KUNGIYOYIN TA'ADDANCI NA IKHWAN
DUKKANIN MASU KIRA ZUWA GA SUNNAH A WANNAN ZAMANI SUN HADU KAN FALLASA KUNGIYAR TA'ADDANCI TA IKHWAN(¹) Kasar musulunci ta Saudi Arabia (Allah ya kiyaye ta) ta tsayu haikan wajen bayyana halayen karkatattun kungiyoyi musamman ma #Kungiyar_Sururiyyah wacce take daya daga cikin 'ya'yan tagwaye uku(²) na kyankyasar kungiyar Ikhwan din (kasancewar ita Sururiyyah din ma'abotan ta sun fi yin kamanceceniya da Salafawa amma kuma ba Salafawa bane, 'yan bid'ah ne na yankan shakku). Muna fatan Allah ya datar da Malaman da suke wannan bayani, kuma yasa wannan tsoratarwa ta amfanar da bayin Allah, muma a nan gida Nigeria da shauran yankunan musulmai Allah ya kiyaye garuruwan mu daga afkawa cikin fikirorin kungiyoyin ta'addanci masu suturce barnar su da sunan addini ko kishin Islama. MALAMAI SUN DAUKE MANA ALHAKIN BID'ANTAR DA KUNGIYAR IKHWAN! Wannan kungiya ta Ikhwan duk da bayyana wani sashe na Sunnah da dai-daikun su suke yi, amma hakan bai tseratar da ita daga ...