المشاركات

SALAFAWAN GASKIYA

 SU WANENE SALAFAWAN GASKIYA?  KO KA SAN MU WA'YANDA AKE CEMA SALAFAWA KUWA?  To a takaice mu din: Muna daukar akidar mu ne kai tsaye daga littafin Allah da ingantattun hadisan Manzon Allah sallallahu 'alayhi wasallam.  Tafarkin mu kuma shi ne tafarkin magabata na kwarai in kaso ka fada da larabci tafarkin Salaf ko kace Salafiyyah.  Muna gabatar da fahimtar Sahabban Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam- (wa'yanda sune jagororin Salaf a bayan Manzon Allah -Sallallahu 'alayhi wasallam wa radhiyallahu 'anhum-.  Muna gabatar da fahimtar su da maganganun su da maganganun mabiya tafarkin su da kyautatawa na daga jagororin musulunci, na jiya da na yau a kan fahimtocin wa'yanda ba su ba.  Muna gane tafarkin mutum dai-dai ne idan ya dace da tafarkin Sahabbai da mabiya tafarkin su da kyautatawa, kuma muna gane tafarkin mutum ba dai-dai bane idan ya saba ma ijma'in magabata din.  Muna martani ga dukkan wanda ya saba ma gaskiya na kusa damu ne ko na nesa...

KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA

صورة
 KOMAWA GA ALLAH SINADARIN SAMUN ZAMAN LAFIYA Allah madaukaki yana cewa: وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ اجْعَلْ هَٰذَا الْبَلَدَ آمِنًا وَاجْنُبْنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعْبُدَ الْأَصْنَامَ [ابراهيم : 35] Kuma ka tuna Ibrahim a lokacin da yake cewa : ya Ubangiji ka sanya wannan gari ya zama amintacce kuma ka nisantar dani da 'ya'ya na daga bautar gumaka (Ibrahim: 35). Annabi Ibrahim -Alaihi al- Salām- yayi addu'a ya roki Allah a kan cewa ya amintar da haramin Makkah kuma sannan ya nisantar da shi da 'ya'yan sa daga bautar gumaka, lallai duk wanda yake neman zaman lafiya da aminci na rayuwar duniya harma da ta lahira to dole ya roki Allah shi kadai, kenan ana rokon ne ga Allah shi kadai, ba'a rokon wanin Allah abin da babu mai iya bayarwa sai Allah, yin haka shirka ne fada ne da Allah din, kuma babu wanda ya isa yayi fada da Allah bare yai nasara, sannan bayan an samu zaman lafiyar kuma to babu abin da zai wanzar da wannan zaman lafiyar ya samu dorewa a samu facakar...

HUKUNCIN YIMA SHUGABA NASIHA A KAN MINBARI TSAKANIN MA'ABOTA SUNNAH DA KHAWARIJAWA 'YAN BID'AH

صورة
 *AHLUS- SUNNAH WAL- JAMA'AH: SALAFAWAN GASKIYA, BASU YARDA DA FITO NA FITO KO KASHE SHUWAGABANNI BA, KO DA AZZALUMAI NE, HAKA KUMA BASU YARDA DA TAFARKIN QA'ADIYYAH ZAUNANNUN KHAWARIJAWA BA!:* *Al- Imam Al- Nawawiy Allah ya jikan sa yana cewa:* وأما الخروج عليهم وقتالهم فحرام بإجماع المسلمين وإن كانوا فسقة ظالمين، وقد تظاهرت الأحاديث بمعنى ما ذكرته، وأجمع أهل السنة أنه لا ينعزل السلطان بالفسق [شرح مسلم ٢٢٩/١٢]. Amma fito na fito garesu da yakar su haramun ne da ijma'in musulmai, ko da sun kasance fasikai ne azzalumai, kuma tabbas hadisai sun bayyana ma'anar abinda na ambata shi, kuma Ahlus- Sunnah sunyi ijma'i akan cewa ba'a tunbuke shugaba saboda fasikan cin sa. [Sharhin Muslim 12/229]. *Al- Imamu Ahmad Bin Hanbal Allah ya jikansa yana cewa:* ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه لأحد من النَّاس، فمن فعل ذلك فهو مبتدع على غير السّنة والطريق. [أصول السنة ص ٤٦]. Kuma bai halasta a yaki shugaba ba, haka kuma bai halasta ayi fito na fito garesa ba, ga wani daga cik...

