
Wani yayi tambaya yace: "menene ma'anar Sururiyyah?" Sai nace dashi: Kungiya ce wacce ake nasabta ta ga Muhammad Surur Zainul Abideen, wanda asalin sa dan Syria ne, yayi zama a Saudiyyah shekaru 8, yayi karatu a Kwalejin ilimi a Buraidah, daga nan ya koma Brtaniya, ya koma Qatar wanda a nan ya mutu a shekarar 2016, wannan kungiya ta Sururiyyah an san ta ne da gauraye tsakanin Sunnah da Ikhwaniyan ci, sune suka kawo rudanin cewa Aqeedar Mutum Salafiyyah amma Manhajin sa Ikhwaniyyah, an san su da tawaye ga shuwagabanni Musulmai, tawaye na kalma da kuma karfafar Khawarijawa masu yakar gwamnatocin su, da yaba musu, da kuma tunzura matasa a kan zanga-zanga ma gwamnatocin su, da da'awar neman 'yanci ko kuma inkari ga azzalumai, sannan suna kambama Sayyid Qutb da tawagar sa 'yan ta'adda, basa kuma ganin cewa akwai gwamnatin Musulunci a wannan zamanin, suna kiran shuwagabanni Musulmai da الطواغيط (ma'ana: dagutai) sannan suna jifan Malaman Sunnah wa...