
Salafawa Ba 'Yan Ta'adda Ba Ne! Karyar jingina wa Salafiyyah kashe Dr. Nadir al-'Umraanee (R. A) Su Dr. Mansur Sokoto da Dr. Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo suka koya wa almajiransu tun November 2016 a cikin wancan Group na Whatsapp mai suna 'Mu'assasatu AhlIl Hadeeth'. Saboda haka ba komai ba ne don wani mabarnaci daga cikin matasan da suke neman gindin zama a wajensu ya jefi Salafawa da shi a bainar jama'a, tare da cewa malamansa sun kudurce haka, amma sun kasa bayyanawa sai a kebe, sai shi saboda neman kusanci gare su, tare da cewa wannan jinginawa karya ce tsagoranta, dalilai mabambanta sun tabbatar da haka, kamar: 1. Ganin halaccin kashe wani musulmi ba tafarkin Salafiyyah ba ne, koda kuwa ya aikata abin da ya cancanta a kashe shi suna wakilta kisansa ga mahukunta. Hakika Salafawa ba sa daukar doka a hanunsu kamar yadda Khawarijawa, da Shi'ah, da Ikhwaniyawa da sauran kungiyoyin bidi'ah da zafin kai suke yi. 2. S...