar: Ikhwaniyawa, Khawarijawa da sauran masu tafiyar a cikin addininsu a kan tsagoron ra’ayi, waccar ka’idar kuwa ita ce:

“هم رجال ونحن رجال”

“Su mazaje ne, mu ma mazaje ne”

Saboda haka ba za ka taba jin kamshin sunayensu a kan harshensu ba, idan kuma ka ji, to sun dauko wata magana ce da za su yi amfani da ita domin biyan wata bukata ta kashin kansu, kamar: tabbatar da abin da suke kai na wata rinjayayyar fahimta a cikin addini, ko koyon bayan wata barna wacce suke gani idan an bayyana ta kamar an bayyana abin da suke kai ne na bacin tafarki dangane da ita ne, misali: Barnar ‘bidi’ar muwazanaat’ da sauransu.

Batun cewa ana jifan wadanda suke kare malamai daga cin mutunci da bidi’antawa da Ikhwaniyanci bayani a kansa zai kasance kamar haka:

 Ikhwaniyawa ba su san mutuncin malamai ba, saboda galibinsu ba daliban ilmin addini ba ne, galibinsu daliban ilmin sana’a ne, shi ya sa a cikinsu daga Lawyer, da Engineer, sai Docter da sauransu, wadanda suka nemi ilmin addini ma a cikinsu sun fi kowa cin zarafin  malaman addini, domin sune suke jingina malaman da sunaye na batanci kamar haka: ‘Malaman Fada’ [علماء السلطان] ko ‘Malaman Haila’ [علماء الحيض]  ko su danganta su da jahiltar ‘Batutuwa Masu Gudana’ [Current Affairs-فقه الواقع] da sauran sunayen banza da suke danganta su das hi, a cikin mafi shahararsu da bayyana manhajinsu akwai kiransu ga Salafawa da ‘Jaamiyyah da Madaakhilah’ [جامية ومداخلة] ko ‘Yan zurfafawa a cikin bidi’antarwa da rotse’ [غلاة التبديع والتجريح].

Kari a kan haka: Abin mamaki irin masu wadannan aika-aika ga malamai wai sune Dr. Muhammad Rabi’u zai ce Salafawa suna danganta masu kare malamai da su, alhali ba wanda ya fi su cin mutuncin malamai da bakanta su mataukar sun bayyana batar uwar gijiyarsu, wato Ikhwan al-Muslimeen a game, ko Suruuriyyah a kebe.

Dalilan da suka sa ake danganta masu bada mabarnata kariya da Ikhwan al-Muslimeen ba su wuce kasancewarsu masu bada kariya ga kowace irin kungiyar bidi’ah ba, matukar ta yi imani da manufofi da tsare-tsarensu na siyasa, ko saboda galibin mabada kariya ga mabarnata yayanta ne na asali ko wadanda suka cafki tafarkinta, saboda sun yi imani da ka’idar nan tata wacce take kira ‘Ka’ida ta Zinariya’ [القاعدة الهبية]  ko ‘Ka’idar Uzuri’ [قاعدة العذر] wacce take tabbatar da uzuri da bada kariya ga duk wanda y ace yana tare da ita duk munin akidarsa da bacin tafarkinta.

Inda Dr. Muhammad Rabi’u mai kare malamai ne wanda hakan yake nuna adalcinsa da gaskiyar maganarsa, tabbas da bai kasance na gaba-gaba a wajen karya da kage ga malaman sunnah ba.

Karyar da nake magana a kanta wacce ya shirga it ace: Wai Sheikh Rabee Bn Hadee al-Madkhalee [H.A] ya yi Fatawa ga Musulman Libya su daga makami, shi ya sa muke ta bukatar ya kawo fatawar domin tabbatar da haka, idan kuma ya kasa, to dama a haka muka dauki maganarsa, kuma abin da ya yi shi ne cin mutuncin malamin da ya zama malami tun a lokacin da malaman da suka yi fice a wannan zamani da ilmi da amana suke raye, kowanne a cikinsu ya yi yabon alheri gare shi, kuma ya karfafa shi a kan aikinsa na bankade barna da ma’abotanta.

