MADAKHILAH?!
*SO DA DAMA MAI DA'AWAR NEMAN GASKIYA DA ADALCI YANA AUKAWA CIKIN TAFARKIN AZZALUMAI BA TARE DA YA SANI BA!*
So tari zakaga mutane masu son addini da adalci ga bayin Allah, sai suyi rashin dace sai su auka tarkon mabarnata fasikai basu sani ba, yana da kyau ya kai mai amfani da Facebook, ko mai neman gaskiya, ya kasance da gaske gaskiyar kake nema, ba yawan mabiya ko masu yin muwafaka da ra'ayin ka kake nema ba, ya kasance gaskiya ce abar neman ka, kuma da gaske, ka saki ta'assubanci, domin duk mai son ya zama "Salafi" (ma'abocin Sunnah na gaskiya) to sai ya yakice rigar ta'assubanci ya wurga wa shedan kayan sa, domin ta'assubanci ba tufafin mumini bane, kuma wuyan rigar gaskiya da adalci tayi kunci ga fasikai masu bada kariya ga 'yan Bid'ah da son zuciya.
Idan ka gane wannan, zaka ga marubuta da yawa masu da'awar su ma'abota Sunnah ne, wani ma zakaji yana cewa shi mabiyin Tafarkin Salaf ne, zaka dinga cin karo da maganganun Ibnu Taimiyyah a rubutunsa, in ma dai yayi tawilin maganganun yadda zai karya alakar ababen da rubutu yake isarwa daga asalin marubuci na farko, ko ya kawo siyakin maganar amma sai ya bude ta ya kara mata fadi, ya sanya wahamin sa domin ya kange masu neman gaskiya daga riskar asalin gaskiyar, da makamanta irin wa'yannan ababe da suka shahara daga ire-iren wa'yannan mutane, wa'yanda basu san inda suka sa kai ba.
Zakaga suna jifan Shaikh Rabee'u Bin Hādiy Al- Madkhaliy, suna ce dashi mai zafafawa ne a Bid'antarwa, mai guluwwi a babin jarhi da ta'adili, da shauran kalamai na kore mutane daga gareshi.
To dan uwa mai neman gaskiya ga tambayoyi daga masoyin ka, amma ba sai ka bani amsa ba, kayi wa'yannan nazarorin kamar haka kuma ka baiwa kanka amsa:
(1) Shin ka taba ganin Shaikh Rabee'u Al- Madkhaliy?
(2) Shin ka taba karanta littafan sa, ka taba sauraron sautin sa, kafin cin karo da wannan mai da'awar adalcin?
(3) Shin kana fahimtar harshen larabci, ka iya karantawa in ka saurara kana ganewa, ko kai ba dalibin ilimi bane, kai gama-gari ne?
(4) Shin menene Malamai suke fada akan Shaikh Rabee'u Al- Madkhaliy, ina nufin Malaman Sunnah, irin su Bin Baz, Albani, Uthaymeen.. Idan su sun riga mu gidan gaskiya, to menene su Shaikh Sāleh Al- Fauzān suke fada a game dashi? Menene Shaikh Sāleh Al- Luhaydān yake fade game dashi? Menene Shaikh Sulaimān Al- Ruhailee yake fade game dashi? Shin daya daga cikin su ya jefe shi da tsanantawa a Bid'antar wa ko guluwwi a babin jarhi da ta'adili?? Ina nufin magana karara wacce bata daukar tawili, domin ire-iren fallasassun nan masu da'awar adalci suna zaluntar malamai, ta hanyar daukar sautin su ko rubutun su su dora shi akan ra'ayin su, sannan su nemi hukuncin da suke tunanin ya dace su dora wa wani malami kuma suyi ilzamin wannan magana ga Malamin ko suce ga hukuncin malam ko ra'ayin Malam wane ga Malamin!.
(5) Shin ka taba cewa su wanene Shaikh Rabee'u Al- Madkhaliy ya bid'antar dasu, don haka mai da'awar adalci ya lissafo maka sunayen su?
(6) Shin Shaikh Rabee'u ya Bid'antar da su Al- Imāmu Mālik ne, ko su Abu Hanēfah, ko su Shāfi'iy, ko Ahmad Bin Hanbal, ko Al- Imām Al- Nawawiy, ko Ibnu Hajar, ko Ibnu Rajab, ko Ibnu Taimiyyah, ko Ibnu Al- Qayyim, ko Ibnu Abdilwahhāb, ko Shaikh Bin Bāz, ko Shaikh Muhammad Shākir, ko Shaikh Hammād Al- Ansāriy, ko Shaikh Safiyyul Rahmān Al- Mubārakphuriy, ko Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albani, ko Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen, ko Shaikh Sāleh Al- Fauzān, ko Shaikh Abdulmuhsin Al- ‘Abbād, ko Shaikh Sāleh Aalu Al- Shaikh, ko Shaikh Sāleh Al- Luhaydān?