KUNGIYOYIN TA'ADDANCI NA IKHWAN

صورة
 DUKKANIN MASU KIRA ZUWA GA SUNNAH A WANNAN ZAMANI SUN HADU KAN FALLASA KUNGIYAR TA'ADDANCI TA IKHWAN(¹) Kasar musulunci ta Saudi Arabia (Allah ya kiyaye ta) ta tsayu haikan wajen bayyana halayen karkatattun kungiyoyi musamman ma #Kungiyar_Sururiyyah wacce take daya daga cikin 'ya'yan tagwaye uku(²) na kyankyasar kungiyar Ikhwan din (kasancewar ita Sururiyyah din ma'abotan ta sun fi yin kamanceceniya da Salafawa amma kuma ba Salafawa bane, 'yan bid'ah ne na yankan shakku). Muna fatan Allah ya datar da Malaman da suke wannan bayani, kuma yasa wannan tsoratarwa ta amfanar da bayin Allah, muma a nan gida Nigeria da shauran yankunan musulmai Allah ya kiyaye garuruwan mu daga afkawa cikin fikirorin kungiyoyin ta'addanci masu suturce barnar su da sunan addini ko kishin Islama.  MALAMAI SUN DAUKE MANA ALHAKIN BID'ANTAR DA KUNGIYAR IKHWAN!  Wannan kungiya ta Ikhwan duk da bayyana wani sashe na Sunnah da dai-daikun su suke yi, amma hakan bai tseratar da ita daga ...

MADAKHILAH?!

صورة
 *SO DA DAMA MAI DA'AWAR NEMAN GASKIYA DA ADALCI YANA AUKAWA CIKIN TAFARKIN AZZALUMAI BA TARE DA YA SANI BA!* So tari zakaga mutane masu son addini da adalci ga bayin Allah, sai suyi rashin dace sai su auka tarkon mabarnata fasikai basu sani ba, yana da kyau ya kai mai amfani da Facebook, ko mai neman gaskiya, ya kasance da gaske gaskiyar kake nema, ba yawan mabiya ko masu yin muwafaka da ra'ayin ka kake nema ba, ya kasance gaskiya ce abar neman ka, kuma da gaske, ka saki ta'assubanci, domin duk mai son ya zama "Salafi" (ma'abocin Sunnah na gaskiya) to sai ya yakice rigar ta'assubanci ya wurga wa shedan kayan sa, domin ta'assubanci ba tufafin mumini bane, kuma wuyan rigar gaskiya da adalci tayi kunci ga fasikai masu bada kariya ga 'yan Bid'ah da son zuciya. Idan ka gane wannan, zaka ga marubuta da yawa masu da'awar su ma'abota Sunnah ne, wani ma zakaji yana cewa shi mabiyin Tafarkin Salaf ne, zaka dinga cin karo da maganganun Ibnu Taimi...
صورة
 DAGA CIKIN MATSALOLIN HOTO: A shar'ance: Manzon Allah (Sallallahu 'alayhi wasallam) yana cewa:  "أشد الناس عذابا يوم القيامة المصورون، يقال لهم: أحيوا ما خلقتم" "Lallai mafi shan azaba a cikin mutane ran kiyama sune masu yin hoto, za'a ce dasu ku sanya rai ga ababen da kuka halitta" (Al- Albani ya inganta shi a cikin Saheehu al- Jaami' 999). A duniyance:  'yan kidnapping suna tara hotunan mutane suna bin su daya bayan daya suna tafiya dasu, musamman wa'yanda suke daukar hotunan su a wajajen cinikayyar su ko ofis din su ko wurin bukukuwan su, daga bisani su dora a kafafen sadarwa, ku sani ana muku ruwan comments kuma kuna burge ire-iren ku, amma kuma kuna bude ma kawunan ku kofofin matsaloli kala-kala na daya wanda shi ne yafi hatsari : shiga mafi matsananciyar azabar Allah, na biyu kuma wanda tun a duniya ne: akwai: 1) illar idanun masu hassada da 'ainu, akwai wani idan har yaga abu mai kyau ko yaga mutum mai kyau idan har ya yaba sai ba...
  SAKAMAKON AYYUKAN DA MUTANE KE AIKATAWA!  بسم الله الرحمن الرحيم، والصلاة والسلام على رسول الله، وعلى آله وصحبه ومن والاه.  أما بعد..  Ya ku al-ummah musulmai, kuji tsoron Allah ku mayar da lamurran ku gare shi, wannan masifar da aka shiga mafi girman sababin ta shi ne juya ma tafarkin Allah baya, Allah ne ya saukar kuma shi ne zai dauke, amma in kuka ce shuwagabanni ne suka saukar ba zaku taba ganin dai-dai ba, domin kunyi wa Allah tarayya a cikin ayyukan sa. A na samun masu shirka ga Allah kuma babu zalunci da ya kai shirka, ana samun masu bid'o'i kala-kala, ana samun masu sabo kala-kala, cin riba ba komai bane, kade-kade ba komai bane, yanzu ma ta kai ga cewa masu sabo sune suke cikin walwala, masu ayyukan da'a sune suke taka tsan tsan, lallai an zalunci kai, kuma sakamakon duk wa'yanda halin su ya zama haka.  Allah madaukaki yana cewa: (وكذلك نولي بعض الظامين بعضا بما كانوا يكسبوت) [الأنعام: 129]. " Kuma kamar haka ne muke dora sashen azzalumai a kan sashe...