Goyon bayan kage kuma da na ce ya yi shi ne a lokacin da ya ce Sheikh Raslan [H.A] yana da alaka da kisan da aka yi wa wani malami a Libya, saboda wanda ya yi kisan ya ce shi dalibinsa ne, alhali Sheikh Raslan din ya barrantar da kansa daga gare shi, kuma dalibansa sun tabbatar da rashin samuwarsa ko halartarsa ga majalisinsa koda sau daya ne, amma tare da haka Dr. Muhammad Rabi’u ya hakikance a kan tabbatar da alhakin kisan ga barrantacce, wato Sheikh Raslan [H.A].

Tambaya a nan ita ce: shin wadannan ba malamai ba ne, ko ba ya daukarsu a matsayin malamai saboda sun bankade halin mabarnatan da yake dauka a matsayin malamai?!

A karshe: Lallai Salafawa sun fi shi sanin cewa: ba duk wanda ya kare wani malami ba ne daga jafa’in masu jafa’I yake kasancewa Ba’ikhwaniye, amma ha’inci ne Ba’ikhwaniye kamar  Nura Musa ya fito ya yi batanci ga Malamin Kirki, Makiyin Sharri, Mai son ci gaban Sunnah, irin Sheikh Rabee [H.A] kuma a ce wani marayin Sunnah ya fito yana kare shi da wasu wulakantattun jumloli wadanda suke dauke da kwange, harda ma saba ka’idojin rubutu.

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Sukan Malaman Sunnah, wadanda suka ba da lokacinsu da rayuwarsu wajen yada sunnah da fada da bidi'a, don sun fada cikin wani kuskure wanda dukkan dan Adam zai iya fadawa ciki - sai wadanda Allah ya kare - manhaji ne sabo, kuma ba a gina shi a kan ilimi da adalci ba, kuma ba manhajin salaf ba ne.”

Na ce:

Wannan shubuha mun sha warware ta a gurabe mabambanta, amma babu laifi mu takaice waccar warwarar a nan kamar haka:

1. Kuna hada tsakanin ‘Kuskure’ [خطأ] da ‘Karkata’ [إنحراف] alhali kun san cewa malamanku sun bambance tsakanin haka, kuma sun sanya ka’idojin mu’amalantar duk wanda ya fada daya a cikinsu, amma saboda rashin kiyaye amanar ilmi sai ku rinka dora ajiye karkata a gurbin kuskure ga malaman da kuke ki, sa’annan ku ajiye kuskure a gurbin karkata ga malaman da kuke so.

2. Idan mutum ya fada cikin wani kuskuren da ba wanda ya fadakar da shi a kansa har Allah [S. W. T] ya karbi ransa, lallai wannan ana yi masa uzuri, kuma ana yi masa tsammanin inda yana da rai aka gyara masa zai iya karban gyara, saboda haka ake daukarsa a matsayin mutumin kirki, bawan Allah wanda ya mutu tare da wani kuskure wanda ba za a bar bayyana wa mutane shi ba saboda kar su fada a cikinsa.

3. Idan yana yare har aka samu damar gabatar masa da nasiha a kan kuskurensa, amma sai ya kangare, lallai sunan wannan kangarewar tasa karkata, saboda haka abubuwan da ya rubuta bayan karkatarsa ba a la’akari da su, bal har wadanda ya rubuta kafin karkacewarsa, domin a cikin alkintattu za a iya samun wadanda suka yi rubutu mai fa’idantarwa sama da nasa, saboda karanta rubutunsa zai iya kasancewa tallata shi ko ya dauki kansa a matsayin mai muhimmanci bayan tafiyarsa.

Salafawa sun barranta daga wadanda suke cin zarafin malaman da suka fada wani kuskure wanda nasiha ko ilmi bai isa gare su ba har Allah [S. W. T] ya karbi ransu. Masu aikata irin wannan aika-aika sune Khawarijawa da Haddaadiyyah, Salafawa sun fi kowa martani gare su a kanta, saboda haka danganta aikinsu da su, shi ma ha’inci ne!

