KUNGIYOYIN TA'ADDANCI NA IKHWAN

 DUKKANIN MASU KIRA ZUWA GA SUNNAH A WANNAN ZAMANI SUN HADU KAN FALLASA KUNGIYAR TA'ADDANCI TA IKHWAN(¹)




Kasar musulunci ta Saudi Arabia (Allah ya kiyaye ta) ta tsayu haikan wajen bayyana halayen karkatattun kungiyoyi musamman ma #Kungiyar_Sururiyyah wacce take daya daga cikin 'ya'yan tagwaye uku(²) na kyankyasar kungiyar Ikhwan din (kasancewar ita Sururiyyah din ma'abotan ta sun fi yin kamanceceniya da Salafawa amma kuma ba Salafawa bane, 'yan bid'ah ne na yankan shakku).


Muna fatan Allah ya datar da Malaman da suke wannan bayani, kuma yasa wannan tsoratarwa ta amfanar da bayin Allah, muma a nan gida Nigeria da shauran yankunan musulmai Allah ya kiyaye garuruwan mu daga afkawa cikin fikirorin kungiyoyin ta'addanci masu suturce barnar su da sunan addini ko kishin Islama. 


MALAMAI SUN DAUKE MANA ALHAKIN BID'ANTAR DA KUNGIYAR IKHWAN! 


Wannan kungiya ta Ikhwan duk da bayyana wani sashe na Sunnah da dai-daikun su suke yi, amma hakan bai tseratar da ita daga fallasar Manyan Malamai ba, la'akari da ayyukan da jagororin kungiyar ke yi na karkata daga tafarkin Annabta. 


Daga cikin wa'yannan manyan Malaman akwai: 

(1) Shaikh Bin Baz

(2) Shaikh Al- Albaniy


An tambayi Shaikh Bin Baz Allah ya jikan sa a kan wannan kungiya ta Ikhwan, mai tambaya yake cewa:


أحسن الله إليك حديث النبي صلى الله عليه و سلم في افتراق الأمم وقوله "ستفترق أمتي على ثلاث وسبعين فرقة كلها في النار إلا واحدة " فهل جماعة التبليغ على ما عندهم من شركيات وبدع وجماعة الإخوان المسلمين على ما عندهم من تحزب وشق للعصا على ولاة الأمر ....هل هاتان الفرقتان تدخلان في الفرقة الناجية؟


Allah ya kyautata maka, shin hadisin nan na Annabi -Sallallāhu 'alayhi wasallam- game da rarrabuwar al- ummomi, da fadin sa: "al- ummah ta zata rarraba zuwa kashi saba'in da uku, dukkanin su suna wuta sai kwaya daya" to shin kungiyar Tableegh a kan abin dake tare dasu na shirkoki da bid'o'i, ita ma kungiyar Ikhwan a kan abin dake tare dasu na kungiyanci da tawaye daga biyayyar shuwagabanni.. Shin wa'yannan kungiyoyin suna shiga cikin kubutacciyar tawaga? 


الجواب: تدخل في الإثنين والسبعين، ومن خالف عقيدة أهل السنة والجماعة دخل في الإثنتين والسبعين، والمراد بقول النبي صلي الله عليه و سلم أمتي أي أمة الإجابة أي استجابوا لله وأظهروا اتباعهم له .


Amsa: suna shiga cikin saba'in da ukun nan, dama duk wanda ya saba ma akidar Salafawa yana shiga cikin kungiyoyi saba'in da biyu (halakakku), kuma manufar fadin Annabi -Sallallāhu 'alayhi wasallam- "al- ummah ta" yana nufin al- ummar da suka amsa kira, manufa sun amsa kiran Allah sun kuma bayyana biyayyar su gare shi. 


السائل : يعني هاتان الفرقتان من ضمن الإثنتين والسبعين؟

الجواب : نعم من الإثنتين والسبعين. 

(من شريط أحد دروس الملتقي في مدينة الطائف قبل وفاته بسنتين رحمه الله).


