AHLUS - SUNNAH WAL- JAMA'AH: SALAFAWAN GASKIYA, BASU YARDA DA FITO NA FITO KO KASHE SHUWAGABANNI BA, KO DA AZZALUMAI NE, HAKA KUMA BASU YARDA DA TAFARKIN QA'ADIYYAH ZAUNANNUN KHAWARIJAWA BA!: Al- Imam Al- Nawawiy Allah ya jikan sa yana cewa: وأما الخروج عليهم وقتالهم فحرام بإجماع المسلمين وإن كانوا فسقة ظالمين، وقد تظاهرت الأحاديث بمعنى ما ذكرته، وأجمع أهل السنة أنه لا ينعزل السلطان بالفسق [شرح مسلم ٢٢٩/١٢]. Amma fito na fito garesu da yakar su haramun ne da ijma'in musulmai, ko da sun kasance fasikai ne azzalumai, kuma tabbas hadisai sun bayyana ma'anar abinda na ambata shi, kuma Ahlus- Sunnah sunyi ijma'i akan cewa ba'a tunbuke shugaba saboda fasikan cin sa. [Sharhu Muslim 12/229]. Al- Imamu Ahmad Bin Hanbal Allah ya jikansa yana cewa: ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه لأحد من النَّاس، فمن فعل ذلك فهو مبتدع على غير السّنة والطريق. [أصول السنة ص ٤٦]. Kuma bai halasta a yaki shugaba ba, haka kuma bai halasta ayi fito na fito garesa ba, ga...
المشاركات
عرض المشاركات من يونيو, ٢٠١٩
- الحصول على الرابط
- X
- بريد إلكتروني
- التطبيقات الأخرى
SAURARON BID'AH HARAMUN NE KAMAR YADDA KIRA ZUWA GARETA YAKE HARAMUN! Al- ‘Allāmatu Bnu Al- Qayyim (Allah ya jikan sa) yana cewa: «وأما محرّمه: فهو النطق بكلّ ما يبغضه الله ورسوله ﷺ ، كالنطق بالبدع المخالفة لما بعث الله به رسوله ﷺ ، والدعاء إليها ، وتحسينها وتقويتها ، وكالقذف وسب المسلم ، وأذاه بكلّ قول . والكذب ، وشهادة الزور ، والقول على الله بلا علم . وهو أشدّها تحريما» [التفسير القيم ص ١١٦]. « Amma kuma haramtaccen sa (ma'ana: furuci na harshe) shine yin furuci da dukkan abinda Allah yake kin sa, Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ma yake kinsa , kamar furuci da Bid'ah wacce take sabanin abinda Allah ya aiko Manzon sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - dashi ne , da kira zuwa ga wannan Bid'ah , da kayata ta , da karfafar ta , haka kuma yin kazafi haramun ne haka zagin musulmi , da cutar dashi da kowacce irin magana . haka kuma karya haramun ce , da shaidar zur , da magana akan Allah ba tare da ilimi ba . kuma haramcin...
- الحصول على الرابط
- X
- بريد إلكتروني
- التطبيقات الأخرى
FA'IDOJI DAGA MUHADARAR SHAIKH SĀLEH AL- FAUZĀN 01 A cikin muhadara ta Shaikh Sāleh Al- Fauzān (Allah ya kiyaye shi) mai suna: ((موقف المسلم من الفتن والمظاهرات والثورات)) Ma'ana: ((Matsayar Musulmi a kan fitintinu da zanga-zanga da juyin juya hali)) Wacce aka buga ta a matsayin littafi kuma ya bayar da izinin buga ta a Ashirin da hudu ga watan Jumādal Ula shekara ta alif da dari hudu da talatin da biyu (24/05/1432) bayan hijira. Yayi wasu maganganu wa'yanda suka ja hankali na kamar haka: (1) "فهذه الفتن فيها خير؛ لأنها تميز بين الكفر والإيمان وتبين أهل النفاق والمخادعات وتكشف حقيقتهم فلا يغتر بهم بل يحذر منهم، هذه حكمة الله سبحانه وتعالى". ص ١١ Ma'ana: "wa'yannan fitintinun akwai alkhairi a cikin su; domin suna banbance tsakanin kafirci da imani, kuma suna bayyana ma'abota munafurci da yaudara kuma suna bankade hakikanin su, ta yadda ba za'a rudu da su ba, bal ma sai dai a tsoratar daga gare su, wannan hikimar Allah ce mai tsa...
- الحصول على الرابط
- X
- بريد إلكتروني
- التطبيقات الأخرى
ASSASA KUNGIYOYI BAYA CIKIN ABINDA ADDINI YA YARDA DASHI! Shaikh Sālih Al- Fauzan Allah ya kiyaye shi yana cewa: التفرق ليس من الدين ، لأن الدين أمرنا بالاجتماع وأن نكون جماعة واحدة وأمة واحدة على عقيدة التوحيد وعلى متابعة الرسول ﷺ، Rarrabuwa (cikin kungiyoyi) baya daga addini, domin addini ya umurcemu da haduwa, kuma mu kasance jama'ah guda daya, al'ummah guda daya, akan Aqidah ta Tauhidi, da biyayya ga Manzo Sallallāhu 'alayhi wasallam, Nace: anan Shaikh ya bayyana mana akan abinda ya zama wajibi Musulmi su hadu a karkashinsa, a karkashin Aqida ta Tauhidi, ba a karkashin kungiyoyi ba, masu kungiya sun fahimci kalmar jama'ah a baude, shiyasa karan kansu suke akan dimuwa da rikici, a sahun 'yan kungiya zaka taras har da wanda yake akan Aqidar mu'utazilanci kuma sun san da haka sama da shekaru goma sha, amma har yanzu suna kirga wannan bamu'tazile a cikin Ahlus Sunnah, Allah ya kiyaye mu daga son zuciya da bata. يقول تعالى {إنَّ هَذه أمَّتُكم...
- الحصول على الرابط
- X
- بريد إلكتروني
- التطبيقات الأخرى
?MECECE SALAFIYYAR GASKIYA بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، وعلى آله وصحبه ومن والاه.. وبعد: السلام عليكم ورحمة الله وبركاته. Abdulmalik Almaimooniy Allah ya jikansa yace: قال لي الإمام أحمد رحمه الله: «يا أبا الحسن، إياك أن تتكلم في مسألة ليس لك فيها إمام». انظر مناقب الإمام أحمد (١٧٨) ابن الجوزي. Yace: Al-Imamu Ahmad yace dani: «Ya kai baban Alhassan, kashedinka, karkayi magana akan wata mas'ala da baka da Jagora(magabaci) acikinta» . (A duba Manaqibul Imam Ahmad (178) wallafar Ibnu Al- Jawzi). *MUNA DA JAGORORI MAGABATA NA KWARAI AKAN DA'AWAR MU TA SALAFIYYAR GASKIYA!* Al-Imāmu Al-Auzā'iy Allah ya jikansa yana cewa: «اصبر نفسك على السنة، وقف حيث وقف القوم، وقل بما قالوا، وكفّ عما كفوا، واسلك سبيل سلفك الصالح فإنه يسعك ما وسعهم» (اللالكائي في شرح أصول الاعتقاد ١٥٤/١). Yace: «Ka hakurar da kanka akan (ruko da) Sunnah, kuma ka tsaya iyakar inda ma'abota Sunnah(wato Annabi da Sahabbai) suka tsaya, sannan ka furta dai-dai abinda suka furta, ...