Hidimar malami ga addinin Allah [S. W. T] ta hanyar karantarwa ba wanda zai hana a bashi ladansa, bal wannan al’amari ne a tsakaninsa da Ubangijinsa, saboda haka kokarin daukowa abin da yake tsakaninsu zuwa tsakanin jama’ah shi ma wata shubuhar ake kokarin dasawa da shi, in ba haka ba, kowa ya sani duk wanda ya yi wani aiki na alheri za a saka masa da shi, amma wannan aikin nasa ba zai sa a yi shiru gabarin kuskurensa ko karkatarsa ta fuskar tsoratar da mutane gabarinsu ba.

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Littafan malamai magabata cike suke da bada uzuri ga yan uwansu malamai, wadanda suka dauki nauyin yada sunnah da fada da bidi'a, da karantar da mutane, yayin da suka fada cikin wani kuskure.”

Na ce:

Amsa ga wannan shubuha sune wadannan tambayoyi:

Shin bada uzurin magabata ga junansu ya hana su bayyana wa mutane kuskurensu, ko sun yi musu rufa-rufa a kan kuskuren da suka fada, idan su yi musu sai a kawo mana misali koda daya ne?

Abin da muka sani shi ne: sun yi uzuri wa juna a kan bin da yake bukatar uzuri, amma ba wanda ya fada cikin wani kuskuren da ba ya bukatar uzuri, kamar na akida da manhaji, sa’annan bayan sun bayyana masa gaskiya, kuma suka bar shi a kan abin da yake kai ba tare da yanke masa uzuri wancan uzuri ba.

Shin batun uzuri ga wanda ya kangare a kan wani kuskure ba shi ne manhajin Ikhwaniyawa ba, to me zai hana idan shi ne a hade mai kira zuwa ga re shi da su?!

Dr. Muhammad Rabi’u y ace:

“Babu ko shakka 'yan ikhwan ba sa kan manhaji na daidai. Kuma tafiyarsu cike take kurakurai, amma wannan baya nufin babu malamai wadanda malamai da daliban ilimi zasu amfana da su ba.”

Na ce:

Wannan magana taka ita ce ‘Bidi’ar Muwazanaat’  [بدعة الموازنات] wacce kuke yawan lullube ta da rigar adalci da insafi, kuma harda kasancewarta bidi’ah, ba kwa iya sauke ta ga Salafawa, amma kuna iya mu’amalantar Yan Bidi’ah da ita, wannan yake nuna cewa dama bidi’ah ce da aka kirkira muku domin bada kariya ga barna da ma’abotanta, in ba haka ba, inda tabbatarwarka ga bacin tafarkin Ikhwaniyawa na gaskiya ne, saboda me za ka hada alakar wani malami mai dauke da tafarkinta da wani dalibin da zai iya lalata masa tunaninsa koda ‘Lissafi’ [Mathematics] yake karantar da shi?

Ko shakka babu, wannan bidi’ah duk wani malami da ake la’akari da ilmi da amanarsa a wannan zamani ya amince da kasancewarta bidi’ah, haka duk wani Ba’ikhwaniye wanda yake bada jama’ar kungiyarsa kariya ya tabbatar da sabanin haka, ko kuma da wahala ka samu Ba’ikhwaniye bai amince da ita ba, musamman dangane da wadanda suke kan manhaji irin nasa.

Dr. Muhammad Rabi’u y ace:

“Yana daga cikin abin da yake nuna munin wannan manhaji shagaltuwar ma'abotansa da suka da batanci ga malaman Sunnah, koyaushe ba su da aiki sai sannafa malamai da siffata su da sunaye kala-kala wadanda suka kirkire su, irinsu : Hizbiy, Ikhwaniy, Mumayyi'i, Sufiyuun Mutasattir, da makamantansu. Wani abin takaici ma shi ne kullum bakunan wadannan mutane da alkalumansu suna kan yan uwansu Ahlussunnah, kafin su rubuta littafi daya, ko su yi lacca daya ko wani majalisi a kan yan bidi'ar shi'anci ko sufanci, sun yi biyar a kan Ahlussunnah da malamansu. Tir da wannan aiki.”

