DAGA CIKIN MATSALOLIN HOTO:


A shar'ance: Manzon Allah (Sallallahu 'alayhi wasallam) yana cewa: 


"أشد الناس عذابا يوم القيامة المصورون، يقال لهم: أحيوا ما خلقتم"


"Lallai mafi shan azaba a cikin mutane ran kiyama sune masu yin hoto, za'a ce dasu ku sanya rai ga ababen da kuka halitta" (Al- Albani ya inganta shi a cikin Saheehu al- Jaami' 999).



A duniyance:  'yan kidnapping suna tara hotunan mutane suna bin su daya bayan daya suna tafiya dasu, musamman wa'yanda suke daukar hotunan su a wajajen cinikayyar su ko ofis din su ko wurin bukukuwan su, daga bisani su dora a kafafen sadarwa, ku sani ana muku ruwan comments kuma kuna burge ire-iren ku, amma kuma kuna bude ma kawunan ku kofofin matsaloli kala-kala na daya wanda shi ne yafi hatsari : shiga mafi matsananciyar azabar Allah, na biyu kuma wanda tun a duniya ne: akwai:


1) illar idanun masu hassada da 'ainu, akwai wani idan har yaga abu mai kyau ko yaga mutum mai kyau idan har ya yaba sai bala'i ya sauka ga wanda ya yaba din, wani ma yakan fadi ya mace, wani kuma yakan kamu da matsananciyar cuta. 


2) Masu kidnapping suna tara hotuna kamar yadda bayani ya gabata, wannan ma bala'i ne tun a duniya. 


3) Yaduwar zinace-zinace: ya kai mai kyau, ka sani a lokacin da kake sanya hotunan ka a social media kana sanya wasu matan cikin fitnah, yake mai kyau ki sani a lokacin da kike sanya hotunan ki a social media kina sanya wasu mazajen cikin fitnah, wanda hakan hanya ce mai kaiwa i zuwa ga sabon Allah, inma dai tare da mai sanya hotunan ta hanyar firar sirri a tsakani, ko kuma wasu na daban idan hakan ya ta'azzara. Akan samu wa'yanda suka zalunci kawunan su cikin wa'yanda shedan ya kada kararrawa suka bishi sau da kafa, suna bin 'yan mata har ma da matan aure, ko matan su biyo mazajen zuwa unguwanni ko garuruwa domin sada haramtacciyar zumunta wacce shedan ya zayyana musu, daga nan kuma sai a shiga aika-aika (aikin Allah wadai), wanda wannan yana rusa gidaje, yana raba aure, yana sabbaba cututtuka, da rashin kwanciyar hankali, yana sabbaba gaurai-gaurai da cakudedeniya tsakanin 'ya'yan halal da 'ya'yan Allah kyauta. Dukkan wannan asalin sa yana komawa zuwa ga yaduwar hotuna da kalaman so tsakanin maza da mata a social media. 


A takaice; jama'a koda babu wata cutarwa ta zahiri da ido yake gani kunnuwa suke sauraro, a sani cewa idan Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallama- yayi hani daga wani abu mu san hikimar haka ko kar mu san hikimar sa, illolin sa su bayyana ko basu bayyana ba, wajibi ne mu nisanci wannan abun domin babu alkhairi a cikin sa. 


Bamu da karfi bamu da dabara sai ga Allah! 


أمين ثالث يعقوب 

15 / 11 / 1442

25 / 06 / 2021

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!