HUKUNCIN YIMA SHUGABA NASIHA A KAN MINBARI TSAKANIN MA'ABOTA SUNNAH DA KHAWARIJAWA 'YAN BID'AH

 *AHLUS- SUNNAH WAL- JAMA'AH: SALAFAWAN GASKIYA, BASU YARDA DA FITO NA FITO KO KASHE SHUWAGABANNI BA, KO DA AZZALUMAI NE, HAKA KUMA BASU YARDA DA TAFARKIN QA'ADIYYAH ZAUNANNUN KHAWARIJAWA BA!:*



*Al- Imam Al- Nawawiy Allah ya jikan sa yana cewa:*


وأما الخروج عليهم وقتالهم فحرام بإجماع المسلمين وإن كانوا فسقة ظالمين، وقد تظاهرت الأحاديث بمعنى ما ذكرته، وأجمع أهل السنة أنه لا ينعزل السلطان بالفسق

[شرح مسلم ٢٢٩/١٢].


Amma fito na fito garesu da yakar su haramun ne da ijma'in musulmai, ko da sun kasance fasikai ne azzalumai, kuma tabbas hadisai sun bayyana ma'anar abinda na ambata shi, kuma Ahlus- Sunnah sunyi ijma'i akan cewa ba'a tunbuke shugaba saboda fasikan cin sa.

[Sharhin Muslim 12/229].


*Al- Imamu Ahmad Bin Hanbal Allah ya jikansa yana cewa:*


ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه لأحد من النَّاس، فمن فعل ذلك فهو مبتدع على غير السّنة والطريق.

[أصول السنة ص ٤٦].


Kuma bai halasta a yaki shugaba ba, haka kuma bai halasta ayi fito na fito garesa ba, ga wani daga cikin mutane, kuma duk wanda ya aikata hakan to shi dan Bid'ah ne, baya akan Sunnah da tafarki.

[Usulul- Sunnah 46].


*Al- Imām Al- Barbahariy yana cewa:*


ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه -وإن جار، وذلك لقول رسول الله -صلى الله عليه وسلم- لأبي ذر الغفاري: «اصبر وإن كان عبدًا حبشياً»، وقوله للأنصار: «اصبروا حتى تلقوني على الحوض». وليس من السنة قتال السلطان، فإن فيه فساد الدين والدنيا. 

[شرح السنة للبربهاري ص ٥٨].


Kuma bai halasta a yaki shugaba ba, haka kuma bai halasta ayi fito na fito garesa ba, ko da yayi zalunci ne, kuma dalili shine fadin Manzon Allah Sallallahu 'alayhi wasallama ga Abu Dharri Al- Ghifariy: «kayi hakuri, ko da bawa ne dan habasha», da fadin sa ga Ansar: «kuyi hakuri har ku hadu dani a tafki», kuma baya daga cikin Sunnah yakar shugaba; domin a cikin hakan akwai barna ga duniya da addini.

[Sharhus Sunnah 58].


*AN TAMBAYI SHAIKH SALIH AL- FAUZAN ALLAH YA KIYAYE SHI:*


السؤال : هل الخروج على الحاكم بالقول كالخروج بالسيف سواء بسواء ؟ وما الحكم بالخروج على الحاكم ؟ وهل من يخرج على الحاكم الآن كالخوارج في عصر الصحابة ؟


Tambaya: Shin fito na fito ga shuwagabanni da magana daya yake da fito na fito garesu da makami dai-dai wa dai-da yake? Sannan kuma menene hukuncin fito na fito ga shugaba? Kuma shin wanda yayi fito na fito ga shugaba a wannan lokaci shin dai-dai yake da khawarijawa a zamanin sahabbai?


الجواب : الخروج على الحاكم بالقول قد يكون أشد من الخروج بالسيف ، بل الخروج بالسيف مترتب على الخروج بالقول ، الخروج بالقول خطيرٌ جداً ، ولا يجوز للإنسان أن يحث الناس على الخروج على ولاة الأمور، ويبغَّض ولاة أمور المسلمين إلى الناس ، فإن هذا سبب في حمل السلاح فيما بعد والقتال ، فهو أشد من الخروج بالسيف ، لأنه يُفسد العقيدة ويُحرَّش بين الناس ويلقي العداوة بينهم وربما يسبب حمل السلاح . نعم . والخوارج في كل زمان هم خاصين بالخوارج في عصر الصحابة ، بل في كل زمان ، من سلك مسلك الخوارج فهو منهم في أي زمان ، ومن سلك مسلك أهل السنة فهو منهم في أي زمان . نعم .