Mai tambaya yace:

Ana nufin wa'yannan kungiyoyin guda biyu (Tableegh da Ikhwan) suna shiga cikin kungiyoyi saba'in da biyu (halakakku)? 


Amsa: 

Eh, suna cikin saba'in da biyu (halakakku) .


[Zaka iya sauraron fatwar ta wannan link din:

https://youtu.be/XjJjRsuid_8 ]


BABBAR FA'IDA MANHAJIYYAH DAKE CIKIN FALLASAR SHAIKH BIN BAZ GA IKHWAN DA TABLEEGH:


Shaikh Bin Baz -Allah ya jikan sa- ya jarraha(fallasa) Tableegh a kan karkata biyu:

(1) shirka

(2) bid'ah

Ya kuma jarraha Ikhwan a kan karkata biyu:

(1) kungiyanci

(2) tawaye ga shuwagabanni

(Wa'yannan bid'o'in guda biyu na kungiyar Ikhwan, kai dama dukkan bid'o'in Ikhwan a yau suna nan jibge a cikin kungiyar Izala, amma a hakan ake samun wasu da rigar Malunta suna kiran ta wai kungiyar Sunnah!) 


Wannan yana kara bayyana mana cewa tafarkin Malamai Salafiyyun baya bukatar sai an kirgo karkata dubu kafin ayi ma wani mutum ko wata kungiya fallasa, a'a idan karkata kwaya daya ce tabbatacciya ana ma mutum hukunci da ita ace shi baya cikin ma'abota Sunnah, kuma yana cikin 'yan bid'ah wa'yanda sune saba'in da biyu hallakakku. 


Shaikh Al- Albaniy -Allah ya jikan sa- shima yana cewa:


خلافنا مع الإخوان المسلمين خلاف في الأصول لا في الفروع فقط! وليس صوابا أن يقال بأن الإخوان المسلمين من أهل السنة لأنهم يحاربون السنة |[ سلسلة الهدى والنور: 356 ]|


Sabnin mu da Al- Ikhwanu al- Muslimun sabani ne a cikin akida, ba kawai a cikin fiqhu bane, kuma ba dai-dai bane ace lallai Al- Ikhwanu Al- Muslimun suna cikin ma'abota Sunnah, domin ai suna yaki da Sunnah

[Silsilatu al- Huda wa- Al- Nur, kaset na dari uku da hamsin da shida]. 


ــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــ


(¹) Kungiyar Al- Ikhwanu Al- Muslimun ('yan uwa musulmi/'yan buraza) Hassan Al- Banna shine ya assasa kungiyar Ikhwan wanda shi ya mutu tun shekarar turawa na alif da dari tara da arba'in da tara (1949) miladiyya. 

Wannan kungiya ci gaba ne ga fikirorin khawarijawa, kuma tana da da tarbiyya ne ta Sufaye tare da tsare-tsare na kungiyanci na siyasa, a karon farko ta bayyana ne ba tare da fitowa a rigar Sunnah ba, wanda hakan ya sa mutane da yawa basu karbe ta ba, bal sunyi inkarin ta musamman a yankunan Saudiyyah, Bahrain, Qatar, Kuwait, Imarat, Oman.. Musamman saboda rashin lazimtar su ga Sunnah!


Sai dai ta samu karbuwa a tsakanin wayayyun 'yan Boko zalla haka kuma 'yan inna rududu daga cikin gama-garin mutane sun tasirantu da ita (ja ya fado ja ya dauka kenan!).


Daga cikin ababen da suka yaudari mutane dashi shine bayyanar da yaki da Yahudawa abokan adawa (Zionist), tare da rufe kofar martani ga 'yan Bid'ah da hujjar cewa ana son a dayanta sahun musulmai, saboda haka lokaci ba zai bayar da damar taba 'yan Bid'ah ba kuma hadafin dake gaban mu yafi girma a kan martani ga 'yan Bid'ah!!! Nan da nan sai wannan fikirar ta yadu cikin wani sashe na mutane ta cafke zukatan gama-garin su, nan take suka karkata zuwa gare su daya bayan daya, tare da wanzuwar wasu mutanen kuma da basu yarda sun amince musu ba, tare da kuma ana samun wani nau'i na tausayin su a wani sashe na mutane .