Na ce:

Wannan magana tasa tana kara fitowa da rashin saninsa ga Tafarkin Magabata Na Kwarai, ko kuma son zuciyarsa wanda zai sa shi jahiltar da kansa abin da ya tabbata da dalilan Shari’ah, ina nufin hukunci ga wanda ya cancanta a hukunta shi ta hanyar danganta shi zuwa ga ayyukansa ko kungiyarsa, Misali: Dan Kungiyar Ikhwan al-Muslimeen ka ce masa Ba’ikhwaniye, Dan Kungiyar Izala ka ce masa Dan Izala da sauransu.

Kari a kan haka: Wannan shi ma kangarewa malaman Salafiyyah ne da jifansu da munin manhaji, domin su ma sun aikata haka, kuma sun goyi bayan masu aikata haka da ilmi da adalci, misali: Idan ya tabbata cewa wani yana da alaka da wani aiki ko fahimta babu laifi a danganta shi da shi.

Kuma menene laifi a cikin danganta mutum da aikinsa ko kungiyarsa wacce ya kirkira da kansa?!

Abin da yake kara tabbatar da zaluncinsa ga malaman Salafiyyah shi ne: Batun jifansu da rashin yawaita raddi ga Yan Shi’ah da Sufaye, domin zahiri yana karyata haka, kuma misalai a kan wannan batu suna da yawa, Sheikh Rabee yana da ‘Majmuu’ah’ [Collection] na raddi ga Shi’ah, haka yana da wallafe-wallafe a kan Sufaye, musamman wadanda ya yi yana martani gare su a kan kage ga Da’awar Salafiyyah wacce Sheikh Muhammad Bn Abdulwahab [R.A] ya jaddada, sa’annan yana da martanoni kala-kala ga Shi’ah da daidaikun Sufaye, kamar: al-Kautharee da al-Bootee da makamantansu.

Yana daga cikin abin da ambatonsa zai amfanar: Lallai raddi ga Yan bidi’ah ba shi ne abin da yake maida mai yinsa ma’abocin Sunnah ba, bal a tarihi an iske cewa a cikin mafi girman wadanda suka yi martani ga Yan Bidi’ah akwai Yan Bidi’ah da kansu, misali: Daga cikin wadanda suka tsaya a makogoron Mu’utazilawa akwai Asha’irah, kuma tabbas sun yi kaca-kaca da akidunsu da manhajinsu, amma wannan bai maida su ma’abota Sunnah ba, saboda haka Idan wani Bakhawarije wanda ya rabu da Sunnah ya fantsama fagen martani ga Shi’ah wannan ba ya maida shi ma’abocin Sunnah, misali: Adnan ‘Ar’oor wanda ya zama daya a cikin mabarnatan da suka kai Musulman Syria cikin tashin hankali da halaka, ko shakka babu, ba malami ko dalibin da bai san kwazonsa wajen bankade halin Shi’ah ba, ta fuskar tattaunawa da rubuce-rubuce, amma wannan bai tseratar da shi daga bidi’o’in da suke tare da shi jingim ba!
Ka sani! Ma’abocin Sunnah na hakika ba abin da yake burge shi a jikin kowa duk ilminsa da littattafansa matukar bai kasance a kan kyakkyawar akida da ingantaccen manhaji ba, misali: Ibn Arabee da al-Zamakhsharee watakila ka ce su ma’abota manyan bidi’o’I ne, ko ma ka ce an kafirta Ibn Arabee, to amma idan ka’idarka za a bi, shi ma zai iya tsira.

A takaice: Galibin wadanda kake nufi da malamai ko ma’abota Sunnah, lallai yan bidi’ah ne da son zuciya, kuma jera sunayensu a tsakanin malaman sunnah yaudara ce.

