GASKIYA NE LITTAFAI DA KASUSUWAN SHAIKH RABEE‘U SUNA RABA KAN AL'UMMA?



📚 هل كتب و أشرطة العلامة ربيع تُفَرّق الأمة ؟

     🖍 قال الامام :
ربيع بن هادي المدخليّ
            -حفظه الله- 
Shaikh Rabee’u Bin Hādiy Almadkhaliy yace:

✍🏻 ( انّ ربيعاً يحارب الفرقة و التفرق و الحزبية و التحزب و يدعو من أول حياته في الدعوة الى أن يموت - ان شآء الله - الى الاعتصام بالكتاب و السنة و الى منهج السلف الصالح ,

Lallai Rabee‘u yana yakar rarrabuwa da kungiyanci, kuma yana kira tun daga farkon rayuwarsa acikin da'awa har zuwa mutuwarsa -In Allah ya yarda- kira yake zuwaga riko da Al-Qur’āni da Sunnah, sannan kuma zuwaga Manhaji na magabata na kwarai (Salafus Sāleh),

و هذه كتاباته و أشرطته بأيدي الناس و ما من كتابٍ الا و عرضه على علماء الاسلام في المملكة العربية السعودية و خارجها قبل أن ينشر . )

Sa'annan kuma ga littafansa da kasusuwansa nan a hannuwan mutane, kuma babu wani littafi face saida ya mikashi zuwaga Malaman Musulunci acikin kasar Saudiyyah da wajenta tun kafin ya yadashi!

📚 المجموع     📖  ( 10\276 )  📖

Mu dai munada wani kaso na littafan kuma muna ganin sa hannun Malaman Sunnah na gaskiya akan littafan nasa, da kuma yabo a gareshi da kuma karfafa masa gwuiwa wajen aikin da yakeyi na kariya ga sunnah, da kwankwatse Bid’ah da martani ga duk wani wanda ya saba mata, da kuma nasiha ga Musulmai wajen yada littafan -godiya ta tabbata ga Allah- .

Allah ka kiyaye dattijon arziki Malamin Salafiyyah Shaikh Rabee‘u Bin Hādiy Umayr Almadkhaliy, kasa ya cika da imani, ka sadamu da alkhairai da fa'idojinda suke jibge a cikin gudummawarsa ga Sunnah ta gaskiya koda mabarnata basa so.

تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

MADAKHILAH?!