(²) Tagwaye uku kyankyasar kungiyar Ikhwan su ne: 


1- BANNA'IYYAH (nasabtuwa zuwa ga Hassan Al- Banna wanda ya kasance akidar sa akida ce ta sufaye, manhajin sa kuma Ikhwaniy, yana da wata yana da wani wasu baituka da ya rera a taron maulidi yana cewa:

هذا الحبيب مع الأحباب قد حضرا *** وسامح الكل فيما قد مضى وجرى

Manufa: Annabi -Sallallāhu 'alayhi wasallam- gashi nan ya halarci taron maulidi tare da masoyan sa, kuma ya yafe ma kowa dukkan wani zunubi da ya auku ya gabata. Malaman Sunnah sun yi bayanin halin sa kuma sun rushe shi, musulmai basu da bukatuwa zuwa ga 'yan takardun da ya wallafa, sai dai 'yan ta'adda ne suke kara samun caji a cikin su, da kuma masu bada kariya ga batattu na zaune cikin gida. 


2- QUTBIYYAH: Nasabtuwa zuwa ga Sayyid Qutb, shima jagora ne a tafiyar Ikhwan din, yana da tsananin son yin rubutu sai dai baya da tantancewa yana shiga cikin kowane irin littafi da aka rubuta da sunan addini ko da'awa, wanda hakan ya jashi zuwa dukufa gun karanta littafan 'yan shi'a da mu'tazilawa da 'yan faira ('yan darika) dama shauran tarkacen 'yan Bid'ah, wa'yanda ba'a zaton samun wani alheri daga gare su, a takaice babu wani irin bata wanda wannan mutumi bai bayyana shi a matsayin kyakyawan tafarki wanda Annabawa suka tafi a kan sa ba. Shi ma yana da maganganu na kafirci tsantsa kamar tafsirin sa ga Suratu al- Ikhlas inda ya bayyana akidar komai Allah ne, sannan yana da bakaken maganganu a kan zababbun bayin Allah, don shi har Annabawa basu kubuta daga sharrin sa ba, ya soki Annabi Musa ('alayhi al- Salam) ya soka daga Sahabban Manzon Allah (Sallallāhu 'alayhi wasallam) kamar Uthman bin 'Affan, da Abu Sufyan da Mu'awiya (Allah ya kara yarda gare su). 


Yana da maganganu da suke kafurta musulmi, bal duk wani mai akidar kafirta musulmi ba tare da hujjah ba a wannan zamani to a bayan Sayyid Qutb yake, na daga cikin maganganun sa:

"إن المسلمين اليوم لا يجاهدون، ذلك لأن المسلمين اليوم لا يوجدون".

Manufa: "lallai musulmai a wannan zamanin basa jahadi, kuma hakan ya faru ne don a yau babu musulmai".

A takaice; babu wani abun alheri da musulmai suke bukata ko tsammani daga mai sukar Annabawan Allah da Sahabbai, babu wani alheri da musulmai suke tsammani daga mai ikirarin babu su a cikin samuwa! Amma dai shi ma yana da masoyan sa da masu bashi kariya da masu yada littafan sa lungu da sako, duk mai son kawar da ta'addanci na kuduri da na aiki to ya nisanci wannan miskini, ya nisanci littafan sa, ya kuma tsoratar daga littafan sa, ya nuna illar halartar majalasai da ake tarjama su da karantar dasu! 