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Haka nan daga cikin munin wannan Manhaji cin kansu da kansu da ma'abota wannan manhaji suke wa junansu, yau su kore wancan, gobe su kore wancan, aikin kenan kullum ba su da aiki sai jarrahawa da fitarwa.”

Na ce:

Wannan yana nuna cewa dole a daidaita sahu a kan tafarki daya, domin Salafiyyah ba Ikhwaniyyah ba ce ma’abociyar rufa-rufa da hadin baki a kan bisine gaskiya da tafiya a kan karya.

Kuma zan so ka kawo mutum daya da malamai suka yi magana a kansa ba tare da ilmi da hikima ba, ko adalci da insafi?!
Matukar wani ya aikata abin da ya cancanci a kafirta shi, ba kadai tsoratarwa ko bidi’antawa ba, za a kafirta shi matukar sharudan kafita shi sun cika, dalilan hana hakan su kawu.

Da wannan takaitaccen bayani zai cewa lallai tafarkinku shi ya fi cancanta a yi tir das hi, saboda yana goyon bayan ha’inci a cikin Addinin Allah.

Dr. Muhammad Rabi’u y ace:

“Ya ishe wannan manhaji muni a ce wai su sheikh Abu Ishaq Al-huwainiy da sheikh Aliyyu Al-halabiy, da sheikh Mustapha Al-adawiy, da sheikh Mashhur Hasan Salman, da Sheikh Ja'afar Mahmud, da Dr Sani R/lemo da Dr Jalo jalingo da Dr Bashir Aliyu Umar da Sheikh Abdulwahab da sauran malaman sunnah da yawa duk yan ikhwan ne, wani lokaci ma su ce musu Khawarijawa, don kawai sun saba musu a kan wanan mummunan manhaji da suka kirkiro.”

Na ce:

Bayani a kan wannan shubuha zai kasance kamar haka:

Maganganun malamai a kan su Ali al-Halabi, da Mustafaa al-Adawee da Mashhuur Hassan da Sauransu a fili suke, kuma bana tsammanin akwai mai tsoron Allah da adalci da zai ce bisa jahilci aka yi magana a kansu da bidi’antarwa ko tsoratarwa. Bayani a kan biyu a cikinsu a takaice:

1. Ali al-Halabee bayan rasuwar malaminsa al-Albaanee [R.A] wasu mabarnatan yan bidi’ah sun rabe shi, har suka lalata shi, daga nan ya fara cin dunduniyar malaminsa a kan wasu fatawowi da matsayinsa dangane wasu mutane, kamar fatawarsa a kan ‘Bidi’ar Muwazanaat’ da Matsayinsa a kan Abdurrahman Abdulkhaliq, da malamai suka fahimci yadda ya dosa, sai suka fara taka masa burki, domin su ma dadliban malamin nasa ne, bal sun zama malamai tare da malaminsa, alhali shi yana dalibi, daga wannan lokaci ya fara fuskantar da harcensa a kansu, a karshe bayan dogon zamani da aka dauka ana yi wa juna martani har ya fito ya ce ya barranta daga tafarki na kaushi da zurfafawa, yana nufin tafarkinsa dana malaminsa, alhali babu wani dalili na shari’ah da ya tabbatar da cewa tafarkin nasu na kaushi ne, bal shi ne ya lalace, daga nan malamai suka  tabbatar da bidi’ancinsa, musamman bayan ya fara wallafe-wallafe wadanda suke barnata tafarkin magabata na kwarai da juya alakarsa zuwa ga sabanin abin da yake kai na asali.

A karkashin wancan bataccen tafarki ne da ya dauko na bada kowane mabarnaci kariya, musamman wanda Sheikh Rabee [H.A] ya bayyana barnarsa ko tabbatar da bidi’ancinsa, tunda shi ne  mafi girman makiyinsa a rayuwarsa, sai ya bude wani shafi na ‘yanar gizo’ [Internet] wanda ya kira da ‘Zaurukan dukkan Salafawa’ [منتديات كل السلفيين] a nan ya tattara dukkan karkatattu gabarin tafarkin magabata na kwarai, hakan ya sa malamai suka yi tsoratarwa gabarinsa.