Amsa: Shi fito na fito ga shugaba da kalma yakan iya zama yafi tsanani akan fito na fito garesa da makami, bari ma dai, ai shi fito na fito da makami yana kintsuwa ne bayan fito na fito da magana ya gabace shi, fito na fito da magana yana da hatsari sosai, kuma bai halasta ga mutum ya kwadaitar da mutane suyi fito na fito ga shuwagabannin su ba, kuma bai halasta ya sanya fushin mutane akan shuwagabannin su ba, domin hakan musabbabi ne ga daukar makami a nan gaba, da kuma kashe-kashe, saboda haka yafi tsanani akan fito na fito da makami, domin yana bata Aqidah, kuma yana haddasa cece kuce a tsakanin mutane, kuma yana jefa adawa a tsakanin mutane, kuma yakan ma sabbaba daukar makamai . Na'am . kuma su khawarijawa a kowane zamani sune suka kebanta da (dabi'un) khawarijawa na zamanin sahabbai, bari ma dai a cikin kowane zamani, duk wanda yabi matafiya ta khawarijawa to lallai yana cikin su (khawarijawan) a kowane zamani ne, haka kuma duk wanda yabi matafiya ta Ahlus- Sunnah to yana tare dasu (Ahlus- Sunnah) a kowane zamani ne.


Daga shafin Shaikh Salih Al- Fauzan:


https://www.alfawzan.af.org.sa/ar/node/13293


Kenan: matafiya ta Ahlus- Sunnah ita ce rashin caccakar shuwagabanni ko da fasikai ne, kuma ko da azzalumai ne, matafiya kuma ta khawarijawa ita ce caccakar su, ko da mai caccakar bai dauki makami ya jagoranci tawagar ta'addanci ba, a'a da ace irinsa basuyi irin wa'azin sa ba to da ba'a samu 'yan ta,'adda masu daukar makami ba, kenan wa'azin charge shine yake kyankyashe khawarijawa a kowanne zamani, a wannan lamari duk wanda ya tsaya akan asullai na Ahlus- Sunnah shine yake tare da Ahlus- Sunnah, duk kuma wanda matafiya ta Khawarij ta burge shi har yabi tafarkin nasu to shima bakhawarije ne akan haka.


*AN TAMBAYI SHAIKH BIN BAZ:*


هل من منهج السلف نقد الولاة من فوق المنابر؟ وما منهج السلف في نصح الولاة؟


Shin yana daga cikin Manhajin Salaf martani ga shuwagabanni a kan minbarori? Sannan kuma menene Manhajin Salaf wajen nasiha ga shuwagabanni?


فأجاب: ليس من منهج السلف التشهير بعيوب الولاة، وذكر ذلك على المنابر؛ لأن ذلك يفضي إلى الفوضى وعدم السمع والطاعة في المعروف، ويفضي إلى الخوض الذي يضر ولا ينفع، ولكن الطريقة المتبعة عند السلف: النصيحة فيما بينهم وبين السلطان، والكتابة إليه، أو الاتصال بالعلماء الذين يتصلون به حتى يوجه إلى الخير.

[مجموع فتاوى ابن باز ٢١١/٨].


Sai ya bada amsa yace: baya cikin manhajin Salaf yada aibobin shuwagabanni da ambaton haka akan mimbarori, domin hakan yana haifar da rikici, da rashin saurare da biyayya akan abu mai kyau, yana haifar da aukawa cikin abinda zai cutar kuma bazai amfanar ba.

Sai dai hanya wacce magabata suke bi ita ce: yin nasiha a tsakanin su da shugaban, da kuma rubuta wasika zuwa gareshi, ko samun malamai wa'yanda zasu isa gareshi har ya zamanto anyi masa fuskantarwa zuwa ga alheri.

[Majmu'ul Fatawa ta Ibnu Baz 8/211].


*SHAIKH BIN BAZ ALLAH YA JIKANSA YANA CEWA KUMA:*


ولما فتح الخوارج الجهال بابَ الشر في زمان عثمان -رضي الله عنه- وأنكروا على عثمان علنًا؛ عظمت الفتنة والقتال والفساد الذي لا يزال الناس في آثاره إلى اليوم، حتى حصلت الفتنة بين علي ومعاوية، وقُتل عثمان وعلي -رضي الله عنهما- بأسباب ذلك، وقتل جمعٌ كثير من الصحابة وغيرهم بأسباب الإنكار العلني، وذكر العيوب علنًا، حتى أبغض الكثيرون من الناس ولي أمرهم وقتلوه». 

[مجموع فتاوى ابن باز ٢١١/٨].


A yayin da Khawarijawa jahilai suka bude kofar sharri a zamanin Uthman Allah ya kara masa yarda, kuma sukayi wa Uthman inkari a bayyane; sai fitina da kashe-kashe da fasadi suka girmama, wanda mutane basu gushe suna cikin burbushin sa ba har zuwa yau, har sai da fitina ta auku a tsakanin Aliyu da Mu'awiyah, har aka kashe Uthman da Aliyu Allah ya kara yarda a garesu, duk ta sababin haka, kuma an kashe adadi mai yawa na sahabbai dama wasun su ta sababin inkari a fili, da kuma ambaton aibobi na shuwagabanni a bainar jama'a, har sai da aka fusatar da mutane akan shugaban su har suka kashe shi.

[Majmu'ul Fatawa ta Ibnu Baz 8/211].