3- SURURIYYAH: Nasabtuwa zuwa ga Muhammad Surur bin Nayef Zainu al- 'Aabideen, asalin sa dan Syria ne, kuma daya daga cikin 'yan Ikhwan, ya koyi ilimi a Saudiyyah amma kuma daga baya ya kafirya gwamnatin ta ya kira malaman ta da "عبيد الطواغيت" manufa: "BAYIN DAGUTAI". bayan kafirta gwamnatin Saudiyyah sai ya koma Birtaniya a nan ya bude cibiyar sa ta "Al- Muntada al- Islamiy" , ya bayyana karara cewa shi ya fitar da wani sanfuri na Ikhwaniyyah wanda shi wannan sanfurin zai rinka bada kulawa da akidah, har ya kawo rudani a tsakanin matasa masu neman gaskiya, har ta yadu a tsakanin matasa cewa: "wane akidar sa Salafiyyah ce manhajin sa kuma ikhwaniy ne" da yake Malaman Salafiyyah ma'abota ilimi ne masu bada kariya ga tafarkin Allah caraf Shaikh Muhammad Nasiru al- Deen Al- Albaniy (Allah ya jikan sa) ya bayyana cewa:

يقول: يمكن الجمع بين السلفية والإخوانية؟! فهذا كالجمع بين الصواب والخطأ إن لم أقل بين الهدى والضلال.... 

Manufa: yana cewa: wai ana iya gwama tsakanin Salafiyyah da Ikhwaniyyah?! To ai wannan kamar gwama tsakanin dai-dai ne da kuskure, in ban ce tsakanin shiriya da bata ba.... (Ana iya sauraren shi tsaf ta wannan link din: https://youtu.be/HB7iykuvug4 )

Shi wannan Muhammad bin Surur din shugaban Muntada daga cikin bid'o'in sa yana kafirta mai manyan zunubai, yana kira zuwa ga tawaye ga shuwagabanni, kamar dai yadda halin 'yan Ikhwan yake, dukkanin su sun hadu a kan tawaye ga shuwagabanni, yana kuma raina sha'anin karantar da littafan 'Aqeedah, yana ganin cewa tauhidin Hakimiyyah daya ne daga cikin karkasuwar Tauhidi, kamar yadda Abu Ishāq Al- Huwainiy ma yana da wannan akidar (Ku tambayi Al- Qasim Hotoro matsayar sa a kan babban Malamin Sururiyya Abu Ishāq Al- Huwainiy) yana kuma sukar Manyan Malaman Saudiyyah irin su Shaikh Bin Baz, Shaikh Muhammad Aman Al- Jāmiy (asalin sa dan kasar Habasha ne), Shaikh Rabee' Bin Hādiy, dss. Yana sukar su cewa basu san siyasar zamani ba, yana da bid'o'i kala kala, yana da mabiya a kan tafarkin sa har a cikin Nigeria, sun hada da Malam Jafar -Allah ya jikan sa- (an gina masa masallacin Muntada a Kano wanda yana tare da gida, a nan ma aka harbe shi) kuma shi ma ya koyar da irin tafarkin Muhammad bin Surur din kamar yadda yake a bayyane, haka ma Mal. Auwal Albanin Zaria (Allah ya jikan sa), daga cikin mabiyan sa akwai Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo, Dr. Rabi'u Umar R/Lemo, Dr. Abdullahi Gadon Kaya, Alqasim Hotoro, Dr.  Mansur Sokoto, Dr. Mansur Isa Yelwa da shauran su. (Idan kana shakka kan Sururiyyancin wa'yanda muka ambata ka tambaye su me zasu ce game da Muhammad Surur, Muhammad Hassan, Abdul'azeez Al- Turaifiy, Salman 'Audah, Safar Al- Hawāliy, (musamman Dr. Sani domin dan sa Abdulrahman yana yawan kambama su, tambayi mahaifin menene matsayar sa a kan wa'yannan Malaman Sururiyyar kafin matsayin sa a kan dan nasa) . Ku tambayi wa'yanda ambaton su ya gabata game da Manhajin Al- Muwazanat, domin yana daga cikin manyan tafarkokin 'yan Sururiyyah


Muhammad bin Surur ya mutu a kasar Qatar a shekara ta dubu biyu da sha shida (2016) bayan jinyar ajali da yayi. 


Allah muke roko ya bamu tabbatuwa a kan tafarkin sa mikakke, ya kuma yi mana kariya daga tafarkokin karkata da ma'abotan su. 


أمين ثالث يعقوب 

18 / 02 / 1443

26 / 09 / 2021

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!