Na ga kamar Dr. Muhammad Rabi’u  ya amince da Salafiyyah ta Sheikh Salih al-Suhaimee [H. A], to shi ma Ali Halabee dan bidi’ah ne a wajensa, yanzu idan na yi riko da hukuncinsa a kan Ali al-halabee na yi daidai?!

Har ilau yana cikin malaman da suka tsoratar gabarin wancar mahada da al-Halabee ya yi wa duk wani kangararre ga tafarkin malamai, kama gada kan Ikhwaniyawa, da Tablighawa da Khawarijawa da sauransu, bal abin da ya fada a kansu shi ne: “Wadannan mutane yan fashi ne” wato fashin ingantacciyar akidar mutane da kyakkyawan tafarkinsu.
Mostafaa al-Adawee daya ne daga cikin daliban Sheikh Muqbil [R.A], amma bai wuce shekaru hudu a wajensa ba ya fahimci karkacewarsa da yadda yake hada hatsaniya da jayayya a tsakanin dalibai, bayan nasiha gare shi sai ya kore shi, kuma ya sa aka cire sunansa a jerin dalibansa, bayan ya dawo Misra ya ci gaba da gabata kan batun karantarwa ba tare da ya tuntubi tafarkinsa ya inganta shi ba, shi ya sa barnarsa, musamman a bangaren manhajin Salafiyyah ta yi yawa, kuma adawarsa gare su ta yawaita, tunda shahararren malamin salafiyyah ya kore shi daga majalisinsa saboda bacin tafarkinsa, amma ba son zuciya ba, domin Sheikh ‘Uthaimeen [R.A] taba cewa dangane da malamin da ya kore shi: “Lallai ina akidance cewa Sheikh Muqbil yana daya a cikin jagororin addini”.

2. Mostafaa al-Adawee yana ganin halaccin zanga-zanga da fito-na-fito ga azzalumin shugaba, ko wannan batun kadai ya kai ya zama dan bidi’ah na gaske, domin batu ne yake kare shi a tsawon shekaru, kuma har yanzu babu wata magana daga gare shi ta dawowa daga wannan tafarki na Khawarijawa.

Bayani a kan Batun Ikhwaniyanci da ka ce ana jingina wa wasu malamai a Nigeria zai kasance kamar haka:

1. Ban taba jin wanda ya ya danganta Sheikh Ja’afar  [R.A] da Ikhwaniyanci ba sai yau a wajenka, abin na sani shi ne: Ana danganta shi da Suruuriyyah, ita kuma wani bangare ne na Ikhwaniyawa, saidai sun  bambanta da su a wani bangare, kamar bayyana da Sunnah da fada da bidi’ah tare da tafiya a kan tafarki na caji da zafin kai, wadannan abubuwa kuma kama daga kan jingina shi da Suruuriyyah ko tafiyarsa a kan manhajinsu lallai wannan abu ne da ba wanda ya isa ya karyata shi sai wanda ya jahilci tafarkin Suruuriyyah ko dan son zuciya, to amma shin Dan Bidi’ah ne? Har yanzu ba wanda ya yi masa hukunci da haka a cikin Malaman Salafiyyah da na sani a Nigeria, ko Dr. Kabiru Lawal da aka jingina masa haka tabbas zalunci ne gare shi, domin ya tabbatar da wasu abubuwa ne wanda yake kai wadanda suka saba wa Sunnah, amma bai yi hukunci na bai daya gare shi da bidi’ah ba, idan ma ya yi, abin da ya kamata shi ne danganta shi gare shi, kafin nan da bibiyar dalilai da sabuban da suka sa ya yi masa hukunci da haka, sai a tabbatar da hukuncinsa ko a kore bayan an yi la’akari da su!

