
RADDI GA MASU JINGINA MA WASU MALAMAI TAWAYE (01) (1) Duk wanda yace maka Al- Imamu Malik yayi khuruji ga shugaba musulmi yayi ma Al- Imamu Malik kirkira . yana daga cikin dabi'un munharifai jingina tafarkin su da magabata domin samar masa da gindin zama. (2) Abin da aka ruwaito daga Al- Imamu Ahmad kuma shi ne hani daga tawaye, bal Malaman Fiqhu na Baghdad sun yi gangami domin su labarta masa kuma su nemi shawarar sa a kan cewa zasu yi tawaye ga Al- Wathiq, wanda yake azzalumin shugaba ne kuma yana da kafirar akidar cewa Al- Qur'ani halittar Allah ne, amma sai Al- Imamu Ahmad yace suyi hakuri, daga cikin abin da aka ruwaito daga gare shi a kan hani daga tawaye ma Al- Wathiq akwai fadin sa: "عليكم بالنكرة بقلوبكم، ولا تخلعوا يدا من طاعة، ولا تشقوا عصا المسلمين، ولا تسفكوا دماءكم ودماء المسلمين معكم، انظروا في عاقبة أمركم، واصبروا حتى يستريح بر أو يستراح من فاجر". Yace: ku rinka inkari da zukatan ku, amma karku fita daga yi masa biyayya, kuma karku fita da...