SAKAMAKON AYYUKAN DA MUTANE KE AIKATAWA! 


بسم الله الرحمن الرحيم، والصلاة والسلام على رسول الله، وعلى آله وصحبه ومن والاه. 

أما بعد.. 


Ya ku al-ummah musulmai, kuji tsoron Allah ku mayar da lamurran ku gare shi, wannan masifar da aka shiga mafi girman sababin ta shi ne juya ma tafarkin Allah baya, Allah ne ya saukar kuma shi ne zai dauke, amma in kuka ce shuwagabanni ne suka saukar ba zaku taba ganin dai-dai ba, domin kunyi wa Allah tarayya a cikin ayyukan sa.


A na samun masu shirka ga Allah kuma babu zalunci da ya kai shirka, ana samun masu bid'o'i kala-kala, ana samun masu sabo kala-kala, cin riba ba komai bane, kade-kade ba komai bane, yanzu ma ta kai ga cewa masu sabo sune suke cikin walwala, masu ayyukan da'a sune suke taka tsan tsan, lallai an zalunci kai, kuma sakamakon duk wa'yanda halin su ya zama haka. 

Allah madaukaki yana cewa:

(وكذلك نولي بعض الظامين بعضا بما كانوا يكسبوت) [الأنعام: 129].

"Kuma kamar haka ne muke dora sashen azzalumai a kan sashe sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa" .


Kenan duk al-ummar da ta zalunci kanta ta hanyar aikata shirka tsibbace-tsibbace (asirin soyayya da asirin raba aure da kisisina kala kala da yankan kai da binne binne wane iri ne ba'a yi a yankunan mu ba?) Cin riba, caca kala-kala (yaushe aka dena 9jabet? da shauran caca da shaye-shaye?) Abin da yafi wannan hadari yanzu ne ma ake samun tsinannu 'yan hakika masu zagin Allah da Manzon sa (Sallallāhu 'alayhi wasallam) da tauye darajar sa, duk da hakan kuke ganin cewa sai Allah ya barku haka nan ya kawo muku irin su Abubakar da Umar su mulke ku? Ina hankalin ku yake ne? Al- Hafidh Ibnu Katheer (Allah ya jikan sa) yana cewa:


"ومعنى الآية الكريمة : كما ولينا هؤلاء الخاسرين من الإنس تلك الطائفة التي أغوتهم من الجن ، كذلك نفعل بالظالمين ، نسلط بعضهم على بعض ، ونهلك بعضهم ببعض ، وننتقم من بعضهم ببعض ، جزاء على ظلمهم وبغيهم"

Ibnu Katheer -Allah ya jikan sa- yake cewa: "kuma ma'anar wannan aya mai karamci ita ce: kamar yadda muka dora wancan gungu na aljanu a kan wa'yancan asararun na daga cikin mutane da suka batar dasu, haka ne muke aikatawa ga azzalumai, muna dora sashen su a kan sashe, kuma muna halakar da sashen su da sashe, muna kama sashen su da sashe, sakamakon zaluncin su da rashin adalcin su".


Yana daga cikin sabubban fitintinu saba ma Manzanni da bijire ma shiriyar da suka zo da ita daga Allah ta tauhidi da Sunnah da barin shirka da bid'o'i da dukkan wani nau'i na sabon Allah, kamar yadda babban sababin zaman lafiya da saukin rayuwa da budewar kofofin arziki shine kadaita Allah da bauta da biyayya ga tafarkin Annabta. Allah madaukaki yana cewa :

(ولو أن أهل القرى آمنوا واتقوا لفتحنا عليهم بركات من السماء والأرض ولكن كذبوا فأخذناهم بما كانوا يكسبون) [الأعراف:96].

"Da ace mutan alkaryoyi sunyi imani sun tsoraci Allah da mun bude musu albarkar ruwan sama da arzikin kasa sai dai sun karyata sakon Allah sai muka kama su sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa) [Al- A'raaf:96].


Al- Hafidh Ibnu Katheer -Allah ya jikan sa- yake cewa:

"وقوله تعالى : ( ولو أن أهل القرى آمنوا واتقوا ) أي : آمنت قلوبهم بما جاءتهم به الرسل ، وصدقت به واتبعته ، واتقوا بفعل الطاعات وترك المحرمات ، ( لفتحنا عليهم بركات من السماء والأرض ) أي : قطر السماء ونبات الأرض . قال تعالى : ( ولكن كذبوا فأخذناهم بما كانوا يكسبون ) أي : ولكن كذبوا رسلهم ، فعاقبناهم بالهلاك على ما كسبوا من المآثم والمحارم"

"Kuma fadin sa madaukaki: (da ace mutan alkaryoyi sun yi imani kuma sun tsoraci Allah) manufa: zukatan su sunyi imani da abin da manzanni suka zo dashi, kuma suka gaskata shi suka bi shi, kuma suka tsoraci Allah ta hanyar aikata ayyukan da'a da barin haramtattun ababe, (da mun bude musu arziki daga sama da kasa) manufa: ruwa daga sama da tsirrai daga sama. Allah yace (sai dai sun karyata sai muka kama su sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa) manufa: sai dai sun karyata manzannin da aka aiko musu sai muka kama su ta hanyar halakarwa sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa na sabo da zakke ma haram". 


Kuma Allah madaukaki yana cewa:

(ظهر الفساد في البر والبحر بما كسبت أيدي الناس ليذيقهم بعض الذي عملوا لعلهم يرجعون) [الروم: 41].

"Fari (yankewar ruwan sama a lokacin damuna) da kashe-kashe sun bayyana a kauyuka da birane sakamakon abin da hannayen mutane suka aikata, don Allah ya dandana musu wani sashe daga ayyukan su ko sa koma ga addinin sa" [Al- Rum:41].

Al- Hafidh Ibnu Katheer -Allah ya jikan sa- yana cewa:

وقوله : ( ليذيقهم بعض الذي عملوا لعلهم يرجعون ) أي : يبتليهم بنقص الأموال والأنفس والثمرات ، اختبارا منه ، ومجازاة على صنيعهم ، ( لعلهم يرجعون ) أي : عن المعاصي.


Ibnu Katheer -Allah ya jikan sa- yake cewa: "kuma fadin Allah: (domin Allah ya dandana musu wani sashen laifukan da suka aikata ko sa koma) manufa: yana jarabtar su ta hanyar tauye dukiyoyi da rayuka da 'ya'yan ice, wannan jarabtawa ce daga gare shi, kuma sakamako ne a kan ayyukan su, (ko sa koma) manufa: daga barin ayyukan sabo.


Ya 'yan uwa, a koma ga Allah, a daina shirka ana hada Allah da wanin sa a bauta, a daina dukkan bid'o'i da dukkan nau'ukan sabon Allah, domin bala'o'i Allah ne yake saukar dasu domin jarabawa ga masu imani kuma sakamako ga masu saba masa. 

Shuwagabanni in sun zama azzalumai to ayyukan mutane ne domin Allah yana dora sashen azzalumai ne a kan sashe sakamakon ayyukan tir da suke aikata wa. 


Allah ya shiryar damu ya kubutar damu daga fitintinun boye da na sarari. 


أمين ثالث يعقوب 

20 / 10 / 1442

01 / 06 / 2021

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!