A dauka cewa Suruuree da ya ce dangane da shi yana nufin Ikhwanee, to ai dama Ikhwaniyawa sune suka haife Suruuriyyah, kuma abin da ya bambanta su dan kadan ne.

2. Batun Ikhwaniyancin Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo wannan muma zargi muke yi, saboda irin manhajinsu da yake tafiya a kansa, sa’annan da bata Malaman Salafiyyah da yake yi a boye da kokarinsa na hana daliban ilmi zuwa wajen karatun Malaman Salafiyyah a kasashen waje, kamar Misra da Saudi Arabia. A kan wannan batu ni shaida ne, domin daya a cikin wadanda suka tarbo shi Airport a lokacin da ya zo Egypt da bakinsa yake fama din cewa malaminsu Dr. Sani ya hana su zuwa wajen Sheikh Raslan [H.A], saboda ba a kan tafarki nagari yake ba koda yana da ilmi da larabci. Dalilinsa bai wuce maganar da Sheikh Raslan din yake yi a kan Ikhwaniyawa ba.

Tare da wancan al’amari duk muna cikin zargi ne na kasancewarsa boyayyen Ba’ikhwaniye, ba mu fara kokarin tabbatar da wannan ala’amari ba, sai bayan kullace-kullacen dakile da’awar salafiyyah da bata ta da kuka yi a cikin ‘Dandalin Whatsapp’ na Dr. Mansur Sokoto mai suna ‘Mu’assasatu Ahl Baiti Was Sahaabah’ [مؤسسة أهل البيت والصحابة] a nan ne Dr. Mansur Sokoto ya ce: bai san malaman da suke bayyana Ikhwaniyancinsu a Nigeria kai tsaye ba kamar Dr. sani, da Dr. Jalo Jalingo, da Dr. Bashir ko Engr. Bashir Aliyu, na kasa tantacewa. Kuma ko shakka babu gaskiya ya fada, domin muna ganin irin rawar da suke takawa na ruwantar da manhajin salafiyyah, saboda a cikinsu daga wanda zai ce babu laifi a yi zanga-zangar lumana, sai wanda zai ce ana zaluntar Ikhwaniyawa a Misra tare da cewa ya san galibin hare-haren bama-bamai da ake kaiwa sune da alhakin haka, ka ga idan an kama su domin zaunar da kasa lafiya da yi musu hukuncin da ya dace ina zalunci a cikin haka?!

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Shawarata ga yan uwana daliban ilimi ita ce, su watsar da wannan manhaji, su rungumi karatu da karanta littafan malamai na hakika, kada su shagaltar da kawunansu wajen soke-soke da bidi'antar da malaman da tun kafin a haife su suke yi wa sunnah hidima, da kiran mutane zuwa gare ta, su sani ba wani dan adam baya kuskure, sai wanda Allah ya kare, wato Annabawa da Manzanni, kuma kuskuren malamai ba abin bibiya ba ne da shelantawa ga mutane da yanke musu hukunci ba tare da wani uzuri ba. Malamai magada Annabawa, namansu kuma guba gare shi, duk wanda ya ci, sai ya ji a jikinsa, Allah kuma baya barin wanda ya ci namansu sai ya tozarta shi.”

Na ce:

A karshe: Ina ga shawarar da ya kamata ka bada daliban ilmi a kan wannan batu ba haka ya kamata ta kasance ba, domin zai sake maimaita irin kuskuren da wadanda suka gabace ne suka yi na kokarin hana wasu malamai da dalibansu karanta littattafan Salafawa, kamar yadda ka yi a yanzu, a karshe kuma suka ci gaba da karatunsu da karantarwarsu, tunda su ba ‘Yan Benci ba ne, gaskiya suke nema, kuma Allah [S.W.T] ya datar da su da ita tun daga shekaru ashirin da suka wuce a kalla zuwa yanzu ba su girgiza ba, saboda haka abin da ya kamata ka bada daliban ilmi shawara a kansa shi ne:

1. Su yi kokarin bincike da karatu a kan kowane irin sabani da suka ga ana yi, sa’annan su bi yadda gaskiya take, domin gaskiya tana sama da kowa.