*SU WANENE  "AL- QA'ADIYYAH" (ZAUNANNUN KHAWARIJAWA)?*


*Al- Hāfidh Ibnu Hajar Allah ya jikan sa yana cewa:*


والقعد: الخوارج، كانوا لا يرون الحرب، بل ينكرون على أمراء الجور حسب الطاقة ويدعون إلى رأيهم ويزينون مع ذلك الخروج ويحسنونه

[تهذيب التهذيب ١١٤/٨].


 

Khawarijawan zaune: sun kasance basa ganin su fita suyi yaki, sai dai suna inkari ga azzaluman shuwagabanni, gwargwadon ikon su, kuma suna kira zuwa ga ra'ayin su, kuma suna kawatawa tare da hakan: fito na fito kuma suna kyautata shi.

[Tahdheebu Al- Tahdheeb 8/114].


*Al- Hafidh Ibnu Hajar Allah ya jikan sa yana cewa:*


والقعدية: الذين يزينون الخروج على الأئمة، ولا يُباشرون ذلك. 

[هدي الساري ص ٨٣٠].


Zaunannun Khawarijawa: sune masu kawata fito na fito ga shuwagabanni, amma su basa fitowa don zartar da hakan.

[Hadyus Sari 830].


*Kuma ya sake cewa:*


«والقعدية: قوم من الخوارج كانوا يقولون بقولهم، ولا يرون الخروج بل يزينونه». 

[فتح الباري  ٤٣٢/١].


Kuma su zaunannun Khawarijawa: mutane ne daga cikin Khawarij, sun kasance suna furta irin maganganun su, amma basa ganin fito na fito din, amma su suke kawata shi!

[Fathul Bari 1/432].


*Yana ambaton maruwaitan da aka jefesu akan Aqidar su, sai Ibnu Hajar ya kawo kan Imran Bin Hittān sai yace:*


عمران بن حطان رمي برأي القعدية من الخوارج

[هدي الساري ٨٣٢].


Imran Bin Hittān: an jefe shi da ra'ayin Qa'adiyyah (zaunannu) daga cikin Khawarij.

[Hadyus Sari 832].


*Al- Imām Al- Suyutiy Allah ya jikan sa yana cewa:*


 عمران بن حطان من القعدية الذينَ يرون الخروج على الأئمَّة، ولا يباشرون ذلك. 

[تدريب الراوي ٣٩٠/١].


Imran Bin Hittan yana daga cikin zaunannu wa'yanda suke da ra'ayin fito na fito ga shuwagabanni, amma basa fitowa don zartar da hakan.

[Tadreeb Al- Rawi 1/390].


*Abdullahi Bin Ahmad Bin Hanbal yana cewa:*


سمعت أبا معمر يقول: كنا عند وكيع، فكان إِذا حَدَّثَ عن حَسَنِ بنِ صَالِحٍ، أَمسَكنَا أَيدينا، فَلَم نكتب، فقال: مَا لَكُم لاَ تَكتُبُوْنَ حَدِيْثَ حَسَنٍ؟!

فقال له أخي بيده هكذا، يعْني: أنه كان يرى السيف.

فسكت وكيع.

 [سير أعلام النبلاء ٣٦٤/٧].


Naji Abu Ma'mar yana cewa: mun kasance a gurin Wakee'u, sai ya kasance idan ya ambaci hadisi daga Hassan Bin Salih sai mu kame hannayen mu, bama rubutawa, sai yace: me ya sameku bakwa rubuta hadisin Hassan?

Sai dan uwa na ya kwatanta masa da hannun sa haka, yana nufin: ai yana da ra'ayin daukar makami.

Sai Wakee'u yayi shiru.

[Siyar 7/364].


*Al- Imam Al- Dhahabiy Allah ya jikan sa yana cewa:*


 كان يرى الحسن الخروج على أُمراء زمانه لظلمهم وجورهم، ولكن ما قاتل أَبدا. 

[سير أعلام النبلاء ٣٧١/٧].


Alhassan ya kasance yana da ra'ayin fito na fito ga sarakunan zamanin sa saboda zaluncin su da rashin adalcin su, sai dai shi bai taba yin yaki ba.

[Siyar 7/371].


Allah yasa masu wannan dabi'ah ta kawata kisan shuwagabanni su shiryu su daina, ko kuma Allah ya kawo karshen su ya mayar wa al'ummah mutanen kirki a makwafin su, so da dama mafi yawancin mutane suna daukar wannan ta'asa ita ma tana cikin Sunnah, sannan masu wannan danyen aikin sau da dama zakaji ana cewa dasu jarumai masu karfin fadin gaskiya, alhali kuwa halakar da al'ummah sukeyi da harsunan su masu tsayi, ya Allah duk wanda harshen sa zai ci gaba da haddasa halaka ga addinin musulmai cikin wa'yannan Qa'adiyyah din ya Allah ka datse harshen sa.


Dan uwanku a Musulunci da Sunnah:


أمين ثالث يعقوب


03 / 12 / 1439

14 / 08 / 2018

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!