
DAGA CIKIN MATSALOLIN HOTO: A shar'ance: Manzon Allah (Sallallahu 'alayhi wasallam) yana cewa: "أشد الناس عذابا يوم القيامة المصورون، يقال لهم: أحيوا ما خلقتم" "Lallai mafi shan azaba a cikin mutane ran kiyama sune masu yin hoto, za'a ce dasu ku sanya rai ga ababen da kuka halitta" (Al- Albani ya inganta shi a cikin Saheehu al- Jaami' 999). A duniyance: 'yan kidnapping suna tara hotunan mutane suna bin su daya bayan daya suna tafiya dasu, musamman wa'yanda suke daukar hotunan su a wajajen cinikayyar su ko ofis din su ko wurin bukukuwan su, daga bisani su dora a kafafen sadarwa, ku sani ana muku ruwan comments kuma kuna burge ire-iren ku, amma kuma kuna bude ma kawunan ku kofofin matsaloli kala-kala na daya wanda shi ne yafi hatsari : shiga mafi matsananciyar azabar Allah, na biyu kuma wanda tun a duniya ne: akwai: 1) illar idanun masu hassada da 'ainu, akwai wani idan har yaga abu mai kyau ko yaga mutum mai kyau idan har ya yaba sai ba...