2. Kar su damu da girman malami ko shekarunsa, idan ya saba wa gaskiya su sake sabawar tasa su kama gaskiya, saboda ba a sanin gaskiya da mutane, mutane ne ake saninsu da gaskiya.

3. Nusantar da su sanin cewa rotse na malamai ne ba dalibai ba, su bari idan sun kai wannan matakin malunta sai su yi, domin a yanzu ma suna yi ga malaman salafiyyah, kuma ba wanda yake hana su, bal ma gani suka yi ana yi sai suka yi, amma ba su san a kan wane dalili ba!

4. Umartarsu da daukar maganganun malamai, kamar Ibn Baaz, da al-Albaanee, da ‘Uthaimeen, da Muqbil, an-Najmee da sauransu a kan mabarnata da son zuciya na wannan zamani. Na san koda maganganun wadannan suke dauka a kan wannan batu, tabbas wata rana sai sun fahimci ha’incin da aka jima ana yi musu a kansa, kuma za su fahimci wasu batutuwa da suka danganci mazaje a fagen da’awah, da dalilan da ya sa ake kokarin raba tsakaninsu da malamai.

 5. Karantar da su cewa malamin da ya yi kuskure aka gyara masa ko aka yi masa nasiha ya kangare ba shi da wani uzuri da ya rage a gare shi, kuma kuskurensa ya tashi zuwa ga karkata, amma za a iya tsumayinsa na wasu lokuta ko Allah [S.W.T] zai sa ya dawo daga kanta, idan ya kangare sai a bayyana hukuncin da ya cancance shi.

6. Sanar da su cewa alherin da wani malami ya aikata sakamakonsa yana wajen Allah [S.W.T], kuma ana ganinsa da shi, ana fatan ya samu lada a kansa, amma wannan ba ya hana a gyara kuskurensa idan ya aikata kuskure ana mai kare masa mutuncinsa, ko a bayyana batarsa ana mai nisantarsa, saboda karkata takan zama dabi’ah, ita kuma dabi’ah tana kaura daga mutum zuwa mutum.

Shi ya sa wani Dan uwa yake bani labarin cewa wanda Dr. Muhammad Rabi’u ya yi rubutu domin kare shi a ‘sakin layi’ [Paragraph] na farko wato Ba’ikhwaniye Nura Musa, ya yaudari wasu matasa a Kaduna wai zai karantar da su ‘al-Kutub  as-Sittah’ da ‘Alfiyah’ ta Ibn Maalik, da suka je karatun sai ya ce za su yi shimfida da ‘Qadr an-Nadaa’, kafin su yi wata daya ya jefa musu kiyayya da Salafiyyah, har ya zamanto ba sa son a danganta su da ita, wannan shi ne hatsarin mika dalibai ga mabarnata kamarsa domin karatu.

7. Fada musu cewa duk wanda ya raina malaman sunnah na hakika, sai Allah [S.W.T] ya bayyana halinsa a hanun wadanda yake ganin ba su taka kara ba balle su karya, kuma a tunatar da su Sunnah ta rayuwa: Kamar yadda ka yi haka za a yi maka, musamman idan ba ka yi da kyau ba, lallai ba za ka ki ganin abin da hanunka ya shuka ba! Watakila ma Allah [S. W. T] ne ya fara tozarta masu cin naman malamai tun daga yanzu, amma mu je zuwa, kowa matsayinsa zai bayyana imma da harcensa ko alkalaminsa.

Dr. Muhammad Rabi’u ya ce:

“Allah ya tabbatar da mu a kan gaskiya da manhajin magabata.”

Na ce:

Wannan addu’a ce maras madadi, musamman a cikin hali irin wannan, ba abin da ya cancanta ya biyo bayanta face fadin:

“Amin!”

©Ibrahim Lawal Soro
11. 01. 2018 C. E

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!