(7) Ka taba tambayar mai da'awar adalci don Allah ya lissafo maka Malaman da Shaikh Rabee'u Al- Madkhaliy ya Bid'antar?
(8) Ka san cewa Shaikh Rabee'u ya gabatar da Muhadarah Shaikh Bin Bāz yayi ta'aliki?
Karanta nassin muhadarar da nassin ta'alikin ta wannan link din dake kasa 👇🏼👇🏼👇🏼
https://www.ajurry.com/vb/showthread.php?t=335
Saurari sautin muhadarar daga wannan link din dake kasa 👇🏼👇🏼👇🏼
http://ar.alnahj.net/audio/1516
(9) Shin ka taba ganin wani littafi da wani Malami mai lafiyayyen manhaji yayi wa littafin suna da "kungiyar salafiyyun" kamar yadda akwai littafai na raddoji ga "Alqutubiyyah" "sururiyyah" "banna'iyyah" kyankyasar kungiyar Ikhwan, sannan kuma akwai adadi mai yawa na rududi ga kungiyar da sunan ta karara daga Malamai kamar su Bin Bāz, Albani, Uthaymeen, Fauzān, Luhaydān, Muqbil.. Kar a baka labari, ka saurare su da kunnuwan ka, ga link din su nan a kasa. 👇🏼👇🏼👇🏼
http://ar.alnahj.net/tree/254
Kasusuwa ne guda tamanin da shida (86), in ma baka fahimtar larabci kayi downloading Malamin ka ya fassara maka, duk akan raddi da tsoratarwa daga kungiyar Ikhwan, harma daga ayyanannu cikin malaman kungiyar, to meyasa baka taba ganin irin wannan rududi ga abinda mai da'awar adalci yake kira da "kungiyar salafiyyun" ba?
(10) Shin ka taba sauraron yabon da Malaman Sunnah su Shaikh Muhammad Bin Sāleh Al- Uthaymeen, Shaikh Abdul- Azeez Bin Bāz, Shaikh Sāleh Al- Fauzan, Shaikh Sāleh Al- Luhaydān, Shaikh Muhammad Nāsir Al- Albaniy duk sukayi ga Shaikh Rabee'u Al- Madkhaliy? Saurara daga wannan link din dake kasa 👇🏼👇🏼👇🏼
http://ar.alnahj.net/tree/493
(11) Shin Malamai sunyi ha'inci ne da suka kama sunan kungiyar Ikhwan sukayi ijma'i wurin raddi akan ta, tare da tsoratarwa daga gareta, amma suka ki yin haka ga wa'yanda mai da'awar adalci yake kira da "kungiyar salafiyyun" ko kuwa? Shin babu zargi ga Malaman akan haka? Ko dai a wajen Malaman babu wata "kungiyar salafiyyun" ne, shi yasa basuyi dirar mikiya ga wasu da sunan suna tsoratarwa daga "kungiyar salafiyyun" ba?
(12) Ko kuma Malaman suna jin tsoro ne, shi yasa sukayi ijma'i akan Bid'antar da Ikhwan, amma suka kasa fitowa karara suyi irin haka ga wa'yanda mai da'awar adaalci yake kira da "kungiyar salafiyyun" ko kuma dai shi ya fisu zurfin ilimi ne game da lamurran kungiyoyin zamani? Ko kuwa tsiya ce dama can babu wani abu mai suna "kungiyar salafiyyun" shi yasa Malaman da suke raye basu kira kowa da haka ba?!
(13) Anya kuwa abinda ake karantarwa a jami'ar da mai da'awar adalci yake karatu yana ma fahimtar sa kuwa? Domin fa a jami'ar ana tsoratarwa daga kungiyar Ikhwan, da rassan ta guda uku "Qutubiyyah" "Banna'iyyah" "Sururiyyah" (ko kace Al- Muntada)!
Ni kam na fahimci hanyar Malaman nan cike take da adalci, kuma mai da'awar adalci babban azzalumi ne, saboda yana sanya maganganun Malamai a inda ba mazaunin su ba, kuma yana tare hanya ga masu neman gaskiya, kuma yana kiyayya da maganganun malamai wa'yanda suka saba wa ra'ayoyin sa, musamman wa'yanda tawili baya shiga cikin su.
Ya Allah ka bi wa al- umma hakkin ta akan wannan azzalumi mai kange bayin Allah daga fahimtar gaskiya, kuma ka taimaki Salafawan gaskiya a duk inda suke.
أمين ثالث يعقوب
10 / 03 / 1440
18 / 11 / 2018
تعليقات
إرسال تعليق